Mudashiru Obasa
Mudashiru Obasa | |||
---|---|---|---|
11 ga Yuni, 2019 - 11 ga Yuni, 2023 District: Agege I (en) | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Agege, 11 Nuwamba, 1972 (52 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Mazauni | Lagos, | ||
Harshen uwa | Yarbanci | ||
Karatu | |||
Makaranta | Jami'ar, Jihar Lagos | ||
Harsuna | Turanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa da Lauya | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | All Progressives Congress |
Mudashiru Ajayi Obasa (an haife shi 11 ga watan Nuwamban 1972) lauya ne a Najeriya kuma ɗan siyasa wanda ya yi aiki a matsayin kakakin majalisar dokokin jihar Legas tun shekarar 2015.[1]
Ɗan jam'iyyar All Progressives Congress ne wadda ke mulki.
Rayuwar farko
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Mudashiru Ajayi Obasa a Agege, wani gari dake jihar Legas kudu maso yammacin Najeriya a ranar 11 ga watan Nuwamban 1972.[2] Ya yi karatun firamare a St Thomas Acquinas Pry School, Surulere, Legas kafin ya wuce Archbishop Aggey Memorial Secondary School, Mushin, Ilasamaja, Legas inda ya samu takardar shedar makarantar West Africa.[3] Ya sami digiri na farko a fannin shari'a a Jami'ar Jihar Legas dake Legas a shekarar 2006.[4]
Sana'ar siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]A shekarar 1999 ya tsaya takarar kansila a ƙaramar hukumar Agege a ƙarƙashin jam’iyyar Alliance for Democracy kuma ya yi nasara. Ya yi aiki tsakanin 1999 zuwa 2002.[5]
An zaɓe shi ɗan majalisar dokokin jihar Legas mai wakiltar mazaɓar Agege I a shekarar 2007. An sake zaɓen shi a 2011, 2015 da 2019.[6][7]
A cikin shirin na #EndSARS a jiharsa, an yi masa wani bidiyo kai tsaye a gidan talabijin yana cewa " LSHA ba za ta amince da mutuwar ƴan ta'adda a hannun rundunar ƴan sanda ba" a lokacin da yake kira da a yi shiru na minti ɗaya aya ga waɗanda rikicin #Lekki ya shafa. da sauran su a faɗin Najeriya.[8]
Cin hanci da rashawa
[gyara sashe | gyara masomin]A shekarar 2020 ne dai jaridar Sahara Reporters ta ruwaito ta fitar da rahoton zargin almubazzaranci da dukiyar al’umma da ake yi masa. Sai dai ya musanta dukkan zarge-zargen.[9][10][11][12]
Daga baya Sahara Reporters ta ruwaito cewa hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa ta kai Obasa domin yi masa tambayoyi a ranakun 8 da 9 ga Oktoban 2020. A cewar wata majiya mai tushe ta tabbatarwa da Sahara Reporters cewa Obasa ya nuna rashin lafiya ne a lokacin da ake yi masa tambayoyi a ofishin EFCC, wanda ya sa aka dakatar da tambayoyi. Sai da aka kai Obasa zuwa majinyata na ofishin EFCC kafin a bayar da belinsa.[13] Daga nan Obasa ya nemi a dawo masa da fasfo ɗinsa, wai don neman magani a ƙasashen waje kafin ya tafi Umrah don ganawa da Bola Tinubu a Saudiyya. EFCC na ci gaba da binciken Obasa bisa zargin almundahana da zamba.[14]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://thenewsnigeria.com.ng/2015/06/23/meet-obasa-the-new-lagos-speaker/
- ↑ https://www.legit.ng/456274-the-rise-and-rise-of-the-new-lagos-speaker.html
- ↑ http://encomium.ng/why-i-want-to-come-back-to-house-for-the-fourth-time-hon-mudashiru-obasa/
- ↑ https://www.legit.ng/456274-the-rise-and-rise-of-the-new-lagos-speaker.html
- ↑ http://encomium.ng/profiles-of-the-new-principal-officers-of-lagos-house-of-assembly/
- ↑ https://punchng.com/breaking-lagos-speaker-obasa-other-win-lagos-house-of-assembly-seats-in-agege/
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-03-16. Retrieved 2023-03-16.
- ↑ https://allnews.ng/news/endsars-we-won-t-honour-miscreants-killed-by-the-police-lagos-speaker-video
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-03-16. Retrieved 2023-03-16.
- ↑ https://saharareporters.com/2020/05/15/exclusive-lagos-assembly-speaker-obasa-approves-n258m-printing-invitation-cards-house
- ↑ https://saharareporters.com/2020/05/04/exclusive-how-obasa%E2%80%99s-wife-receives-n10m-illegal-monthly-allocation-lagos-assembly
- ↑ https://guardian.ng/tag/mudashiru-obasa/
- ↑ https://saharareporters.com/2020/10/10/exclusive-lagos-assembly-speaker-obasa-returns-efcc-interrogation-feigns-sickness
- ↑ https://saharareporters.com/2021/05/11/lagos-speaker-obasa-under-efcc-probe-sighted-mecca-after-lying-he-was-sick-needed-his