Rufaida Umar Ibrahim
Appearance
Rufaida Umar Ibrahim | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | jahar Kano, 16 ga Janairu, 1995 (29 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Harshen uwa | Fillanci |
Karatu | |
Makaranta | Federal College of Education, Kano |
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | marubuci |
Rufaida Umar Ibrahim (Shekarar haihuwa; An haife ta a ranar 16 ga watan Janairun shekara ta alif 1995) fitacciyar marubuciyar harshen Hausa ce kuma mawallafiyar littattafai daga birnin Kano cikin Jihar Kano a arewa maso yammacin Najeriya. Tauraruwarta ta fara haskawa ne a shekarar 2020 bayan ta lashe manyan gasannin gajerun labarai da manyan kafafen watsa labarai suka sanya ciki harda gasar gajerun labarai ta BBC Hausa inda ta zo a matsayin ta 3 a Hikayata na shekarar 2020.[1] Ita ce kuma ta zamo gwarzuwar gasar Aminiya Trust a matsayin ta 1 wadda kamfanin jarida na Aminiya suka ɗauki nauyi a shekarar 2020. Wannan yasa ake yi mata kallon marubuciyar Hausa da babu kamarta a wannan lokaci. [2]