Masarautar Karaye

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Masarautar Ƙaraye
Emirate (en) Fassara
Bayanai
Farawa 2019
Ƙasa Najeriya
Babban birni Karaye
Wuri
Map
 11°47′06″N 8°00′40″E / 11.7849°N 8.0111°E / 11.7849; 8.0111
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihajihar Kano

Masarautar Karaye masarauta ce a jihar Kano mai hedikwata a garin Ƙaraye. Sarkin Ƙaraye na yanzu shine Alhaji Dr. Ibrahim Abubakar II.[1][2][3]

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

Garin Ƙaraye hedikwatar masarautar Ƙaraye ce kuma tana yammacin birnin Kano. Tun kafin zuwan Bagauda a shekarar 999, Magurguji ke zaune a Karaye. An kafa garin Ƙaraye a shekara ta 1085. Daga shekarar 1101 zuwa 1793, sarakunan Habe sun yi sarautar Ƙaraye. A zamanin sarakunan Habe, masarautar Karaye ta kara faɗaɗa zuwa yankin Yamma da Arewacin Jihar Kano da ke yanzu.[4]

Dangantaka da Kano[gyara sashe | gyara masomin]

A lokacin da Majalisar Bagauda ke mulki a Kano sun nemi haɗin kan maƙwabciyarsu Masarautar Karaye domin haɗa ƙarfi da ƙarfe domin kare kansu daga wasu masarautu irinsu Zariya da Katsina da Sakkwato . Ƙaraye ta amince ya bada hadin kai da gidan Bagauda inda Ƙaraye ya koma masarautar Kano . Daga lokacin da Karaye yake ƙarƙashin masarautar Kano har zuwan Sarakunan Fulani bayan Jihadin Usman Dan Fodio.[5]

Masarautar Ƙaraye A Yanzu[gyara sashe | gyara masomin]

Masarautar Ƙaraye ta ci gaba da kasancewa a ƙarƙashin Daular Kano har zuwa shekarar 2020 lokacin da gwamnatin jihar Kano ta fitar da wasu sabbin masarautu guda biyar tare da sauya tsarin masarautar Kano. A wancan lokacin gwamnatin Kano ta dawo da sabuwar Masarautar Karaye.[6][7][8][9] Masarautar Ƙaraye ta ƙunshi ƙananan hukumomi takwas na jihar Kano, Karaye, Rogo, Gwarzo, Kabo, Rimin Gado, Madobi, Kiru da Shanono.[10]

Nassoshi[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Lawal, Muhammad Dahiru (2021-06-11). "Karaye Emirate - A Symbol of Hope and Prosperity". Arewa Agenda (in Turanci). Retrieved 2022-12-30.
  2. "Emir of Karaye Archives". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). Archived from the original on 2022-12-30. Retrieved 2022-12-30.
  3. "Dr. Ibrahim Abubakar II Archives". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). Archived from the original on 2022-12-30. Retrieved 2022-12-30.
  4. "Alakar Masarautar Karaye da Gidan Dabon Kano". Aminiya (in Turanci). 2019-05-10. Retrieved 2022-12-30.
  5. Fika, Adamu Mohammed (1978). The Kano Civil War and British over-rule, 1882-1940. Ibadan: Oxford University Press. ISBN 978-154-008-7. OCLC 5246776.
  6. "Why we created more emirates in Kano -Ganduje | The Nation Newspaper" (in Turanci). 2021-05-16. Retrieved 2022-12-30.
  7. "4 Emirates create to transform society- Karaye Emir". TRIUMPH NEWS (in Turanci). Archived from the original on 2022-12-30. Retrieved 2022-12-30.
  8. "Ganduje's Creation Of Kano Emirates Was To Carry Everyone Along, Says Bayero". Channels Television. Retrieved 2022-12-30.
  9. "Ganduje approves 4 new emirates in Kano". Daily Trust (in Turanci). 2019-05-09. Retrieved 2022-12-30.
  10. Buhari, Mustapha (2019-05-08). "Emir of Kano now controls 8 LG district heads as Assembly creates 4 more emirates". Daily Nigerian (in Turanci). Archived from the original on 2022-12-30. Retrieved 2022-12-30.