Jump to content

Lakurawa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Lakurawa
Bayanai
Iri irregular military (en) Fassara da ƙungiyar ta'addanci
Ƙasa Najeriya
Tarihi
Ƙirƙira 2024

Lakurawa ƙungiya ce ta ta'addanci da ke da alaƙa da ƙungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi da ke aiki a yankin Sahel, sun fito daga Mali da Jamhuriyar Nijar. Sun fara kutsawa cikin Arewacin Najeriya, musamman a jihohin Sokoto da Kebbi. Ayyukansu sun ta’allaƙa ne a ƙananan hukumomi biyar na Jihar Sakkwato, wato: Tangaza, Gudu, Illela, Binji, da Silame.[1][2]

Lakurawa sun fara bayyana ne a dajin Gongono, ƙaramar hukumar Tangaza ta jihar Sokoto, a shekarar 2018.[3] amma a cewar wasu majiyoyi, Lakurawa sun bayyana tun a wajajen shekarar 2016/2017, kuma gwamnati ta san da bayyanar su.[4] Ƙungiyar ta'addanci ta Lakurawa daga Nijar da Mali na da alaƙa da ISIS a cewar shelkwatar tsaron Najeriya.[5] Suna tilasta biyan zakkah, suna ƙwace shanu daga waɗanda ba su bada Zakka ba. Ayyukan su kusan irin na Boko Haram, suna magana da yurukan Azbinanci, Zabarmanci, Barbanci, da Hausa. Lakurawa na bawa matasa ₦1,000,000 don su shiga cikin ƙungiyar su.[6]

Lakurawa daga farko sunyi ikirarin kare jama'a daga harin ƴan fashi da masu garkuwa da mutane, amma kuma sai suka sanya tsauraran dokokin addini, waɗanda suka wuce gona da iri.[7] Wanda ya kai har suna yiwa matasa dukan tsiya saboda sun aske gemu, ko kuma sunyi askin banza, ko idan mutum yana sauraron waƙa, wanda wannan ba ƙaramin abin tashin hankali bane ga al'ummar yankin. Sun fara kai harin ta'addanci na farko a ƙauyen Mera da ke a ƙaramar hukumar Augie jihar Kebbi inda suka kashe mutane 25 amma kamar yadda kafafen yaɗa labarai suka bayyana sun kashe mutane 15.[8]

  1. "Su wane ne Lakurawa masu iƙirarin jihadi da ke barazana ga tsaron jihar Sokoto?". bbc.hausa.com. 6 November 2024. Retrieved 10 November 2024.
  2. Yusuf, Ibrahim (6 November 2024). "Sabuwar Kungiyar Yan Ta'adda na Raba Miliyoyi Domin Rudar Matasan Arewa". hausa.legit.ng. Retrieved 10 November 2024.
  3. "Revealed: How herdsmen invited new terrorist group, Lakurawa, to Sokoto". vanguard.com. 10 November 2024. Retrieved 10 November 2024.
  4. Egobiambu, Emmanuel (11 November 2024). "Lakurawa Not A New Terror Group — ACF, Bukarti". channelstv.com. Retrieved 12 November 2024.
  5. Sunday, Odita (7 November 2024). "New terrorist group `Lakurawa` affiliated to ISIS -DHQ". guardian.ng. Retrieved 10 November 2024.
  6. Are, Jesupemi (9 November 2024). "Report: Lakurawa luring Sokoto youths with financial incentives". thecable.ng. Retrieved 10 November 2024.
  7. Isamotu, Idowu (November 2024). "How Lakurawa members are terrorising us – Sokoto residents". dailytrust.com. Retrieved 10 November 2024.
  8. Sabiu, Muhammad (9 November 2024). "15 killed as Kebbi community fights off Lakurawa terrorist attack". tribuneonlineng.com. Retrieved 10 November 2024.