Yakubu Musa Katsina

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Yakubu Musa Katsina
Rayuwa
Haihuwa Gwaram, 1 ga Janairu, 1950 (74 shekaru)
Sana'a
Sheikh

Yakubu Musa Katsina
Personal
Haihuwa (1950-01-01)1 Janairu 1950
Addini Islam
Kabila Hausa
Era Modern era
Yanki Northern Nigeria
Akida Sunni
Dabbaga Izala[1]
Aiki mafi so Da'awah
Sana'a Teacher
Farmer
Muslim leader

Yakubu Musa Katsina wanda aka fi sani da Yakubu Musa Hassan sanannen malamin addinin Islama ne dake zaune a Jihar Katsina amma Dan asalin garin Kafanchan ne na jihar Kaduna,kuma memba ne na shugabannin kafa daya daga cikin manyan kungiyoyin Musulunci a Afirka ta Yamma mai suna JIBWIS,wato Izala kamar yadda aka fi sanin kungiyar a Arewacin Najeriya inda har yanzu yake cikin ƙungiyar,a matsayin Shugaban kwamitin na Amintattu.

Rayuwar farko da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

Sheikh Yakubu Musa Katsina an haife shi ne a Gwaram Local Governmernt na jihar Jigawa kuma ya girma ne a jihar Kano, Jos, Plateau da kuma jihar Katsina . Ya fara karatun ilimin Musulunci da ilimi a karkashin mahaifinsa. Yana ɗan shekara bakwai, mijin yayarsa ya ɗauke shi wanda shi ma ɗan uwa ne ga dangin su na Kano, domin yayi karatun Alkur'ani kamar yadda aka saba. Ya kasance a gidan yayarsa inda ya koyi Al-Qur'ani kuma ya haddace shi. Haka kuma yayi karatun wasu littattafan addinin Musulunci na gargajiya a Kano.A lokacin da ya kai shekaru bakwai,tuni ya fara koyon wasu ayyukan kere kere don dogaro da kai. Ya riga ya san fasahar tukwane daga mahaifinsa da kuma yin kwalin ƙarfe. Yayinda yake kano,ya koyi kamun kifi kuma abokansa suka amince dashi a matsayin masanin masunci.

Daga baya,ya dawo Gwaram. Amma bai zauna da yawa ba har sai da ya yi tattaki zuwa garin Jos don ci gaba da karatunsa tare da kawun mahaifinsa,Sheik Ibrahim Mushaddidu,sanannen malamin Tijjaniyya ne Muqaddami kuma a Nijeriya dukka a wancan lokacin.A Jos,Yakubu Musa ya shiga makarantar Islamiyya ta zamani wacce J.N.I (Jama'atu Nasril Islam) ta kafa don horar da daliban da suka kammala karatunsu na makarantun allo.A waccan makarantar, Yakubu Musa ya yi fice sannan aka daga shi zuwa bangaren sakandare na makarantar JNI. An kuma horar da shi daidai a matsayin murshid na JNI.Irin wannan horon ya rinjayi aikinsa na gaba a matsayin mai yada addinin musulunci.

Canza akida Tijjaniyya zuwa Izala[gyara sashe | gyara masomin]

Lokacin da Addinin Islama ya sami fadada sosai a Kafanchan, yanzu haka yana cikin jihar Kaduna, sai mutanen garin suka nemi malamai da masu wa'azi. An aika Yakubu Musa tare da wasu mutum uku. A lokacin duk suna bin Darikar Tijjaniyya Sufi a Kafanchan ne, makarantun da aka bunkasa na yara da manya.

A wancan lokacin, da'awah din Sheikh Abubakar Gumi tana kara samun daukaka kuma Rediyon Najeriya Kaduna ya watsa shi. Sukar da yake yi game da Sufaye ko yaushe yana da sha'awar duk mai hankali. Yakubu Musa yana cikinsu. Sannan ya fara yin bincike kan abin da aka samu a cikin Alqurani da Sunnar annabawa tare da abin da Sheikh Gumi ya nuna a matsayin rashin zuwa Sufanci. Saboda haka, Yakubu Musa ya canza daga riko da Sufanci zuwa Izala. Sannan ya yi mubaya'a tare da Sheikh Gumi kuma ya zama dalibi na kusa da shi. Ya halarci Kwalejin Koyar da Larabci da ke Katsina sannan kuma ya tafi Kwalejin Kimiyyar da Fasaha ta Hassan Usman Katsina, Sashen Nazarin Shari'a kafin daga baya ya zama malamin addinin Musulunci a Najeriya.

Koyarwa[gyara sashe | gyara masomin]

Ya kafa Makarantar Islamiyya ta Riyadhul Kur'an da Sautussunnah Comprehensive Secondary School duk a cikin jihar Katsina.

Kasancewarsa baƙon indean jihar Katsina, birni mafi yawan musulmai a arewacin Najeriya, an ga Sheikh Katsina ya fito fili ya nuna adawa da cin hanci da rashawa da sauran rashin adalci a ƙasar.

Marataba[gyara sashe | gyara masomin]

A watan Yulin 2020, an saka Yakubu a cikin mujallar "Musulmai 500 " a matsayin daya daga cikin musulmai 500 da suka fi tasiri a duniya, a shekarar 2020.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Sheikh Musa-Hassan backs FG plan to modernise Almajiri education -". The Eagle Online. 7 July 2019. Retrieved 23 April 2020.