Jump to content

Mohammed Jega

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mohammed Jega
governor (en) Fassara

ga Maris, 1976 - ga Yuli, 1978
Rayuwa
Cikakken suna Mohammed Jega
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a soja
Digiri Janar
Manjo Janar

Manjo Janar Mohammed Jega ya kasance gwamnan soja a jihar Gongola ta Najeriya tsakanin watan Maris na shekara ta 1976 zuwa Yulin shekara ta 1978 a lokacin mulkin soja na Janar Olusegun Obasanjo, da kuma tsakanin watan Janairu na shekarar 1984 zuwa na Agustan 1985 a lokacin mulkin soja na Janar Muhammadu Buhari.[1]

Jega ya riƙe muƙamin kwamandan birgediya na 6 na shiyya ta biyu, Onitsha, da kuma babban kwamandan runduna ta biyu na mechanized na sojojin Najeriya, Ibadan.[2][3] A wa'adinsa na biyu a matsayin gwamna, ya rufe galibin makarantun da gwamnatin farar hula ta gwamna Abubakar Barde ta kafa saboda ƙarancin ƙasafin kudi.[4]

Bayan ya yi ritaya, Jega ya taka rawa sosai a zaɓen sarauta a cikin 1980s.[5] A ranar 5 ga watan Yuni, 2005 aka naɗa Jega Sarkin Gwandu[6][7] a Jihar Kebbi, ya maye gurbin Alhaji Mustapha Jokolo.[8]

  1. "Nigerian States". WorldStatesmen. Retrieved 2 April 2010.
  2. Bayo Ohu (12 January 2004). "Dikko in Ogun, condemns money politics". The Guardian. Archived from the original on 9 February 2013. Retrieved 2 April 2010.
  3. Oke Epia (6 May 2005). "Mohammed Jega Now Emir of Gwandu". ThisDay. Archived from the original on 16 November 2005. Retrieved 2 April 2010.
  4. Rima Shawulu (15 June 2008). "Governor Mohammed and History". Rima Shawulu. Retrieved 2 April 2010.
  5. Olufemi Vaughan (2006). Nigerian Chiefs: Traditional Power in Modern Politics, 1890s-1990s. The International Journal of African Historical Studies. 33. University Rochester Press. pp. 672–674. doi:10.2307/3097441. ISBN 978-1-58046-249-5. JSTOR 3097441.
  6. Dalhatu, Usman (2016). Major-General Muhammadu Iliyasu Bashar, CFR, Mni (M.D. Jega): The 20th Emir of Gwandu (in Turanci). Woodpecker Communication Services. ISBN 978-978-083-075-5.
  7. "Emir of Gwandu declares support for basic education in Kebbi". The Sun Nigeria (in Turanci). 2020-03-04. Retrieved 2020-10-06.
  8. Mohammed Kabir (6 June 2005). "Jega Replaces Jokolo As Emir of Gwandu". Daily Champion. Retrieved 2 April 2010.