Arewa ta Gabas (Najeriya)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Arewa ta Gabas (Najeriya)
geopolitical zone of Nigeria (en) Fassara
Bayanai
Ƙasa Najeriya
Wuri
Map
 11°22′N 11°46′E / 11.36°N 11.76°E / 11.36; 11.76

Arewa ta gabas (wanda aka fi sani da Arewa maso Gabas ) na daya daga cikin shiyyoyin siyasa shida na Najeriya dake wakiltar yankin kasa da kuma yankin siyasan arewa maso gabashin kasar. Ta ƙunshi jihohi shida – Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba, da Yobe .

Ta fuskar yanayin kasa, Arewa ta Gabas ita ce shiyyar siyasa mafi girma a yankunan kasar, wanda ya mamaye kusan kashi daya bisa uku na daukacin fadin Najeriya. Dangane da mahalli, an raba yankin da farko tsakanin yankin sahel na hamadar sahel da kuma yankin savanna na yammacin Sudan .

Yankin yana da yawan mutane kusan miliyan 26, kusan kashi 12% na yawan al'ummar ƙasar. Maiduguri da Bauchi su ne biranen da suka fi yawan jama'a a yankin Arewa maso Gabas kuma itace ta goma sha biyar kuma na goma sha bakwai mafi yawan jama'a a Najeriya. Sauran manyan garuruwan arewa maso gabas sun hada da (bisa ga yawan jama'a) Bauchi, Yola, Mubi, Gombe, Jimeta, Potiskum, Jalingo, Gashua, da Bama .

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

Labarai da dumi-duminsu daga Arewa maso Gabashin Najeriya a NortheastReporters.com Archived 2022-09-05 at the Wayback Machine