Jump to content

Sallar Gani

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Infotaula d'esdevenimentSallar Gani
Iri biki
Wuri Arewacin Najeriya, Masarautar Borno, Masarautar Daura, Gumel Emirate (en) Fassara da Hadejia
Ƙasa Najeriya
Sallah

Bikin Gani ko Sallar Gani biki ne na in gargajiye na shekara-shekara da akasarin masarautuɗhudu ke yi a Arewacin Najeriyaɗ waɗanda sukaɗ haɗa da Masarautar Borno, Masarautar Hadejia, Masarautar Daura, da Masarautar Gumel.[1][2] Ana gudanar da wannan biki kamar yadda ake gudanar da bikin Durbar na Eid al-Fitr da Eid al-Adha .[ana buƙatar hujja]</link>Ana gudana ranar 12 ga watan Rabi'ul Awwal na kowace shekara domin tunawa da kuma haihuwar Annabi Muhammad . Sarki tare da majalisarsa suka hau dawakai da aka yi wa ado da kayan ado a kewayen birnin. Jama’ar unguwar kuma su kan yi ado na musamman a wannan rana tare da yin abinci na musamman don rabawa ga ‘yan uwa da abokƴaarziki. Ana yin kade-kaden gargajiɗa naɗHausa, wakokin yabon ManzƙoƙAllah, da raye-raye a yayin bikin. Bayan Durba, sarki ya koma fada inda zai tattauna da majalisar ministocinsa kan batutuwan da suka shafi al'umma. Bikin ya ja hankalin masu yawon bude ido saboda yaɗa nuna al'adun Hausawa, Arewacin Najeriya da Afirka.[3][4][5]

  1. Webmaster (2017-12-12). "Sallar Gani: Daura's biggest festival". Daily Trust (in Turanci). Retrieved 2022-12-16.
  2. "Ko kun san asalin bikin hawan sallar gani?". BBC News Hausa. Retrieved 2022-12-16.
  3. "Gani Durbar Festival Jigawa State :: Nigeria Information & Guide". www.nigeriagalleria.com. Retrieved 2022-12-16.
  4. "Festivals & Games | Katsina State Government" (in Turanci). Archived from the original on 2022-12-16. Retrieved 2022-12-16.
  5. Webmaster (2017-12-12). "Sallar Gani: Daura's biggest festival". Daily Trust (in Turanci). Retrieved 2022-12-16.