Jump to content

Abincin Hausawa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Abincin Hausawa
national cuisine (en) Fassara
Bayanai
Bangare na Abincin Najeriya da Abincin Nijar
tuwan shinkafa DA miya
Sinasir

Abincin Hausawa Su ne kayan sarrafa abinci na gargajiya dana zamani wadanda Hausawa ke shirya su, kuma sun ta'allaka ne a kan samuwar danyen kayan abinci wanda aka noma, ko samar da su daga wasu wurare, a mafi yawan lokuta Hausawa suna dogaro ne kacokan a kan kayan gonar da suka noma, wanda ake amfani da su don shirye-shiryen abinci. [1] Hausawa suna da abincin da ya saba wa yawancin al'ummomin Zongo da ake kira (Tuo Zaafi).[2]

Yadda ake gasa nama

Karin kumallo

[gyara sashe | gyara masomin]

Karin kumallo abinci ne da ake ci da safe, ana kiransa da suna kalaci ko abinci a wasu wuraren. Hausawa na daukar karin kumallo da matukar muhimmanci, kasancewar ana cin karin kumallo da sassafe. Hausawa suna cin abinci maras nauyi a matsayin karin kumallo, galibi ana shirya irin wadannan abincin ne a gida, amma wasu Hausawan suna sayen abincin kasuwa daga gidajen sayen abinci ko masu sayar da abinci a titi. Mafi yawan Hausawa na ci ko shan wadannan nau'in abincin a matsayin karin kumallo:

  • Koko da kosai : Wannan abincin galibi Hausawa kashi 70% ne ke amfani da shi a matsayin karin kumallo. Kosai wani abinci ne wanda ake yinsa daga ɗanyen wake, wanda aka yi shi cikin ƙullu, sannan kuma a soya shi a kaskon mai,[3][4] yayin da koko ya kasance wani tsohon abincin gargajiya na Hausa wanda ake yi da gero ko masara. Ana yin koko kamar haka: [5]
  1. Koko: Ana yin sa ne da gasara wadda ake samu daga nikakken gero.
  2. Kunun tsamiya: Ana yin sa ne daga gero, sa'annan ana jiƙa tsamiya a zuba a ciki don ya bayar da dandanon tsami.
  3. Kunun gyada: Ana yin sa ne daga niƙakƙiyar gyada, wasu suna sa garin fulawa da shinkafa a ciki.
  4. Kunun dawa: Ana yin sa ne da dawa.
  5. Kunun Alkama: ana yin kunun alkama daga alkama shi ma kunu ne, mai dan karen daɗi.
  6. Kunun acca: Ana yin sa ne daga acca.
  7. Kunun masara: Ana yin shi ne daga masara.
  8. Kunun aya: Wannan abin sha ne da aka yi daga aya "Tigernut". [6]
  9. Kunun kanwa: An yi daga gero amma ya sha bamban da kunun tsamiya.
  • Waina ko Masa:
  • Kofi (coffee) da Gurasa : a wannan zamani, Hausawa suna ɗaukar kofi da burodi a matsayin karin kumallo, ba ya cikin al'adunsu, amma an ɗauke shi ne sakamakon wayewar Turawan Ingila.

Abincin rana

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Dambu
  • Dan wake: ana yin Dan wake da ko dai wake zalla ko kuma da gauraye da dawa. Haka kuma, ana yinsa da wadansu abubuwan kamar gero da busashshen rogo ko kuma da Fulawa ko alkama. Ana cinsa da dakakken yaji da mai.
  • Dan Gauda
  • Taliya
  • Shinkafa
  • Alale
  • Gwaza/Makani
  • Dankali
  • Tuwon Bula
  • Hoce

Abincin dare

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Tuwo: tuwo ya kasu iri daban-daban daga wanda ake yi da garin masara da na gero ko masara. Yawanci ana cinsa da miya iri daban-daban. Yawanci an fi cinsa da miyar kuka. Miyar kuka ita ce miyar da ake yi da busasshen ganyen kuka "baobab", wanda aka nika ta ta zama gari., sai kuma miyar kubewa. Da ta taushe da sauransu.[7][8][9]
  • Shinkafa:
  • Funkaso :

Abin shan Hausawa

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Zobo
  • Kunun Zaki
  • Kunun Aya
  • Dinja

Kayan ciye-ciye

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Chin Chin
  • Alkaki
  • Alkubus
  • Dubulan
  • Dakuwa
  • Nakiya
  • Hikima
  • Adamu, Abdalla Uba, 1956-, Adamu, Yusuf Muhammad., Jibril, Umar Faruk. Hausa home videos : technology, economy and society. Kano, Nigeria: Center for Hausa Cultural Studies. 2004. ISBN 978-36906-0-4.OCLC 61158034.
  • Abubakar Aliyu Mohammed. Cultural Torism. ISBN:978-978-087-937-2
  1. Ibenegbu, George (2018-07-11). "Top 3 Hausa foods and how to prepare them". www.legit.ng (in Turanci). Retrieved 2020-05-11.
  2. https://www.muryarhausa24.com.ng/2019/10/karanta-jerin-abincin-hausawa-kafin-zuwan-yar-thailand-kafin-zuwan-shinkafa-yar-kasashen-waje-girke-girken-gargajiya-sunayen-abincin-gargajiya-abincin-zamani-filin-girke-girke-abincin-zamani-filin-girke-girke.html
  3. Lete, Nky Lily (2013-02-23). "Nigerian Akara Recipe: How to Make Akara". Nigerian Food TV (in Turanci). Retrieved 2020-05-11.
  4. "How to make Akara - African Bean Fritters recipe". Chef Lola's Kitchen (in Turanci). 2015-07-27. Retrieved 2020-05-11.
  5. "Try This Popular West African Street Food, Hausa Koko". The Spruce Eats (in Turanci). Retrieved 2020-05-10.
  6. "Recipe: How To Prepare Hausa Koko At Home". Modern Ghana (in Turanci). Retrieved 2020-05-10.
  7. Ibenegbu, George (2018-07-11). "Top 3 Hausa foods and how to prepare them". www.legit.ng (in Turanci). Retrieved 2020-05-11.
  8. "Miyan Kuka (Baobab Leaves Soup)". All Nigerian Recipes (in Turanci). Retrieved 2020-05-11.
  9. https://www.muryarhausa24.com.ng/2019/10/karanta-jerin-abincin-hausawa-kafin-zuwan-yar-thailand-kafin-zuwan-shinkafa-yar-kasashen-waje-girke-girken-gargajiya-sunayen-abincin-gargajiya-abincin-zamani-filin-girke-girke-abincin-zamani-filin-girke-girke.html