Usman Alkali Baba

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Usman Alkali Baba
Rayuwa
Haihuwa 1 ga Maris, 1963 (61 shekaru)
Sana'a

Alkali Baba Usman (an haife shi a ranar 1 ga watan Maris a shekara ta 1963), shi ne babban sufeto-janar na ƴan sandan Najeriya a halin yanzu, kuma shi ne shugaban hukumar ƴan sanda na( 21) a Hukumar ƴan sanda ta Najeriya. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne ya naɗa shi bayan cikar wa'adin Muhammad Adamu wanda ya yi ritaya daga aikin ƴan sanda a cikin watan Fabrairun shekara ta( 2021). Majalisar ƙolin ƴan sanda a ranar Juma’a ( 4) ga watan Yuni na shekara ta (2021) ta tabbatar da naɗin Alkali Usman Baba a matsayin babban sufeton ƴan sandan Najeriya.[1]


Rayuwar farko[gyara sashe | gyara masomin]

Alkali ɗan asalin garin Gaidam ne, Jihar Yobe, Najeriya. A shekara ta ( 1980) ya samu takardar shedar kammala karatunsa na kwaleji na biyu a kwalejin malamai da ke Potiskum a jihar Yobe. Inda daga baya kuma ya karanci kimiyyar siyasa a Jami'ar Bayero Kano (Political science), inda ya kammala a shekara ta (1985) ya kuma samu digiri ta( 2) a Jami'ar Maiduguri inda ya karanta fannin harkokin gwamnati (Public Administration) a shekara ta (1997) Baba ya kasance memba na kwas ɗin (22/2014 2014) a kwalejin tsaro ta ƙasa (National Defence College).[2][3]

Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Alkali ya shiga aikin ƴan sandan Najeriya a ranar( 15) ga watan Maris shekara ta (1988) sannan ya zama mataimakin sufeton ƴan sanda, kafin daga bisani ya samu ƙarin girma zuwa kwamishinan ƴan sanda a ranar( 2) ga watan Janairun shekara ta ( 201 3). A shekarrta ( 2014 ) aka tura shi jihar Delta a matsayin kwamishinan ƴan sanda.[4] Ya yi aiki a matsayin DIG, CID, sakataren rundunar a shelkwatar rundunar da ke Abuja. Ya yi aiki a FCT a matsayin mataimakin kwamishina, bincike da kuma kwalejin ma'aikata a matsayin jagoran ma'aikata. Ya kuma yi aiki a Kaduna a matsayin mataimakin kwamishinan gudanarwa da mataimakin kwamishinan CID. Ya yi aiki a Ilorin a matsayin kwamandan yanki, haka a jihar Ebonyi shi ne na biyu. Ya yi aiki a Kaduna, Yola, Jos da kuma jihar Gombe a matsayin DPO. Baba ya kasance tsohon mataimakin sufeto-janar na ƴan sanda shiyya ta 5 (Zone 5), mai kula da jihohin Edo, jihar Delta da kuma jihar Bayelsa. Baba mamba ne Kwalejin Yaki ta Duniya kuma mamba ne a Ƙungiyar ƴan Sanda ta ƙasa da ƙasa.[5][6][7]

Sufeto-Janar na ƴan sanda[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar (6) ga watan Afrilu a shekara ta ( 2021) Shugaba Muhammadu Buhari ya naɗa Baba don maye gurbin Mohammed Adamu wanda ya yi ritaya daga aikin ƴan sandan Najeriya a watan Fabrairun shekara ta (2021).[8] Har zuwa lokacin da aka naɗa shi a matsayin IG na ƴan sanda, ya kasance mataimakin sufeto-janar na ƴan sanda, sashen binciken laifuka na hed kwatar rundunar.[9][10][11]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Olumide, Johnson (6 April 2021). "Usman Alkali Baba Biography: 8 things you didn't know about new IGP" (in English). Creebhills.com. Retrieved 5 March 2022.CS1 maint: unrecognized language (link)
  2. Abiodun, Alao (6 April 2021). "8 things to know about new IGP Usman Alkali Baba". The Nation Newspaper. Retrieved 5 March 2022.
  3. "Buhari Approves Appointment Of Usman Alkali As Acting IGP". Channels TV. Channelstv.com. 6 April 2021. Retrieved 5 March 2022.
  4. Eribake, Akintayo (24 September 2014). "I've come to police Delta with human face — CP Alkali" (in English). Vanguard Newspaper. Retrieved 5 March 2022.CS1 maint: unrecognized language (link)
  5. "Facts on Acting DIG Usman Alkali, Just Appointed By Buhari". The News Nigeria.Com. 6 April 2021. Retrieved 5 March 2022.
  6. Nwafor, Polycarp (6 April 2021). "Who is Usman Alkali Baba, acting IGP?". Vanguard Newspaper. Retrieved 5 March 2022.
  7. "AIG Alkali resumes at police Zone 5". Blueprint Newspaper. 18 October 2018. Retrieved 5 March 2022.
  8. Egbas, Jude (6 April 2021). "Buhari names Usman Baba new IGP" (in English). Pulse NG. Retrieved 5 March 2022.CS1 maint: unrecognized language (link)
  9. Oludiran, Olusola (6 April 2021). "Police minister: Why ex-IGP Adamu didn't complete his three months tenure extension". The Cable.ng. Retrieved 5 March 2022.
  10. Ibrahim, Aminu (6 April 2021). "Usman Alkali Baba: Abubuwa 6 da ya kamata ku sani game da sabon Babban Sufetan 'Yan Sanda". legit.hausa.com. Retrieved 5 March 2022.
  11. Muideen Olaniyi, da Sagir Saleh Kano (7 April 2021). "Osinbajo Ya Daura Wa Usman Alkali Baba Sabon Mukaminsa". Aminiya daily trust.com. Retrieved 5 March 2022.