Ado Ibrahim
Ado Ibrahim | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 7 ga Faburairu, 1929 |
ƙasa | Najeriya |
Mutuwa | Jaguar Abuja, 29 Oktoba 2023 |
Karatu | |
Makaranta |
London School of Economics and Political Science Department of Economics (en) Makarantar Kasuwanci ta Harvard. |
Sana'a | |
Imani | |
Addini | Musulunci |
AbdulRahman Ado Ibrahim (An haife shi ranar 7 ga watan Fabrairu, 1929- 29 Oktoba 2023).[1][2][3] Shi ne sarkin gargajiya na huɗu, kuma a halin yanzu yana a matsayin sarkin masarautar Ebiraland,[4][5][6] jiha ce ta gargajiya mai hedikwata a Okene, Jihar Kogi da ke yankin, Middle Belt, Najeriya. Shi ɗa ne ga attah na biyu (yanzu "ohinoyi") na Ebiraland, Ibrahim Onoruoiza, na dangin Omadivi, wanda ya yi sarauta a shekara ta 1917 zuwa 1954.[5][7]
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Ibrahim ranar 7 ga watan Fabrairu, 1929. Ya halarci makarantun western nursery da na Al-Qur'ani, sannan ya kammala karatunsa na firamare a shekarar 1940 a makarantar (Native Authority (NA))) da ke Okene, Jihar Arewa (yanzu jihar Kogi ). Ya fara karatunsa na sakandare a Ondo Boys High School daga baya ya koma kwalejin Oduduwa, inda ya kammala a shekarar 1949. A 1954, ya sami digiri na farko a fannin tattalin arziki daga Makarantar Tattalin Arziki ta London da kuma digiri na biyu daga Makarantar Kasuwancin Harvard a 1959.[1]
Sarauta
[gyara sashe | gyara masomin]Bayan rasuwar Ohinoyi Sanni Omolori na ƙabilar Ogu a shekarar 1997,[5] ɗan kasuwa mazaunin birnin Legas kuma ɗan sarkin Ebiraland na biyu, AbdulRahman Ado Ibrahim, ya hau gadon sarautar Okene a matsayin ohinoyi na biyu ko kuma na huɗu basaraken gargajiya mai zaman kansa a Ebiraland ranar 2 ga watan Yuni, 1997.[1][7][5]
Ibrahim ya gina fadar Azad, mai sunan ɗaya daga cikin ƴaƴansa, wanda ɗan aka ce yana cikin mafi kyau-(kyakkyawa) a yammacin Afirka.[1]
Takun saka da gwamnatin jihar
[gyara sashe | gyara masomin]Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin jihar Kogi ce ta yi wa Ibrahim wata tambaya, biyo bayan gazawarsa wajen yiwa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tarba a ziyarar da ya kai jihar a ranar 29 ga watan Disamban shekarar 2022.[8][9][10][11] An bayyana cewa bam ne ya tashi a lokacin ziyarar shugaban a wani masallaci da ke kusa da fadar ohinoyi a Okene, inda ya kashe mutane kusan uku.[12][13][14][15] A ranar 3 ga watan Junairu, 2023, hukumar ƴan sandan Najeriya DSS ta ce ta damke maharan da suka kai harin bam ɗin waɗanda mamba ne na ƙungiyar ISWAP, wadda ta fitar da wani faifan bidiyo kwana guda kafin a kama su, inda aka ce "soldiers of the caliphate" ke da alhakin kai harin.[16] Ibrahim a martanin da ya bayar a kan tambayar a ranar 12 ga watan Janairu, 2022, wanda ya aika wa kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu na jihar, ya bayyana cewa bai samu sanarwa a hukumance ba, kuma bai san da gina wata fada ba, wadda tana cikin ayyukan da za a yi da shugaban ƙasa ya ba shi aiki, banda cikin fadar da ya ke zaune tun hawansa mulki a shekarar 1997. Bugu da ƙari, ya bayyana cewa a lokacin da yake shirin tafiya ganawa da shugaban ƙasar, bam ɗin ya faru, kuma kofar fadarsa ta yi masa katanga, wanda hakan ya sa ya kasa fita wajen ganawa da shugaban kafin daga bisani ya tafi Lokoja.[17]
Tun da farko a watan Disamba 2022, Ibrahim ya bayyana goyon bayan sa ga Natasha Akpoti-Uduaghan na jam'iyyar PDP mai neman kujerar Sanatan Kogi ta Tsakiya.[18] Abin lura shi ne, gwamnatin jihar a wancan lokacin kuma a halin yanzu tana karkashin jam’iyyar adawa ta APC.
Gidan sarauta
[gyara sashe | gyara masomin]Ɗaya daga cikin ƴaƴan Ibrahim, Ya zuwa ranar 7 ga watan Janairu, 2023, Yarima Malik Ado-Ibrahim, ya kasance ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Young Progressives Party (YPP) a zaɓen da ke tafe a Najeriya.[14][19]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 1.2 1.3 Ojeifo, Sufuyan (February 7, 2019). "Ado Ibrahim @90: Humanist, Royal Icon For All Seasons". Tribune Online Nigeria. Retrieved January 9, 2023.
- ↑ "Ado Ibrahim 90 Still a Humanist Royal Icon for All Seasons". TheWill Nigeria. February 7, 2019. Retrieved January 9, 2023.
- ↑ Omotayo, Joseph (November 4, 2021). "5 of the Oldest Kings in Nigeria and Their Ages, One Is Over 90 Years Old". Legit Nigeria. Retrieved January 9, 2023.
- ↑ Otu, M.M. (1997). New Ohinoyi Ebira and Pax Ebirana (in English). BOTCOM Enterprises. ISBN 9789783303744. Retrieved January 9, 2023.CS1 maint: unrecognized language (link)
- ↑ 5.0 5.1 5.2 5.3 Ajanah, Nuhuman (1997). Ebiras at a Glance. 2. Nigeria: Numa. p. 37.
- ↑ Ajanah, Nuhuman (1996). Ebira Vacant Stool: Dr. Amezigi Ayamuku Drops Rotation for Ogu Clan for Ohinoyi and Governor for Omavi Clan (in English). Ebira Tao Social Club. Retrieved January 9, 2023.CS1 maint: unrecognized language (link)
- ↑ 7.0 7.1 Hogan, Edmund M. (2011). Berengario Cermenati Among the Igbirra (Ebira) of Nigeria: A Study in colonial, missionary and local politics, 1897-1925. HEBN Publishers Plc. p. 202. ISBN 978-978-081-182-2. Retrieved January 9, 2023.
- ↑ Boluwaji, Obahopo (January 7, 2023). "Kogi queries top monarch for 'refusing' to welcome Buhari". Lokoja: Vanguard Nigeria. Retrieved January 9, 2023.
- ↑ Jimoh, Yekini (January 7, 2023). "Presidential Visit: Gov Bello Queries Ado Ibrahim, May Set Up Panel". Lokoja: Tribune Online Nigeria. Retrieved January 9, 2023.
- ↑ "Kogi govt queries monarch, Ado Ibrahim, over refusal to welcome Buhari". Ripples Nigeria. January 7, 2023. Retrieved January 9, 2023.
- ↑ "Gwamnan Kogi na tuhumar Sarki Ohinoyi na Ebira bisa ƙin zuwa tarbar Buhari". Daily Nigerian. January 8, 2023. Retrieved January 9, 2023.
- ↑ "BREAKING: At Least 3 Dead As Bomb Blast Rocks Palace Of Prominent Kogi Monarch Ahead Of Buhari's Visit". Sahara Reporters. December 29, 2022. Retrieved January 9, 2023.
- ↑ "The Many Lies of Kogi's Information Commissioner". This Day Live. January 8, 2023. Retrieved January 9, 2023.
- ↑ 14.0 14.1 Tyohemba, Henry. "Kogi Explosion: Ado-Ibrahim Insists On Probe". Leadership News Nigeria. Retrieved January 9, 2023.
- ↑ Uthman, Samad (January 8, 2023). "Buni declares two-day holiday to welcome Buhari for inauguration of projects". The Cable Nigeria. Retrieved January 9, 2023.
- ↑ "Nigeria Secret Police, DSS Arrests ISWAP Leaders Over Kogi Bomb Blast During President Buhari's Visit". Sahara Reporters. January 4, 2023. Retrieved January 9, 2023.
- ↑ "BREAKING: Prominent Monarch For Ebiraland, Ohinoyi Replies Kogi Government's Query, Says Allegations Unfair To His Age, Experience, Royal Dignity". Sahara Reporters. 12 January 2023. Retrieved January 12, 2023.
- ↑ Oluokun, Ayotunde (5 December 2022). "Kogi Central: Natasha takes campaign to palace of Ohinoyi of Ebiraland". PM News Nigeria. Retrieved 12 January 2023.
- ↑ AbdulKareem, Mumini (December 25, 2022). "YPP: Kogi Prince's Quest To Defeat Tinubu, Atiku, Others". Ilorin: Daily Trust. Retrieved January 9, 2023.
Hanyoyin haɗi na waje
[gyara sashe | gyara masomin]Ado Ibrahim Omadivi royal house Born: February 7, 1929
| ||
Regnal titles | ||
---|---|---|
Magabata {{{before}}} |
{{{title}}} | Magaji {{{after}}} |