Jump to content

Amal Umar

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Amal Umar
Rayuwa
Karatu
Makaranta Yusuf Maitama Sule Un AUWALI SANI BENA (en) Fassara
Harsuna Hausa
Turanci
Sana'a
Sana'a jarumi da ɗan wasan kwaikwayo
hoton jaruma amal umar
Amal Umar
Amal Umar

Amal Umar (an haifeta a ranar 21 ga watan Octoba, shekarata 1998) a Jihar Katsina, a kasar Najeriya, ta kasance ƴar wasan kwaikwayo ce a masana'antar fim ta Kannywood. Ta kuma fito a cikin shirin turanci na Nollywood MTV Shuga Naija tare da sauran taurarin Hausa, kamarsu Rahama Sadau da Yakubu Muhammed.[1][2]

Kuruciya da Ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Amal, ranar 21 ga watan Oktoba a shekara ta 1998 a jihar Katsina, kasar Najeriya. Tayi karatun ta na firamare da sakandare a Katsina, sannan ta koma jihar Kano domin yin karatun gaba da sakandare a Jami’ar Yusuf Maitama Sule, Kano.

Amal Umar ta fara wasan kwaikwayo ne a shekara ta 2015, inda ta shiga masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood. Amma kafin ta fito a fim ta fara fitowa cikin bidiyon waƙoƙi tare da mawaƙa kamar Umar M Sherrif, Garzali Miko da sauransu. Ta fara fitowa a fim ɗin Hausa mai suna "Itikam" tun daga nan ta fara samun suna a faɗin ƙasar Hausa. Ayyukanta sun fara haskakawa bayan fitowarta ta farko a cikin jerin matasan Nollywood MTV Shuga.

  1. saharan1 (2021-12-13). "Amal Umar Biography Acting Career Awards Latest Pictures". S-News (in Turanci). Archived from the original on 2022-07-31. Retrieved 2022-07-31.
  2. "Shuga" MTV Shuga Naija - Ep 4 (TV Episode 2019) - IMDb (in Turanci), retrieved 2022-07-31