Saad al Ghamidi
![]() | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | سعد بن سعيد بن سعد الغامدي |
Haihuwa | Dammam, 7 ga Augusta, 1967 (57 shekaru) |
ƙasa | Saudi Arebiya |
Harshen uwa | Larabci |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Imam Muhammad ibn Saud Islamic |
Harsuna | Larabci |
Sana'a | |
Sana'a |
Liman da qāriʾ (en) ![]() |
Imani | |
Addini | Musulunci |
Sa'ad al-Ghāmidī ( Larabci: سعد الغامدي; An haife shi a shekarar 1967) mahaddaci ne kuma limamin babban masallaci mai alfarma Masjid an-Nabawi. Al-Ghamdi ya zama limami ga al'ummar musulmi a faɗin duniya.[1]
Tarihin Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi al-Ghāmidi a Dammam, Saudi Arabia a shekara ta 1967. Ya haddace Al-Qur'ani mai girma gaba dayansa a shekarar 1990 lokacin yana ɗan shekara 22. Ya shahara a bangare tajwidi. Ya karanci bangaren shari'ar Musulunci (Islamic Studies) a Dammam, musamman a mazhabar Shari'a, tushen dokokin addinin musulmi . A shekarar 2012 aka nada shi a matsayin Limamin Masallacin Yousef bin Ahmed Kanoo da ke birnin Dammam kafin nan ya jagoranci sallah a masallatai da dama na duniya ciki har da Amurka da Ingila da Ostiriya.
A cikin Ramadan a shekarar 2009, Sheikh Sa'd al-Ghāmidi ya shugabanci sallar Tarāwīḥ a al-Masjid an-Nabawi (Madina's Holy site of Islam) na Madina.
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ News, Arab (28 July 2018). "FaceOf: Sheikh Khalid Al-Ghamdi, Imam at the Grand Mosque in Makkah". Arabnews.com. Arabnews. Retrieved May 22, 2023.