Solomon Arase
Solomon Arase | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Sapele (Nijeriya), 21 ga Yuni, 1956 (68 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Harshen uwa | Harshen Edo |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Ahmadu Bello |
Harsuna |
Turanci Harshen Edo Pidgin na Najeriya |
Sana'a |
Solomon Ehigiator Arase (an haife shi 21 ga Yuni, shekara ta alif ɗari tara da hamsin da shida 1956) ɗan sandan Najeriya ne mai ritaya wanda ya yi aiki a matsayin Sufeto-Janar na ƴan sandan Najeriya na 18 (IGP) . Shugaban kasa Goodluck Jonathan ne ya nada shi IGP a shekarar 2015 bayan an tube Suleiman Abba . Kafin nadin sa a matsayin IGP, Arase ya kasance shugaban babban sashin tattara bayanan sirri na ‘yan sandan Najeriya, hukumar leken asiri da binciken manyan laifuka.[1]
Rayuwa da aiki
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Arase ranar 21 ga watan Yuni, 1956 a karamar hukumar Owan ta Yamma, jihar Edo a Kudancin Najeriya. Ya halarci Jami'ar Ahmadu Bello inda ya yi karatun digirinsa na farko kuma ya kammala karatunsa na digiri a fannin siyasa a shekara ta 1980. An dauke shi aikin ‘yan sandan Najeriya shekara guda bayan ranar 1 ga Disamba, 1981. Ya kuma sake samun digirin farko a fannin shari'a a Jami'ar Benin da kuma Masters daga Jami'ar Legas .
Yayin da yake aikin ‘yan sanda, Arase ya yi ayyuka da dama da suka hada da zama kwamishinan ‘yan sanda a jihar Akwa Ibom da kuma sashin tattara bayanan sirri a matsayin mataimakin sufeto Janar. Shi ma'aikaci ne a ƙwalejin Tsaro ta Najeriya kuma ya yi aiki a Namibia a lokacin aikin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya.[2][3][4]
Arase ya yi ritaya daga aikin a ranar 21 ga Yuni na shekara ta, 2016. A ranar 21 ga watan Yuni, 2016, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Ibrahim Kpotum Idris a matsayin Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya . Bayan ya yi ritaya daga aikin ‘yan sanda, an nada Arase shugaban kwamitin da ke da alhakin aiwatar da dokar ƙungiyar ci gaban al’umma ta jiha a jihar Edo.[4][5][6] [7]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Vanguard Newspaper. "Jonathan sacks Suleiman Abba, appoints Arase". Retrieved 28 April 2015.
- ↑ "Meet Nigeria's new Inspector General of Police, Solomon Arase | Premium Times Nigeria" (in Turanci). 2015-04-21. Retrieved 2022-03-17.
- ↑ "How I will spend the rest of my life — Ex-Police IG, Solomon Arase". Premium Times. Retrieved 9 September 2018.
- ↑ 4.0 4.1 Nnennah, Ibeh. "Meet Nigeria's new Inspector General of Police, Solomon Arase". Premium Times. Retrieved 10 September 2018.
- ↑ "Six DIG's to be retired as Arase bows out - Vanguard News". Vanguardngr.com. 2016-06-21. Retrieved 2016-08-07.
- ↑ "Buhari congratulates new Acting IGP Ibrahim Idris as Arase bows out - Vanguard News". Vanguardngr.com. 2016-06-21. Retrieved 2016-08-07.
- ↑ Funsho, Akinwale. "Former IGP, Solomon Arase, gets new job". Guardian. Archived from the original on 9 September 2018. Retrieved 9 September 2018.