Kayode Olofin-Moyin
Kayode Olofin-Moyin | |||
---|---|---|---|
ga Augusta, 1998 - 29 Mayu 1999 ← Sam Ewang (en) - Olusegun Osoba → | |||
Rayuwa | |||
ƙasa | Najeriya | ||
Harshen uwa | Yarbanci | ||
Karatu | |||
Makaranta |
Jami'ar Tsaron Nijeriya National Defence College, Nigeria (en) | ||
Harsuna |
Turanci Yarbanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa da soja |
Kayode Olofin-Moyin (an haife shi ranar 13 ga watan Mayu, 1950) a jihar Ekiti. Tsohon jami'in soja ruwa ne.
Rayuwar farko
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Kyaftin Navy Kayode Olofin-moyin a Ilawe-Ekiti, Jihar Ekiti, a ranar 13 ga Mayu, 1950.[1]
Karatu
[gyara sashe | gyara masomin]Bayan kammala karatunsa na firamare, ya shiga makarantar Annunciation Catholic School, Ikere-Ekiti a shekarar 1965. Ya kammala a shekarar 1969 tare da kyakykyawar takardar shedar west african examinations council (WAEC).
Ya samu gurbin shiga makarantar horas da sojoji ta Najeriya a shekarar 1971 a matsayin dalibi kuma ya samu nasarar kammala kwas dinsa a watan Disamba 1972 sannan ya samu aikin sojan ruwan Najeriya. Bayan haka, ya ci gaba da samun ƙarin horo. ya bar Makarantar Sojoji ta Najeriya a watan Disamba 1972, lokacin da ya fara kwas a Midshipman a cikin jirgin NNS OBUMA (Tsohon NNS NIGERIA). Ya kammala horonsa a watan Oktoba 1973 [2]
Aikin soja
[gyara sashe | gyara masomin]Kyaftin Navy Olofin-Moyin ya wuce babbar kwalejin Command and Staff College, Jaji a 1985, ya kammala a 1986. Daga nan ya halarci Kwalejin Yaki ta Kasa da ke Abuja tsakanin 1997 zuwa 1998.
Kyaftin navy Olofin-Moyin yafara ne a hankali. Daga Cadet a 1972, an ba shi matsayi na Midshipman a 1973; Karamin Laftanar (1973 – 1977); Laftanar (1977 - 1981); Laftanar Kwamanda (1981 - 1988); Kwamanda (1988 - 1994) da Kyaftin Navy (1994)
Wasu daga cikin Naɗin nasa sun hada da,
Commanding Officer, NNS HADEJIA (Patrol Boat), (1978 – 1979); Commanding Officer, NNS RUWAN YARO (Cadets Training Ship), (1984 – 1985); Commanding Officer, NNS ENYIMIRI (A Corvette on ECOMOG Operation), Liberia, (1992 – 1993) and Commanding Officer, Naval Air Station, (1996 – 1997).[3]
Kyaftin Navy Olofin-Moyin ya kuma gudanar da nadin ma'aikata kamar Jami'in Ma'aikata (Aiki), Rundunar Sojojin Ruwa ta Yamma (1986 - 1988); Base Commander, Nigerian Naval College, Onura, Port Hacourt (1990 – 1992); Babban Hafsan Sojan Ruwa, ECOMOG, Laberiya (1994 – 1995) da Daraktan Ayyuka, Hedikwatar Sojojin Ruwa, Legas (1995 – 1996).
Gwamnan Jihar Ogun
[gyara sashe | gyara masomin]An naɗa Kayode Olofin-Moyin a matsayin shugaban mulkin soja a jihar Ogun ta Najeriya daga watan Agusta 1998 zuwa Mayu 1999 a lokacin mulkin Janar Abdulsalami Abubakar na rikon kwarya, inda ya mika mulki ga zababben gwamna Olusegun Osoba a farkon jamhuriya ta hudu ta Najeriya. Ya gina sabon masaukin gwamna a jihar Ogun, wanda aka bude ranar 27 ga Afrilu 1999 kafin mikawa gwamnan farar hula.
A watan Nuwamba 2002 gidansa da ke Victoria Island, Legas ya yi gobara.[4]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://military-history.fandom.com/wiki/Kayode_Olofin-Moyin
- ↑ https://guardian.ng/news/skewed-security-formation-responsible-for-herders-killings-says-olofin-moyin/
- ↑ https://www.wikiwand.com/en/Kayode_Olofin-Moyin
- ↑ https://archive.ogunstate.gov.ng/ogun-state/governors/kayode-olofin/ Archived 2022-08-08 at the Wayback Machine