Nasiru Idris

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Nasiru Idris
Gwamnan Jihar Kebbi

2023 -
Rayuwa
Haihuwa Birnin Kebbi, 6 ga Augusta, 1965 (58 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Usmanu Danfodiyo
Harsuna Hausa
Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da trade unionist (en) Fassara
Imani
Addini Musulunci
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress

Mohammed Nasir Idris (an haife shi 6 ga Agusta[ana buƙatar hujja]1965) ne, ƙwararren ilimi, ɗan siyasa wanda yake rike da mukamin gwamnan jihar Kebbi a halin yanzu. A baya ya taba zama shugaban kungiyar malamai ta Najeriya kuma mataimakin shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya.[1] A ranar 17 ga Afrilu, 2023, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana Idris a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kebbi a shekarar 2023.[2][3]

Rayuwar farko da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Nasir Idris a ranar 6 ga watan Agusta[ana buƙatar hujja] ƙaramar hukumar Birnin Kebbi a jihar Kebbi.[4] Ya halarci Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Birnin Kebbi tsakanin shekarar 1994 zuwa 2003, da Jami'ar Usmanu Danfodio, Sokoto, tsakanin 2006 zuwa 2009 don yin MBA. [4] Idris ya yi digirin digirgir a fannin ilimi kuma ya rubuta kasidu daban-daban kan ilimi.[5]

Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]

A shekarar 2018, an zaɓi Idris a matsayin shugaban kungiyar malamai ta Najeriya (NUT) da kuma mataimakin shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya NLC.[6] Tsohon shugaban kungiyar NUT reshen jihar Kebbi, tsohon shugaban NLC, jihar Kebbi kuma tsohon ma'ajin kungiyar NUT ta kasa.[7] A watan Mayun 2022, Mista Idris ya fito a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na jihar Kebbi a zaben fidda gwani na gwamnan APC.[8] A ranar 17 ga Afrilu, 2023, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ayyana Idris a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kebbi a shekarar 2023.[9]

Nassoshi[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Sub-editor (2023-04-17). "Meet Dr Nasiru Idris, winner of Kebbi State Governorship Election". NewsWireNGR (in Turanci). Retrieved 2023-04-22.
  2. "Kebbi poll: INEC declares APC guber candidate, Nasir Idris, winner". Punch Newspapers (in Turanci). 2023-04-17. Retrieved 2023-04-22.
  3. "My Top Priority is education sector in Kebbi – Governor Elect Dr. Nasir Idris - INDEPENDENT POST NIGERIA" (in Turanci). 2023-04-17. Retrieved 2023-04-22.
  4. 4.0 4.1 "Decision Day 2023: Those who will be governors". The Sun News Online.
  5. "Seven things to know about Kebbi gov-elect, Idris". Punch Newspapers (in Turanci). 2023-04-16. Retrieved 2023-04-22.
  6. Rapheal (2019-05-07). nut-president/ "It's wickedness to pay primary school teachers salary in percentage, says Nasir, NUT President" Check |url= value (help). The Sun Nigeria (in Turanci). Retrieved 2023-04-22.
  7. "NUT National President, Nasir Idris emerges Kebbi APC Guber candidate – Nigeria News" (in Turanci). Retrieved 2023-04-22.
  8. "NUT National President, Nasir Idris emerges Kebbi APC Guber candidate – Nigeria News" (in Turanci). Retrieved 2023-04-22.
  9. "APC's Nasiru Idris Wins Kebbi Governorship Poll – THISDAYLIVE". www.thisdaylive.com. Retrieved 2023-04-22.