Zaɓen Gwamnan jihar Yobe na shekarar 2019
| |
Iri | gubernatorial election (en) |
---|---|
Kwanan watan | 9 ga Maris, 2019 |
Ƙasa | Najeriya |
Applies to jurisdiction (en) | Jihar Yobe |
Zaben gwamnan jihar Yobe na 2019 ya gudana a ranar 9 ga watan Maris na shekarar 2019, dan takarar APC Mai Mala Buni ne ya lashe zaben, inda ya kayar da Umar Iliya Damagum na PDP.
Mai Mala Buni ya zama dan takarar gwamna na APC bayan ya samu kuri’u 2,797 sannan ya kayar da babban abokin karawarsa, Honorabul Sidi Karasuwa wanda ya samu kuri’u 23. Inda ya zabi Alhaji Idi Barde Gubana a matsayin mataimakin sa. Umar Iliya Damagum shi ne dan takarar PDP tare da Baba Abba Aji a matsayin abokin mataimakin sa. ‘Yan takara 13 ne suka fafata a zaben.
Tsarin zabe
[gyara sashe | gyara masomin]An zabi Buni a matsayin Gwamnan jihar Yobe ta hanyar amfani da tsarin kada kuri'a .
Zaben Fidda Gwani
[gyara sashe | gyara masomin]Fidda gwanin APC
[gyara sashe | gyara masomin]Zaben fidda gwani na APC a karon farko, ya gudana ne a ranar 30 ga watan Satumba, 2018. Mai Mala Buni ya lashe zaben fidda gwanin inda ya samu kuri’u 2,797 inda ya kara kuma ya kayar da wasu ‘yan takara 3. Babban abokin hamayyarsa shi ne Sidi Karasuwa, wanda ya zo na biyu da kuri’u 23, Umar Ali ya zo na uku da kuri’u 8, yayin da Aji Kolo ya samu kuri’u 4.
'Yan takara
[gyara sashe | gyara masomin]- Dan takarar jam’iyya: Mai Mala Buni
- Mataimaki: Idi Barde Gubana
- Sidi Karasuwa
- Aji Kolo
Zaben fidda gwani na PDP
[gyara sashe | gyara masomin]An gudanar da zaben fitar da gwani na jam’iyyar PDP a ranar 30 ga watan Satumba, 2018. Umar Iliya Damagum ya fito ne a matsayin dan takarar hadin kai bayan da babban abokin hamayyarsa Umar Elgash Maina ya janye.
'Yan takara
[gyara sashe | gyara masomin]- Dan takarar jam’iyya: Umar Iliya Damagum
- Abokiyar takara: Baba Abba Aji
- Umar Elgash Maina- ya janye
Sakamako
[gyara sashe | gyara masomin]Kimanin ‘yan takara 13 ne suka yi rijista tare da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa don tsayawa takara a zaben.
Adadin wadanda suka yi rijista a jihar don jefa kuri'a ya kai 1,365,913, yayin da aka tantance 546,391. Adadin kuri'un da aka kada sun kasance 560,492, yayin da ingantattun kuri'u suka kasance 546,391. Kuri’un da aka ki amincewa da su kuwa yawansu ya kai 14,101.Samfuri:Election results
Ta karamar hukuma
[gyara sashe | gyara masomin]Ga sakamakon zaben da karamar hukumar ta yi wa manyan jam’iyyun biyu. Jimillar halastattun kididdigar kuri'u 546,391 da aka kada ga wakilan jam'iyyun siyasa 13 da suka tsaya takara. Shudi yana nuni da kananan hukumomi wadanda Mai Mala Buni ya ci. Kore yana nuni da kananan hukumomi wadanda Umar Iliya Damagum ya ci.
LGA | Mai Mala Buni
APC |
Umar Iliya Damagum
PDP |
Jimlar Kuri'u | ||
---|---|---|---|---|---|
# | % | # | % | # | |
Damaturu | 26,087 | 3,760 | |||
Geidam | 18,724 | 2,760 | |||
Nguru | 28,366 | 19,468 | |||
Bade | 32,213 | 8,854 | |||
Yunusari | 28,858 | 893 | |||
Karasuwa | 24,262 | 2,762 | |||
Yusufari | 22,221 | 2,964 | |||
Potiskum | 54,773 | 5,114 | |||
Fune | 36,040 | 14,327 | |||
Jakusko | 30,828 | 5,887 | |||
Bursari | 20,657 | 2,813 | |||
Gulani | 21,765 | 4,576 | |||
Fika | 36,519 | 9,552 | |||
Machina | 16,950 | 2,164 | |||
Nangere | 25,698 | 4,765 | |||
Tarmuwa | 11,338 | 3,925 | |||
Gujba | 17,714 | 1,119 | |||
Alsidaya | 444,013 | 95,703 | 546,391 |
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]