Fati Nijar

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Fati Niger
Ɗan Adam
Bayanai
Jinsi mace
Ƙasar asali Nijar
Suna Binta (en) Fassara
Sunan dangi Niger
Wurin haihuwa Maradi
Harsuna Hausa
Sana'a mawaƙi da Jarumi
Work period (start) (en) Fassara 2004

Binta Labaran (wacce aka fi sani da Fati Nijar) ƴar ƙasar Nijar mawaƙiya ce kuma jarumar da ta samu laƙabin "Gimbiyar Mawaƙan Hausa" (wanda aka fassara zuwa "Princess of Hausa Music " ). An haife ta kuma ta girma a garin Maraɗi na ƙasar Nijar inda kuma ta yi karatun Al-Qur'ani kafin ta wuce Najeriya don ci gaba da sana'ar waƙa. Fati Nijar ta fito da albam 4 masu waƙoƙi sama da 500. Ita ‘yar ƙabilar Hausa ce.[1][2][3]

Rayuwar farko da aiki[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Fati Nijar kuma ta girma a Maraɗi, Nijar. Ta kasance tana da sha’awar rera waƙa musamman waƙoƙin Hausa na gargajiya waɗanda galibi ake rera su a cikin daren wata a tsakanin matasa a ƙauyukan Hausa.

Bayan ta ziyarci 'yar uwarta a shekarar 2004 a Najeriya, ta gano masana'antar waƙa da ta bunƙasa a cikin birnin Kano. A nan ta nemi shawarar yayarta da yardarta kafin ta ɗauki wakar ta ta farko a ɗakin taro na Ali Baba da ke cikin birnin Kano.[4]

Waƙa[gyara sashe | gyara masomin]

Fati ta fitar da kundin waƙa 4 da kuma waƙoƙi sama da 500. Ta kuma fito a fina-finan Hausa na Kannywood daban-daban.[5][6]

Waƙoƙi[gyara sashe | gyara masomin]

Fati Nijar, ta yi fice a waƙoƙin fim masu yawan gaske, dama na siyasa gami da bukukuwa. To amma waƙar ta ta ‘Girma-Girma’, ta ɗaga darajar ta inda ta shahara kuma aka santa a duniya.[7]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://www.blueprint.ng/why-im-still-single-fati-niger/
  2. https://dailytrust.com/fati-niger-an-exotic-songbird-from-niger-rep/
  3. https://dailytrust.com/5-kannywood-divas-that-are-not-nigerians/
  4. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-05-18. Retrieved 2023-03-08.
  5. https://www.bbc.com/hausa/labarai-51531594.amp
  6. https://www.afro.who.int/news/who-partners-fati-niger-popular-nigerian-based-singer-create-awareness-cholera-meningitis-and
  7. https://fimmagazine.com/fati-nijar-buri-na-in-sha-gaban-duk-wata-jaruma/