Shinkafa da Taliya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Shinkafa da Taliya wani nau'in abinci ne wanda ake samunshi musamman a kasar hausawa. Ana dafa abincin ne hadi da Shinkafa da kuma taliya. [1]

Yadda ake Girka Shinkafa da Taliya[gyara sashe | gyara masomin]

Kayan da ake bukata

  1. Shinkafa
  2. Taliya
  3. Carrot
  4. Tarugu
  5. Tattasai
  6. Albasa
  7. Dandano
  8. Curry
  9. Kifi
  10. Mai
  11. Ruwa

Yanda ake dafawa[gyara sashe | gyara masomin]

  • Mataki 1

Zaki daura tukunyarki tsaftatacciya kan murhu sae ki ruba ruwa ki saka curry sae ki rufe

  • Mataki 2

Idan tukunyarki ta tafasa sae ki kawo shinkafarki ki motse ki rufe baya 10 min sae ki kawo taliyarki ki zuba karki kareta ki sakata yanda take sae ki motse bayan 5 min sae ki sauke ki dauraye ki ajiye

  • Mataki 3

Sae ki yanka tarugunki da attasae da albasa da lawashi amma ko wanne amai mazubinshi daban

  • Mataki 4

Sai zuba Mai cikin tsaftatacciyar pan inki me girma sae idan ya fara zafi sae ki zuba tarugunki,tattasae,kifi, carrot, dandano,curry sae kita motsawa idan carrot inki y fara taushi sae ki kawo shinkafarki da taliya da Kika tsane sae ki zuba kina motsawa ahankali saboda kar taliyarki ta kare kuma kar shinkafarki ta dame.[2]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]