Dabo Aliyu
Dabo Aliyu | |||||
---|---|---|---|---|---|
9 Disamba 1993 - 22 ga Augusta, 1996 ← Bukar Ibrahim - John Ben Kalio (en) →
Nuwamba, 1993 - Disamba 1993 ← Chukwuemeka Ezeife - Mike Attah → | |||||
Rayuwa | |||||
Cikakken suna | Dabo Aliyu | ||||
Haihuwa | Batsari, 29 Disamba 1947 | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Ƙabila | Hausawa | ||||
Harshen uwa | Hausa | ||||
Mutuwa | 13 Disamba 2020 | ||||
Karatu | |||||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa |
Dabo Aliyu CON mni psc (29 ga watan Disambar 1947[ana buƙatar hujja] – 13 ga watan Disambar 2020) ya kasance shugaban riƙo na jihar Anambra daga Nuwamba zuwa Disambar 1993, kuma ya riƙe muƙamin Administrator na jihar Yobe daga Disambar 1993 zuwa Agustan 1996 a lokacin mulkin soja na Janar Sani Abacha. Ya taɓa zama mataimakin darakta NSO Annex State House, Ya kuma kasance Mataimakin Sufeto Janar na ƴan sanda mai kula da shiyya ta 7 Abuja. An ba shi lambar yabo kan rigakafin laifuka, lambar yabo ga mafi kyawun kwamishinan ƴan sanda daga babban sufeton ƴan sanda da kuma bayar da kyautar mafi kyawun aikin ƴan sanda a jihar Anambra. Ya yi zama a Jihar Kaduna, kuma shi ne Sardaunan Ruma, sarauta a garinsa, Ruma.[1]
Mutuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An kawo rahoto cewa Aliyu ya rasu a Kaduna a ranar 13 ga Disambar 2020, bayan rashin lafiya da ba a bayyana ba.[2][3]