Jump to content

Muhammad Bello Yabo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Muhammad Bello Yabo
Rayuwa
Sana'a

Muhammad Bello Aliyu Yabo wanda aka fi sani da Bello Yabo (an haife shi a ranar 1,ga watan Junairu shekara ta 1962). Malamin Addinin Musulunci ne a Najeriya kuma ana lissafo shi cikin manyan malaman Najeriya. Malam Bello Yabo ya kuma soki gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari kan rashin tsaro a Arewacin Najeriya, wato (Arewa maso Yammacin Najeriya) musamman a jihohin Zamfara, Sokoto, Kaduna, Katsina da Jihar Neja.[1]

Ilimi da Aiki

[gyara sashe | gyara masomin]

Bello Yabo ya yi makarantar Islamiyya tun yana ƙarami. Bayan ya kammala sai Malam Bello Yabo ya fara makarantar firamare a makarantar firamare ta garin Yabo daga bisani ya wuce makarantar Government Day Secondary School duka dai a garin na Yabo. An kuma naɗa Bello Yabo a matsayin mai ba da shawara na musamman kan kula da hanyoyin karkara.[ana buƙatar hujja] Ya yi aiki a matsayin mai kula da kuɗi na cikin gida a ƙaramar hukumar Dange-Shuni, ya riƙe Daraktan kuɗi na musamman na asibitin Sokoto, daraktan kuɗi ma'aikatar ilimi ta Sokoto. Sheikh Bello yabo yana cikin sahun malamman da suka yi yaƙi da Akidar boko haram a Nigeria.

Sukar El-Rufa'i

[gyara sashe | gyara masomin]

A shekarar 2020 yayin da annobar cutar numfashi ta COVID-19 ta ɓulla a jihar Sokoto, Bello Yabo, babban malamin addinin Islama na jihar Sokoto, bayan wani faifan bidiyo ya bayyana a soshiyal midiya yana kiran sauran mabiya addinin Musulunci da su fito ƙwansu da ƙwar-ƙwarta su don Sallar Eid-el-Fitr bayan sun yi azumin watan Ramadan.[2] Wanda har ya nuna cewa cutar bata yaɗu ba a Najeriya saboda haka babu dalilin da za'a hana mutane yin Addinin su. Haka kuma a wani wani faifan bidiyo wanda kuma ya yi Allah wadai da hana Sallar Idi, a Jihar Kaduna. Wanda a faifan bidiyon ya caccaki Gwamnan jihar Kaduna El-Rufae da sauran gwamnoni kan hana Sallar Idi a jihohinsu. Rundunar ƴan sandan Najeriya ta gayyaci Bello Yabo saboda wannan faifan bidiyon na rana ɗaya wanda ya sifanta gwamnan Kaduna El-Rufa'i da "ɗan ƙaramin tsuntsu".[3][4][5][6][7]

Kungiyar Izala

  1. Ammani, Ibrahim (9 December 2021). "Buhari Ya Ci Amanar 'Yan Najeriya – Sheikh Bello Yabo". Muryarƴanci.com. Retrieved 23 May 2022.
  2. "Islamic Cleric, Sheik Bello Yabo, Arrested For Condemning Eid Prayers Ban". saharareporters.com. 22 May 2020. Retrieved 23 May 2022.
  3. Bello, Nasiru (25 May 2020). "Makirci Aka Shirya Da Aka Kama Ni —Malam Bello Yabo". Aminiya.dailytrust.com. Retrieved 23 May 2022.
  4. Usman, Jamil (23 May 2020). "An damke malamin da ya yi wa El-Rufai 'wankin babban bargo' a kan hana sallar Idi". legit.hausa.ng. Retrieved 23 May 2022.
  5. Hassan, Maryam (23 May 2020). "Sokoto-based Islamic scholar, Bello Yabo, arrested for criticizing El-Rufai" (in Turanci). dailynigerian.com. Archived from the original on 23 May 2022. Retrieved 23 May 2022.
  6. Ikeke, Nkem (23 May 2020). "Islamic cleric arrested in Sokoto for criticising Governor El-Rufai". legit.ng. Archived from the original on 23 May 2022. Retrieved 23 May 2022.
  7. Holland, Kitty (26 May 2020). "Islamic scholar arrested for criticising El-Rufai regains freedom". thestreetjournal.org. Retrieved 23 May 2022.