Malcolm X
![]() | |
---|---|
![]() | |
Rayuwa | |
Cikakken suna | Malcolm Little |
Haihuwa |
Omaha (en) ![]() |
ƙasa | Tarayyar Amurka |
Ƙabila | Afirnawan Amirka |
Harshen uwa | Turanci |
Mutuwa |
Manhattan (en) ![]() |
Makwanci |
Ferncliff Cemetery (en) ![]() |
Yanayin mutuwa |
kisan kai (ballistic trauma (en) ![]() |
Ƴan uwa | |
Mahaifi | Earl Little |
Mahaifiya | Louise Little (activist) |
Abokiyar zama |
Betty Shabazz (en) ![]() |
Yara |
view
|
Ahali |
Reginald Little (en) ![]() ![]() |
Karatu | |
Harsuna | Turanci |
Sana'a | |
Sana'a |
ɗan siyasa, autobiographer (en) ![]() ![]() ![]() |
Mahalarcin
| |
Kyaututtuka |
gani
|
Sunan mahaifi | Malachi Shabazz |
Imani | |
Addini |
Musulunci Ƙasar Islama Mabiya Sunnah |
IMDb | nm0944318 |
![]() |
Malcolm X ko el-Hajj Malik el-Shabazz (الحاجّ مالك الشباز) ya canja suna bayan ya musulunta. Yarayu daga shekara ta 1925 zuwa 1965 ya kasance ba Amurike dan'asali Afirka, wanda ya Musulunta, kuma mai rajin kare hakkin dan'Adam. An bayyana shi a matsayin wani wanda baida tsoro wurin karewa da nemawa yan'asalin Afirka mazauna Amurka hakkinsu, mutum ne daya kalubalance farar fata a kasar Amurka da tsauraren kalamai akan cutarwar da sukewa bakar fata. Ana ganinsa daya daga cikin manyan yan'Afirka mazauna Amurka dasuka kasance masu ilimi wurin zance da janhankalin al'umma a tarihi.
Farkon rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]
An haife shi Malcolm Little a watan 19 Mayu a shekara ta 1925 a garin Omaha, Nebraska, dake kasar Amurka, yarasu a watan Febreru 21, shekara ta 1965 (shekaru 39) a garin Manhattan, jihar New York, U.S. Sanadiyar mutuwa Harbi da bindiga Makwancinsa Makabartan Ferncliff
Sunayensa el-Hajj Malik el-Shabazz (الحاجّ مالك الشباز)
Ayyuka[gyara sashe | gyara masomin]
Shugaba, Mai rajin hakkin dan'Adam, Ya Samar da Kungiyar Muslim Mosque, Inc., Organization of Afro-American Unity Movement Black nationalism, da kungiyar Pan-Africanism
Matarsa itace Betty Shabazz sunyi aure a shekara ta 1958.
Ya'ya[gyara sashe | gyara masomin]
- Attallah Shabazz
- Qubilah Shabazz
- Ilyasah Shabazz
- Gamilah Lumumba Shabazz
- Malikah Shabazz
- Malaak Shabazz
Mahaifinsa Earl Little da mahaifiyarsa Louise Helen Norton Little
Karshen rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]
An kashe mahaifinsa a lokacin yana da shekara shida (6) da haihuwa, sannan mahaifiyarsa an sanyata a asibitin jinyan kwakwalwa yayin yanada shekara sha'uku, Sannan ne yayi rayuwa a gidajen rainon yara, a shekara ta 1946, shekaru 20, ankaisa gidan yari akan dauke-dauke ananne yasamu haduwa da kungiyar Nation of Islam (NOI), ya chanja sunansa daga Malcolm Little to Malcolm X saboda cewarsa, Little sunane na farar fata wanda suka sanya wa iyayensa shiyasa bazai yi amfani da sunan ba. Bayan ya fita daga fursuna a shekara ta 1952, yazamanto shugaba a kungiyar Nation of Islam, kuma shahararren mai jawabin kungiyar.
A shekarar 1964, Malcolm X yasamu matsala da Nation of Islam musamman shugabanta a Elijah Muhammad. Inda ya bayyana danasanin zamansa a kungiyar ya koma bin asalin addinin musulunci mai bin Sunnah Islam. Bayan tafiye tafiyensa zuwa kasashen Afirka da zuwarsa Hajji sai ya dawo da amfani da sunansa na musulunci el-Hajj Malik el-Shabazz. Ya tabbatar da rashin goyon bayansa akan wariya ko wata iri ce, sannan ya samar da kungiyar Muslim Mosque, Inc. da kungiyar Organization of Afro-American Unity (kungiyar hadinkan Yan'Afirka). Ya cigaba da tabbatar da rajin yan'Afirka, yancin bakar fata, samun mutuncin kan bakar fata da kariyarsa.
A watan Febreru 21, 1965 aka kashe Malcolm yayin dayake gabatar da jawabi a dakin taro na Ballroom dake jihar New York, yan kungiyar Nation of Islam ne uku aka kama da zargin kisan wadanda daga baya suka tuba, kuma suka bar kungiyar suka koma sunni Islam.