Bisi Komolafe

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Bisi Komolafe
Rayuwa
Cikakken suna Bisi Komolafe
Haihuwa Ibadan, 1986
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Yarbanci
Mutuwa 31 Disamba 2012
Yanayin mutuwa  (puerperal disorders (en) Fassara)
Karatu
Makaranta Jami'ar Jihar Lagos
Harsuna Turanci
Yarbanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Jarumi, darakta da mai tsara fim
IMDb nm3479888

Bisi Komolafe (1986-2012) 'yar wasan kwaikwayo ce a Nijeriya, mai bada umurni kuma mai daukan nauyin fina-finai wacce tayi fice a a kwaikwayo da tayi a fim din Igboro Ti Daru da Aramot.[1]

Kuruciya da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

Bisi ita ce 'ya ta biyu da iyayenta suka haifa a shekara ta 1986 a cikin iyalin mutum biyar a Ibadan, jihar Oyo Kudu-maso-yammacin Nijeriya inda ta kammala karatunta na firamare da sakandare.[2] Ta halarci makarantar St. Louis Grammar School, Ibadan kafin ta wuce zuwa Jami'ar Jihar Legas (LASU) inda ta kammala da digiri a fannin Kasuwanci (Bussiness Administration).[3][4]

Ayyuka[gyara sashe | gyara masomin]

Fitilar tauraruwar ta fara haskawa a yayin da ta fito a fim din Igboro Ti Daru . Ta ci gaba da taka rawa a matsayin tauraruwa acikin fina-finai da suka hada da Bolode O'ku, Asiri Owo da Ebute. Har wayau Bisi ta kuma shirya fina-finai da suka hada da Latonwa, Eja Tutu da Oka.[5] An gabatar da ita a rukunin kyautar "Revelation of the year" a gasan Best of Nollywood Award" na shekarata 2009 da kuma a cikin "Fitacciyar Jagoran fim Jaruma na fina-finan Yarbawa" a kyautar 2012 edition.[6]

Kyauta da gabatarwa[gyara sashe | gyara masomin]

Shekara Bikin lambar yabo Bayanin lambar yabo Sakamakon
2009 Kyautan Best of Nollywood na shekara ta 2009 Wahayin Shekara Ayyanawa[7]
2012 Kyauta Best of Nollywood na shekara ta 2009 ta 2012 Fitacciyar Jarumar Jaruma a fim din Yarbawa Ayyanawa[8]

Mutuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An bayar da rahoton rasuwar Bisi Komolafe a kafofin watsa labarai a ranar 31 ga Disamba 2012.[9] Yanayin da ke tattare da mutuwarta ya haifar da rahotanni da jita-jita da yawa a cikin kafofin watsa labarai. Sai dai rahotanni na likitanci sun tabbatar da cewa ta mutu ne sakamakon matsalolin haihuwa a Asibitin Kwalejin Jami'a, Ibadan.[10] [11]An binne ta a ranar 4 ga Janairun 2013[12] a garin Ibadan.

Filmography da aka zaba[gyara sashe | gyara masomin]

 • Igboro Ti Daru
 • Aye Ore Meji
 • Apere Ori
 • Omo Olomo Larin Ero
 • Jo Kin Jo
 • Akun
 • Bolode O'ku
 • Aramotu
 • Asiri Owo
 • Ogbe Inu
 • Aiyekooto
 • Latonwa
 • Alakada
 • Mofe Jayo
 • Ebute
 • Iberu Bojo

Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An mata baiko da wani dan asalin kasar Kanada dake zaune a Najeriya, Tunde Ijadunola a jihar Oyo.[13]

Duba kuma[gyara sashe | gyara masomin]

 • Jerin furodusoshin fim na Najeriya

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

 1. Aduwo, Bola (2009-12-07). "Best of Nollywood Awards 2009: First Photos". BellaNaija. Retrieved 2021-10-31
 2. Untold Story Of Bisi Komolafe's Mysterious Death – She Died Of Spiritual Attack". MJE Magazine. 4 January 2013. Archived from the original on 27 March 2015. Retrieved 25 August 2015.
 3. Akinnagbe Akintomide (3 January 2013). "PICTURES: THE UNTOLD STORY ABOUT THE MYSTERIOUS DEATH OF MOVIE STAR BISI KOMOLAFE". Nigeria Films. Archived from the original on 10 March 2016. Retrieved 25 August 2015.
 4. Bisi Komolafe biography, net worth, age, family, contact & picture". www.manpower.com.ng. Retrieved 2020-09-30.
 5. Bayo Adetutu (1 January 2013). "Bisi Komolafe, Nollywood actress dies". P.M. News. Retrieved 25 August2015.
 6. Best of Nollywood Awards 2009". BellaNaija. 7 December 2009. Retrieved 25 August 2015.
 7. "Best of Nollywood Awards 2009". BellaNaija. 7 December 2009. Retrieved 25 August 2015.
 8. "BON Winners". Nollywood Mindspace. 9 September 2012. Archived from the original on 2014-10-15. Retrieved 25 August 2015.
 9. Oseyiza Ogbodo (28 December 2013). "January 2013 HIGHLIGHTS: Bisi Komolafe dies". National Mirror. Archived from the original on 2014-08-24. Retrieved 25 August 2015.
 10. Bisi Komolafe's Doctor speaks about her cause of death". Africa Spotlight. January 13, 2013. Archived from the original on 2017-01-04. Retrieved 26 August 2015.
 11. Ebun Sessou (12 January 2013). "Bisi Komolafe's property tears fiancé, family apart". Vanguard. Retrieved 25 August 2015.
 12. Ola Ajayi (4 January 2013). "Tears as Bisi Komolafe goes home". Vanguard. Retrieved 25 August 2015.
 13. Bisi Komolafe biography, net worth, age, family, contact & picture". www.manpower.com.ng. Retrieved 2020-09-30.

Hanyoyin haɗin waje[gyara sashe | gyara masomin]

 • Bisi Komolafe on IMDb