Jump to content

Dahiru Mohammed

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Dahiru Mohammed
Gwamnan Jihar Bauchi

ga Janairu, 1992 - Nuwamba, 1993
Abu Ali (Janar soji) - James Kalau
Rayuwa
Haihuwa Yamaltu/Deba, 24 Satumba 1942 (82 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƙabila Hausa
Harshen uwa Hausa
Karatu
Makaranta Vanderbilt University (en) Fassara
Jami'ar Ahmadu Bello
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Employers Africa Bank Capitalisation Fund project (en) Fassara
Mamba Nigerian Institute of Management (en) Fassara
American Economic Association (en) Fassara
Southern Economic Association (en) Fassara
Chartered Institute of Bankers of Nigeria (en) Fassara
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Dahiru Mohammed (an haife shi a ranar 24 ga watan Satumba a shekara ta alif ɗari tara da arbain da biyu 1942Ac) ɗan siyasa ne. Gwamnan jihar Bauchi[1] ne daga watan Janairu a shekara ta 1992 zuwa watan Nuwamba a shekara ta 1993. Alhaji Dahiru Mohammed Deba (an haife shi a shekara ta 1942) ɗan siyasan kasar Najeriya ne wanda aka zaɓa Gwamnan Jihar Bauchi, Najeriya tsakanin watan Janairun shekara ta 1992 zuwa Nuwamba shekara ta 1993 a lokacin Jamhuriya ta Uku ta Nijeriya, inda ya bar ofis bayan juyin mulkin soja da ya kawo Janar Sani Abacha[2] kan mulki.[3]

Farkon rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Deba a ranar 24 ga watan Satumba shekarara ta alif 1942, a Deba, wanda a lokacin tana jihar Bauchi yanzu kuma a jihar Gombe. An ba shi sarautar gargajiya ta Wazirin Deba.[4]

An zaɓi zabi Dahiru gwamna a shekara ta alif 1991 a karkashin kungiyar National Republican Convention (NRC).[5] Nasarorin da ya samu a matsayin gwamna sun hada da gina asibitoci, da suka hada da babban asibitin Alkaleri da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko a Dambam, Zambuk, Bambam da Burra, da kuma gidauniyar asibitin turawa na Gombe. Gwamnatinsa ta gina sabbin otal-otal guda biyu a Jama'are da Ningi. Ya ƙaddamar da Asusun Amincewar Ilimi na Naira miliyan ɗari biyu (200). Wa'adin mulkinsa ya yanke a watan Nuwamba na shekara ta alif 1993 lokacin da Janar Sani Abacha ya kwace mulki.[6]

Dahiru ya zama memba na Democratic Party of Nigeria (DPN), wanda aka kafa a zamanin mulkin Abacha. Ya taimaka wa Danjuma Goje, wanda daga baya ya zama gwamnan jihar Gombe, a zaben Sanatan shekarar 1998 da Abacha ya yi, wanda aka soke bayan mutuwar Abacha.[7]

  1. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://www.thisdaylive.com/index.php/2024/06/24/bauchi-to-revive-tourism-sector/&ved=2ahUKEwjy0ZzC7vaGAxXUZ0EAHc4hBPUQxfQBKAB6BAgaEAE&usg=AOvVaw1o6lDbg_MpqfxuuCeYFKPH
  2. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://www.premiumtimesng.com/news/top-news/694772-abachas-family-challenges-revocation-of-abuja-land.html&ved=2ahUKEwja-uqk7_aGAxWgRkEAHe_BDqoQxfQBKAB6BAgJEAI&usg=AOvVaw1Klg6t9cmLTglxJniRjphr
  3. http://www.worldstatesmen.org/Nigeria_federal_states.htm
  4. http://allafrica.com/stories/201003030213.html
  5. http://allafrica.com/stories/200911110210.html
  6. https://web.archive.org/web/20110725042938/http://www.bauchistategov.org/pastexecutivecouncil.html
  7. http://odili.net/news/source/2008/nov/15/202.html[permanent dead link]