Samira Saleh Ali al-Naimi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Samira Saleh Ali al-Naimi
Rayuwa
Haihuwa 1963
ƙasa Irak
Mutuwa Mosul (en) Fassara, 22 Satumba 2014
Sana'a
Sana'a Mai kare ƴancin ɗan'adam da Lauya
Masallacin Yunis da ke Mosul, wanda kungiyar IS ta lalata a ranar 24 ga watan Yuli,na shekarar 2014.

Samira Salih al-Nuaimi (kuma Samira Saleh Ali al-Naimi, Sameera Salih Ali al-Nuaimy, ko سميرة صالح النعيمي a Larabci) an haifeta a ranar ashirin da biyu 22 ga watan satumba shekara ta aluf (1963 - 22 Satumba 2014) lauya ce ta Iraqi kuma mai fafutukar kare hakkin bil'adama .

Ta yi suka a shafin Twitter saboda sun lalata masallatai da coci -coci da wuraren ibada . [1] Sai wasu maza da ke rufe fuska suka sace ta. An azabtar da ita na tsawon kwanaki biyar sannan kuma kungiyar IS ( ISIS ko Daish ) ta kashe ta.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kakkausar suka kan kisan.

Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Samiraa al-Nuaimi lauya ce. A cewar Cibiyar Kare Hakkokin Bil Adama ta Gulf, ta yi aiki kan yancin fursunonin da talauci . Ta yi aiki a matsayin mai aikin sa kai don yancin mata . Ta kasance daya daga cikin manyan masu fafutuka a kasar ta Iraki, musamman wajen kare kare hakkin mutanen da ke gidan yari, da kuma taimaka wa iyalai da kudi kadan. [2]

Samira ta zauna a yankin arewa maso gabashin Mosul tare da mijinta da 'ya'yanta uku. A ranar sha bakwai 17 ga watan Satumba, na shekara ta 2014, lokacin da take gida tare da mijinta da 'ya'yanta, kungiyar ISIL ta dauki Samira daga gidanta. Sun ce tana da laifin yin ridda a karkashin shari'ar Musulunci . Sun azabtar da ita har tsawon kwanaki buyar 5. Sai suka kashe ta. Zeid Ra'ad al-Hussein, kwamishinan kare hakkin bil'adama na Majalisar Dinkin Duniya, ya ce ba a ba iyalanta izinin yi mata jana'iza ba. [3]

Tawagar Majalisar Dinkin Duniya a kasar Iraki ta ce an kama ta ne saboda sakonnin da ta yi a Facebook . Ta buga suka kan yadda ISIL ke lalata wuraren ibada a Mosul. Bayan rasuwarta, an cire shafin Facebook.

Halin kasa da kasa[gyara sashe | gyara masomin]

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta yi Allah wadai da kisan Samira. Sun ce ta kasance jarumtaka domin tana taimakon mutane lokacin da take cikin hadari.

Wakilin musamman na Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya a Iraki (SRSG), Mista Nickolay Mladenov, ya kuma yi kakkausar suka kan kisan al-Nuaimi. Ya ce wannan "laifi ne mai cutarwa da aka aikata kan mutanen Iraki". Kwamishinan Majalisar Dinkin Duniya, Prince Zeid bin Raad, daga ofishin babban kwamishina a Geneva da New York, ya ce mutuwar Samira ta yi muni. Ya ce tana da karfin gwiwa domin ta kare hakkin wasu.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]