Tarihin Gabas Ta Tsakiya
Tarihin Gabas Ta Tsakiya | ||||
---|---|---|---|---|
history of a geographic region (en) , aspect of history (en) da study of history (en) | ||||
Bayanai | ||||
Ƙaramin ɓangare na | history of Asia (en) da Tarihin Afirka | |||
Facet of (en) | Gabas ta tsakiya | |||
Gudanarwan | historian of the Middle East (en) | |||
Wuri | ||||
|
Gabas ta Tsakiya, ko kuma Gabas ta Kusa, gida ne ga ɗaya daga cikin Cibiyoyi na Wayewa kuma suna da al'adu da wayewa mafi tsufa a duniya. Tarihin yankin ya fara ne daga matsugunan mutanen farko kuma ya ci gaba ya zuwa manyan dauloli kafin da kuma bayan Musulunci har zuwa kasashen gabas ta tsakiya ta yau. Mutanen Sumeriya sun zama mutane na farko da suka samar da tsarin na musamman wanda za a iya kira "wayewa" tun daga karni na 5 BC. Wayewar Masar ta soma ne tun kusan shekara ta 3150 BC tare da haɗewar siyasa ta Sama da Ƙarƙashin Masar a ƙarƙashin Fir'auna na farko . Mesopotamiya ta kasance gida ga dauloli masu ƙarfi da dama waɗanda suka mulka kusan daukakin yankin Gabas ta Tsakiya, musamman daular Assiriya na 1365-1076 BC da Daular Neo-Assyrian na 911-609 BC. Tun daga farkon karni na 7 BC zuwa gaba, Mediya na Iran, da kuma Daular Achaemenid da sauran jahohi da daulolin Iran da suka biyo baya, sun mamaye yankin. A cikin karni na 1 BC, Jamhuriyar Roma ta mamaye Gabashin Bahar Rum gaba daya, wanda ya hada da yawancin Gabas ta Kusa. Daular Roma ta Gabas, yanzu da aka fi sani da Daular Bazantina, ta mulki daga Balkans zuwa Euphrates, ta ƙara bayyana ta da ƙa'idodi na addinin Kiristanci kuma a hankali ya haifar da ɓatanci na addini tsakanin koyarwar da aka kafa a Konstantinoful da mabiyansu a yawancin sassan Gabas ta Tsakiya. Daga karni na 3 zuwa karni na 7 AD, Rumawa ne da Daular Sasaniya sun mamaye daukakin yankunan Gabas ta Tsakiya. Daga karni na 7, wani sabon iko ya taso a yankin Gabas ta Tsakiya, shine Musulunci. kwatsam a tsakiyar karni na 11 mulkin Larabawa ya zo karshe tare da zuwan daular Seljuq. A farkon karni na 13, wani sabon guguwar mahara, sojojin daular Mongol, galibi Turkic, sun mamaye yankin. A farkon karni na 15, sabon iko ya taso daga yammacin Anatoliya, sarakunan Ottoman, wadanda Turkawa ne a harshe kuma mabiya addinin Islama sanann a shekarar 1453 sun kwace babban birnin Rumawa na Kirista na Constantinoful kuma suka mai da kansu sarakuna.
Manyan sassa na Gabas ta Tsakiya sun zama fagen fama tsakanin Daular Usmaniyya da Daular Safawad ta Iran tun a farkon karni na 16. A shekara ta 1700, an kori Usmaniyawa daga Masarautar Hungary kuma ma'auni na ikon sun koma zuwa yammacin duniya . Daular Biritaniya kuma ta kafa cikakken iko a Tekun Fasha, kuma daular Faransa ta fadada mulkinta har zuwa Lebanon da Siriya. A shekara ta 1912, Masarautar Italiya ta kwace Libya da tsibiran Dodecanese, kusa da gabar tsakiyar Ottoman na yankin Anatoliya. A karshen karni na 19 da farkon karni na 20, sarakunan Gabas ta Tsakiya sun yi kokarin zamanantar da jihohinsu don kara yin gogayya da kasashen Turai. Muhimmin lokaci a tarihin yankin ya zo ne lokacin da aka gano mai a yankin, da farko a Farisa a 1908 sannan a Saudi Arabia (a 1938) da sauran kasashen Gulf na Farisa, da kuma Libya da Aljeriya. Dogaro da Yammacin Turai kan mai na Gabas ta Tsakiya da raguwar tasirin Burtaniya ya haifar da karuwar sha'awar Amurka a yankin.