Isa Almasihu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Isa Almasihu / Yesu Kristi.

Isa Almasihu (عيسى), wanda kiristoci masu amfani da harshen Hausa suke kira Yesu Kristi annabi ne daga cikin annabawan Allah. Uwarsa Maryama ta haife shi ba tare da tayi aure ba. Shi Almasihu ruhin Allah ne. Amma a wani gefen kiristoci masu amfani da harshen Hausa sun dauki Almasihu a matsayin dan Allah. Ga al'ummar Hausawa Musulmi, Yesu shine Annabi Isa (Alaihissalam). Sai dai su Musulmi ba su yarda a suranïta annabawa ba don haka Kiristoci masu amfani da Harshen Hausa ne kawai suke gane wannan sura.