Adabi hausa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

TASIRIN ADABIN LARABAWA GA RAYUWAR HAUSAWA

Adabi dai kamar yadda malamai kan fassara shi, shi ne: Hanyar rayuwar al'umma ta yadda suke cin abinci da sha, da sanya tufafi da gudanar da al'adu ta hanyar bukukuwansu na aure ko na suna, da kuma a wajen mutuwa da dai sauran hanyonyi hulda da jama'a na daga makwabtaka da sadar da zumunta.

Babu shakka kowacce al'umma ko kuma mu ce kowacce kabila suna da nasu adabi. A dalilin haka, Hausawa suna da nasu adabi wanda yake malamai sun rubuta littafai a kansa. Ta haka ba sai na tsaya yin bayani a kansa ba. Abu ne mai wuya a raba rayuwar Hausawa da Musulunci; wannan kuwa saboda kasancewar shi ne ya kawo wa wannan kasa ci-gaba da wayewa kafin zuwan Turawa a wannan kasa. Kuma har yanzu tasirin Musulunci da wayewarsa suna nan a cikin al'ummar Hausawa fiye da rayuwar da Bature ya zo da ita. A dalilin haka ne za mu ga adabin Larabawa na jahiliyya da na lokacin Musulunci ya mamaye rubuce- rubucen malaman wananan kasa na zube da kuma wake. Kai ba ma wannan ba, hatta da mawakan baka akwai ta'asirin adabin Larabci a cikinsu. Wannan na nuna muna cewa haduwa da bakin al'adu sabanin wadanda mutum ya tasa a cikinsu suna iya tasiri a gare shi.

Malamai da yawa sun yi rubuce-rubuce a cikin harshen Larabci kuma da Hausa a wanann kasa kafin bayyanar Shehu Usmanu Danfodiyo. Wannan misali kamar su Mallam Danmasani a Katsina. Haka kuma da Mallam Muhammad na Birnin Gwari mai wakar Gangar Wa'azu.

    Bayan bayyanar Shehu Usman a karni na 19, sai rubutu ya kankama daga gare shi da almajiransa, kamar su Mallam Abdullahi da Muhammadu Bello da Buhari da Nana Asma'u. Haka kuma wadanda suka biyo bayansu a cikin wannan karni da kuma mai bi masa na 20, an yi rubuce-rubuce masu tarin yawa wadanda kuma duk suna da ta'asiri da Adabin Larabawa. Zai yiwu akwai wakoki na baka da aka yi a wandacan lokuta, amma saboda rashin kula da rubutun tarihi ya zama ba a ruwaito su ba. Domin ba mai wakar baka ba, a'a har rubuce-rubucen addini masu yawa sun salwanta a wannan kasa a dalilin rashin kula da tarihi. Wannan kamar yadda Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ya fada: “Akwai sakaci da jahilci da bi ma son rai a wannan nahiya. Abin da ya hana su kula da tarihi”.
 3.RUBUCE-RUBUCEN BOKO
    A lokacin da Turawa suka ci wannan kasa suka kaddamar da ilmin boko sai ya zama akwai bukatar littafai domin koyarwa da karatu. A dalilin haka ne, kamar yadda masana tarihin suka ambata, aka kafa Hukumar Fassara, daga baya kuma aka samu Ma'aikatar Talifi a Zariya. Wadannan wallafe-wallafe sun kankama ne a wajajen shekara ta 1933. Daga nan kuma har zuwa shekar ta 1959. Galibin wadannan wallafe-wallafe sun kasance a bisa jigo na addini da siyasa, da ilimi da kiyon lafiya da ci-gaban zaman jama'a kuma da al'adun Hauswa, da sauransu. Bayan haka, kuma rubuce-rubucen Hausa sun yawaita ainun har zuwa shekara ta 1979. Amma mafi yawan wadannan rubuce-rubucen na baya sun fi mayar da karfi ga almara da tatsuniyoyi. Daga shekara ta 1980 sai aka fara samun marubuta wadanda suka fara rubuce-rubuce a kan irin wadannan littafai na gurbata tunanin makaranta kamar yadda wani marubuci ya ce ta hanyar mayar da ilahirin hankalisu ga jigo na haramtacciyar soyayya.
4. BAYYANAR LITTAFAN SOYAYYA

Masana sun yi bayanin cewa littafin soyayya na farko da aka rubuta aka kuma kai kasuwa shi ne RABIN RAINA, wanda Talatu Wada Ahmad ta rubuta a shekarar 1984. Wanda ya biyo bayansa shi ne SOYAYYA GAMON JINI wanda Ibrahim Hamza Abdullahi Bichi ya rubuta a shekarar 1986. Sai kuma KOGIN SOYAYYA Idaris A.M Zaharadeen, shi kuma a shekara ta 1988. Daga nan sai IDAN SO YA YI SO na Yusuf Muhammad Adam, shi kuma a shekarar 1989.

Daga nan sai wadannan littafai suka ci-gaba da karuwa; suna bayyana a birane da kauyuka. Rubuce-rubucen da suka gabata na Adabin Hausa na kiyaye al'adun Hausawa da kyawawan dabi'unsu na kamar kunya da mutunci d amana da rikon addini. Su kuwa littafan soyayya ya zama sun dogara ne a kan rubuce-rubucen Turawa wadanda ba ruwansu da addini. Shi Bature ganin yake aure ba zai yi kyau ba da armashi face sai saurayi da budurwa sun yi rayuwar soyayya na wani lokaci. Wannan wai domin su fahimci juna kafin su yi aure. Ba ma wannan kadai ba, su Turawa ganin suke yi hatta da matan aure kamata ya yi a ce suna da ‘yancin rikon wadansu abokan soyayya maza.

Da wannan dan bayani da ya gabata za mu ga cewa kamar yadda Muhammad Mujtaba Abubakar ya ambata a cikin littafinsa mai suna SOYAYYA A MA'AUNIN HANKALI DA SHARI’A, littafan soyayya na zamani suna da wadannan aibobi:

  Lalata tarbiyar samari da 'yanmata, ta hanyar saurayi ga shi da halin yin aure, amma ya kai wadansu shekaru bai yi ba, saboda yana samun irin wadancan 'yanmata masu ra'ayi irin nasa. Ita kuma budurwa ta ki fitar da miji da wuri, har sai ta yi samari barkatai.
  Watsa alfasha. A ra'ayin littafan soyayya; ‘yan wasanni tsakanin saurayi da budurwa kamar sumbuta, rungumar juna da shafe shafen jikin juna su ne gishirin soyayya. Idan babu su, babu soyayya.
  Tozarta lokaci: Idan mutum ya cika makarancin littafan soyayya, to shi ba dare ba rana ga wannan. Ana kammala wannan littafi ana fadawa wani. Domin a koyaushe littafan kwararowa suke a kasuwa. Shi kuma makarancin wadannan littafan bai yarda a ba shi labarin wata tatsuniya da bai karanta ba.
  Shishita saurayi ga auren budurwa marasa tarbiyya, ko budurwa ta auri saurayi maras tarbiyya. Wannan kuwa domin marubuta wadannan littafai suna nuna rayuwar aure ba za ta yi armashi ba, sai saurayi da budurwa sun yi rayuwar soyayya ta wani lokaci. Wannan kuwa al’ada ce ta Turawa kamar yadda aka gabatar.
  Jefa samari da ‘yanmata a cikin duniyar mafarki. Wannan domin ta hanyar karatun wadannan littafai, saurayi ya kan koyi dabarun yaudarar ‘yanmata, domin ya yi amfani da su (Watau zina). A wani lokaci kuma ya koyi hanyar yadda zai raba wani saurayi da budurwarsa. Su ma 'yanmatan haka, sukan koyi makirci da hanyiyin kwace ma wadansu 'yanmatan samari. Muradin wadannan samari da 'yanmata samun dabarun neman abokan haramtacciyar alaka.
  Gina al'umma a bisa ga harsashi maras inganci, domin al'umma tana kasancewa ta-gari idan marubuta a cikinsu suka mayar da hankalinsu a wajen rubutunsu ga jigo na addini da tarbiyya, haka kuma da ilmin kyautata rayuwa da dabi'u da sana'o'i. Amma idan samari suka koma ba za su kula da abin da zai amfane su,ko ya amfani al'ummarsu ba, wannan  sai ya kasance sun halaka.

Ganin wadannan abubuwa masu hatsari ya sa sassan mutane na daga masana naAdabi daga malamai da masu tarbiyya suka nuna rashin amfanin yin wadannan littafai da cewa kuma masu rosawa ne ga al'umma. Ga abin da wani mai sharhi a kan Adabin Hausa ya fada a game da wannan matsala, watau Isa Sanusi a cikin mujallar Rana fitowa ta 76:

“Ya kamata mu gane cewa mutuncin kowace al'umma ya dogara ne ga yadda ta mutunta komai nata daidai da addininta da kuma al'adu. A gaskiya ya kamata marubutan Hausa su farka su yi rubutu, amma ba kowane iri ba. Kuma muna nan muna jira mu ga marubutan sun motsa daga batun soyayya su ci-gaba”.
    Da wannan za mu ce wadannan littafai da irin sigarsu ta yanzu karatunsu yana da hatsari, kuma yana ja zuwa ga abubuwan can guda shida da aka ambata a sama. A dalilin haka karanta su ba ya halatta, face sai ga wanda ke son ya ga barnar da ke ciki, domin ya mayar da martani. Wannnan idan ya zama ya aminta da kansa. Amma idan aka tsabtace su daga alfasha da batsa da sauransu, wannan babu laifi a karanta, domin shi adabi yakan canja kamar sauran duk abubuwan da ke karbar canji.
Fadakarwa: A nan wani zai ce, ai akwai littafai na Adabin Larabci wadanda suke na zamanin Jahiliyya kuma da wadanda suke a cikin zamani na Musulunci, kuma akwai ambaton soyayya a ciki. To, yaya al'amarin yake? A nan zan gaya wa mai karatu cewa, ba kalmar so Musulunci ya ki ba, a'a so tsabtatacce ne a cikin Musulunci. Amma gurbata shi, shi ne aka hana. Haka kuma duk wakokin Adabi na Jahiliyya da na Musulunci, babu inda kalmar batsa, ko alfasha ta fito fili, face sai ga 'yan kadan, haka kuma agalibi an cudanya wannan soyayya ta su da jaruntaka. Kuma soyayya wadda ta bayyana a zamanin daular Bani Umayya kuma da daular Bani Abbas an ba ta sunan AL’HUBBU Al’AFIF, watau tsarkakakkiyar soyayya, watau dai wadda babu alfasha a ciki. A bisa ga misali UMR'UL KAISI da ya rayu a cikin Jahiliyya a wani baiti nasa yana cewa:

" A ranar da na soke taguwata ga 'yan mata, akwai mamaki ga sirdinta da ya kasance abin dauka”

Haka kuma Antar Dan Shaddadu ga abin da ya ce a game da abin sonsa ABLA:
“Abla ta yi mamaki ga saurayi mai sadaukar da kai,wanda bai shafa mai ba, kuma bai shace kansa ba tsawon shekara”
    A game da Majnunu Laila:
“ Ke ce kika fura wutar so da bege a cikin zuciya, sa'annan ya zama kina tsoron wutar mai cin fata da gashi”
    Haka shi ma Kaisu na Lubna ya ce:
“Hakika Allah Yana hada masoya biyu, bayan sun zaci cewa, ba su koma haduwa”. 
    Haka ku ma Jamilu Busnina ya ce:
“Da a ce na makance, na kurumce, ya zama Busaina ita ke yi min jagora, to da maganarta (Busaina) ba ta boyuwa a gare ni”.
    To, duk idan muka duba ga wadannan wakoki za mu ga babu alfasha kuma babu batsa. A dalilin haka ne manyan malamai suka zama suna kafa hujja da ire-iren karanta wadannan littafai domin fahimtar harshe.

FINAFINAI

    A game da finafinai, ko kuwa kaset-kaset da yawaitarsu an yi rubuce-rubuce da ka-ce-na-ce a game da su. Ga abin da Isa Sanusi yake cewa ga makalarsa mai taken: Finafinai Hausa Ina aka dosa? Wannan a cikin mujallar Rana, fitowa ta 77:

“Ba sai an nanata ba, finafinan Hausa suna tashe sosai a kasar Hausa da ma sauran sassan kasar nan inda Hausawa ke zaune. Ko'ina ka duba za ka ga shagunan saidawa ko kuma ba da hayar kaset-kaset na finafinan Hausa. Ga shi kuma yara da manya duk na matukar sha'awar abin. In ka shiga tasha ko kasuwa sai ka ji wakokin finafinan Hausa suna tashi ta ko'ina. Ga kuma fastocin Finafinan a kan tituna. Abin ba wai a birane ba ne har ma da karkara. Kafin bullowar finafinai Hausa mun dogara ne ga kallon finafinan kasashen waje, kamar na Amuruka, Chaina, indiya, Japan da sauransu”.

     Har wa yau, a game da yawaitar finafinai ga abin da wani marbuci ke cewa, watau Mauhammad Mujtaba Abubakar a cikin littafinsa da ya gabata:
 “Hakika miyagun rubutattun tatsuniyoyi su ne suka haifi munanan Finafinai a wannan fage na majigi, finafinan Indiya sun fi shahara da jigon soyayya. Akasarin finafinan Amuruka da sauran kasashen Yammacin Turai su suna kasancewa a kan jogon jarunta da na ta'addanci kamar sata, da fashi da makami, da safarar miyagun kwayoyi da fyade da zinace-zinace da kuma liwadi da madigo”.
    Haka kuma wani marubuci mai suna Dokta Abdalla Uba Adamu ya yi bayani a game da yawaitar finafinai da yadda ake ganin su a idanun jama'a. Ga yadda ya ce a cikin wata makala da ya rubuta a cikin jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo 18/2/2002:
 “Babu inda wannan zargi ya fi karfi illa harkar cinikayyar shakatawa, tun ma ba ta hanyar samar da finafinai ba. Babbar illa a zamantakewar dan’adam ita ce, nuna yamutsawar jinsin maza da mata, kamar ta hanyar jima'i. Sa'annan sai taratsi ta hanyar kashe-kashe da kuma sace-sace da shan kwayoyi iri-iri. Wadannan duk ana ganin cewa abubuwan yau da kullum ne a rayuwar Amurukawa, saboda hak babu mamaki idan suka dinga fitar da su a finafinansu. A dalilin haka ne wannan tunani ya ci gaba da nuna babu dokar Allah da ta dattaku a kasar Amuruka, kowa yadda ya ga dama yake”
   Baya ga wadanan abubuwa da suka gabata da ake ganin su ne ya sa ka-ce-na-ce ya yawaita a kan finaninan Hausa, akwai wadansu da masana Adabin Hausa ke korafi a kansu domin kasancewarsu sun saba wa al'adun Hausawa. A cikin makalarsa ga mujallar Rana fitowa ta 79 mai taken “Waka A Finafinan Hausa Kayan aro Isa Sanusi cewa ya yi:

“Amma lokacin da finafinan Hausa suka fito da salon sirka wakoki a finafinasu sai aka yi ta ka-ce-na-ce. Wasu ma har suka ce yin hakan shiririta ne, dalilinsu kuwa shi ne abin bai dace da dabi’u da kuma al'adun Hausawa ba. Wannan haka yake domin duk wanda ya kalli irin wadannan wakoki a finafinan Hausa zai ga abin sam ba tsari, ya yi bambarakwai, kai ka ce an yi haka ne. domin basira ta toshe.…”. A lokacin da aka fara wannan salo abin ban haushi, abin dariya. Domin za ka ga kato da budurwa suna zagawa da fulawa suna cirar fure, suna rausayawa da kuma rangwada. Abin har ya kan fita daga kan jama'a....”.

     Wannan marubuci har wayau, ya fadi korafe-korafen jinsunan jama'a a game da finanfinai. Wannan a cikin makalarsa da ke cikin mujallar Rana fitowa ta 77, mai taken: FINAFINAN HAUSA INA AKA DOSA? Wannan kamar yadda iyaye ke ganin ana son a lalata musu tarbiyyar 'ya'ya ne da wadannan finafinan. Haka kuma akwai korafi na malaman addin da ke ganin akwai lokuta da sau da yawa akan siffanta malamai da bokaye da tsibbace-tsibbace. Haka akwai masu yawaita kawo ayoyin Alkur'ani a gurbace.
     Haka har wa yau wani marubucin ya nananta abin da mutane ke korafi a kansa a game da finafinai. Wannan marubucin kuwa shi ne Abubakar Sadik Yusuf Kano, a cikin makalarsa da ke cikin jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo ta ranar 6/9/2001. Ga abin da yake fada:
 “Duk wanda ke biye da shirye-shiryen finafinan Hausa, ba zai yiwu ya rasa ganin wani abu da ya mamaye finafanan ba, wanda za a iya cewa ya shafi ainihin jigogi, ko kuma sakwannin da ke cikin finafinan. Wannan abu bai wuce yadda samari da 'yanmata ke wage bakuna suna wake-wake da raye-raye kamar Indiyawa. Ba wani fim a halin yanzu da za ka ga an shigar da shi kasuwa, ba tare da wadansu wakoki ba, ko dai a tsakanin budurwa da saurayi, ko tsakanin miji da mata, ko makamatan haka. Masu shirya wadannan finafinan, suna masu ra’ayin yin haka saboda dalilai da suka hada da: 
  Abin da yawancin masu kallo ke bukata ke nan.
  Yana taimakawa wajen cika kaset da sauri.
  Suna inganta wake-waken Hausa da kayan kidan zamani.
     wannan na iya zama gaskiya ganin cewa yanzu yara kanana ko'ina ka je za ka gan su; ko ka ji suna ta famar rera wakokin finafinan, kamar na su Sangaya, Mujadala, Nagari da sauransu. Su kuwa manya za ka ji suna sauraren kasakasn wakokin, ko dai a gidaje; ko a shaguna; ko kuma a cikin motaci”.
 Marubucin har wa yau ya ambata ciwa, Gwamnati Jahar Kano ta kafa Haukuma da ta dora wa alhakin tace finafinai wadda ta haramta sa waka da kida a cikin finafinan, saboda sun saba wa al'adun Hausawa, a ga mace da namiji sun turke suna ta rera waka da 'yan tsalle-tsalle. Ya ce, shugaban hukumar ya nuna damuwrsa kwarai ga yadda ake gwamutsa maza da mata suna tikar rawa.
    Idan muka lura da duk wadannan ka-ce-na-ce da ake ta gudanarwa a kan wadannan finafinai. Za mu ga cewa, an tsangwami al'amuransu a dalilin wadannan abubuwa da ke biye:
  Haduwar maza da mata
  Lalata tarbiyyar yara da samari kamar yadda yake a cikin   wadansu finafinai ta hanyar koyon sata, ko fashi da makami, da kuma shan miyagun kwayoyi.
  Batanci ga addini, ta gurbata ayoyi, da siffanta malaman    addini da mummunar siffa.
  Kawo bakin al'adu da rosa na al'umma da ke akwai.
 5. MENE NE MAFITA?
    Ta duba ga wannan al'amari, ya zama abin da aka sani a harshen addini da sunan AMMATIL BALWA.

Ma'ana wani abu da ya game al'umma ya zama musiba wanda yake da wuya wani ya kubuta daga bala'insa. Ganin haka ne ya sa wadansu na ganin hana finafinan kwata-kwata. Wadansu kuwa na ganin a tsabtace su. Daga cikin wadanda ke ganin a tsabtace su akwai Danjuma Katsina a cikin wata makala da ya rubuta a cikin Jaridar Gaskiya Tafi Kwabo ta 8/3/2002 mai taken: Bidiyon Kasuwar Kano! Martani ga Ibrahim Malumfashi. Shi wannan marubuci ya yi maganganu wadanda akwai abin dubawa a ciki. Daga cikin abin da ya rubuta akwai cewa, ko da an hana wadannan kasusuwa a Arewa ana iya zuwa Kudu a sawo, kuma a shigo da su. Kai ana ma iya zuwa wadansu kasashe a sawo, kuma a shigo da su. A dalilin haka yana ganin mafita ita ce a tsaya a gyara finafinan na gida, yadda za su kori na waje marasa kyau. Daga cikin shawarwarin da ya bayar akwai:

  Marubuta su yo ca ga duk wani fim marar kyau, su kuma rika fito-na-fito da duk wasu halaye munana da ya kamata masu shirya finafinai su guji aikatawa.
  Masu kallo su kaurace wa duk wani fim maras ma'ana da kuma kamfanin da ya shirya shi.
  Gwammnatoci da masu kudi na iya fitowa da gidauniya wadda za a rika daukar nauyin yin finafinai masu kyau da kuma yada su.
  Idan muka dubi wadannan shawarwari na Danjuma, za mu ga suna da kyau, tun ma ba a ce shawara ta karshe ba. Domin abin da Hausawa ke cewa “Rashin uwa ke sa a yi uwar daki”. A nan da mawadatanmu da kuma Gwamnatoci za su karbi wannan shawara a samar da finafinai da suka dace da addininmu da al'adunmu, to, da ba a kallaci marasa kyau ba.
    A nan akwai wata shawara da ake iya dubawa ga wadancan hudu na sama. Wannan kuwa ita ce samar da hukuma mai karfi da za ta fito da dokokin yin fim a kan dacewarsa da addininmu da kuma al'adunmu. Domin wannan ko a Turai akwai wadannan dokoki. Alal misali an fara kafa dokokin fim a kasar Amuruka, da aka shata sharudan fitar da fim tun a shekara ta 1915. Daga cikin sharudan akwai, mutunci da dattaku da sanin ya kamata. Wannan an ce kuma su da kansu masu fitar da fim suka kafa wadannan dokoki kafin Gwamnati ta kafa nata. Haka kuma su sun shata ga finafinan da manya ke kallo da wadanda yaro ke kallo da sauransu. Amma mu a nan a namu yanayi za mu yi abin da ya dace.
KAMMALAWA
    Wannan kammalawa ta kasance ne a kan matsayar shari'a ga finafinai. Abu ne sananne cewa finafinai ba su bayyana ba a zamanin Manzo tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma ba su bayyana ba a zamanin sahabbai ba; haka kuma azamanin tabi'ai ballantana a ce sun yi magana a kansu. Amma da yake shari’ar Musulunci tsari ce na duniya gaba daya, kuma na har abada takan ba da dokoki da ka'idoji na gaba-daya domin su yi mana jagora. Ta haka ne wani daga cikin mashuran malamai na duniya ya wallafa littafinsa mai suna “Hukuncin Musulunci A Kan Kafofin Watsa Labari”. Wannan malami shi ne Abdullahi Nasiru Ulwana mutumen Siriya wanda ya rayu a kasar Sa'udiyya. Ya nuna cewa idan wasar kwaikwayo ta kunshi abubuwa shida ya halatta a yi kuma a kallace ta. Ga abubuwan a takaice:
  Kada a yi kwaikwayon wani ko wasu mutane masu daraja da tsarki a zukatan al'umma kamar Annabawa da halifofi shiryayyu.
  Kada ya kasance akwai alfasha, ko giya ko kuwa abubuwan gabatarwa na jima'i, kamar sumba da sauransu.
  Kada ya zama akwai cudanyar maza da mata.
  Ya kasance manufar wasar maslaha ce ta addini da ilimi da dabi'u na gari.
  Kada wasar kwaikwayo ta zama manufarta yi wa wani tsari na wajen aiki wanda yake manufarsa rosa al'umma.
  Ya kasance marubuta wasar ta kwaikwayo mutane ne na kirki masu tsoron Allah.
     Da wannan kuwa zan dakata da fatar Allah Ya ba mu ikon gyarawa. Amin.
    Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai.

MANAZARTA

  Almufassal Fil Adabil Arabi, Juzu'i na daya Aliyyul-Jarma da ‘yan'uwansa).
  Al’islam Walfannu (Malam Yusuf Alkanawi).
  Infakul Maisur(Sarkin Musulmi Bello).
  Hukumul Islam Fi Wasa’lil Ilam (Abdullahi Nasihu Ulwan).
  Hausa A Rubuce (Farfesa Ibrahim Y. Yahaya).
  Littafan Soyayya A Ma'aunin Hankali Da Shari'a (Muhammad Mujtaba Abubakar).
  Mujallar Rana Fitowa ta 76 da ta 77 da 79.
  Gaskiya Ta Fi Kwabo ta ranar 6-9-2001.
  Gaskiya Ta Fi Kwabo ta ranar 8-3-2001.
  Gaskiya Ta Fi Kwabo ta ranar 15-2-2001.
  Gaskiya Ta Fi Kwabo ta ranar 22-2-2001.

Koma Shafin Mujalla

Koma Babban Shafi