Habu Daura
Habu Daura | |
---|---|
mutum | |
Bayanai | |
Jinsi | namiji |
Ƙasar asali | Najeriya |
Yaren haihuwa | Hausa |
Harsuna | Turanci, Harshen Ijaw, Hausa da Pidgin na Najeriya |
Writing language (en) | Turanci |
Sana'a | ɗan siyasa |
Muƙamin da ya riƙe | Gwamnan Jihar Bayelsa |
Ƙabila | Hausawa |
Habu Daura shine kwamishinan ƴan sanda ya kasance shugaban riƙo na jihar Bayelsa dake Najeriya yana riƙe da muƙamin Kwamishinan Yan sanda daga watan Fabrairu zuwa watan Yuni shekara ta 1997 a lokacin mulkin soja na Janar Sani Abacha.[1][2] A cikin shekarar 1999, Nuhu Ribaɗu, wanda a lokacin jami’in shari’a ne a hukumar ƴan sanda ta hukumar leƙen asiri da bincike, ya bayar da shawarar a gurfanar da Daura a gaban kuliya bisa zarginsa da hana gudanar da bincike kan laifukan fashi da makami a shekarar 1999. Daura ya yi ritaya daga aikin ƴan sanda.[3]
Shugaba Umaru Ƴar'adua ya naɗa Daura a matsayin ma'aikacin hukumar ƴan sanda (PSC) a cikin shekarar 2008 a matsayin mamba na dindindin.[3][4] Nuhu Ribaɗu wanda shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya naɗa shugaban hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa, sannan kuma Ƴar’aduwa ya kore shi, ya bayyana Daura a matsayin wanda bai cancanta ba kuma bai dace ba, yana mai nuni da shawarar da ya bayar tun farko a gurfanar da Daura.[5] A kwanakin baya ne dai hukumar ta PSC ta sauke Ribaɗu daga muƙamin mataimakin sufeto-Janar na ƴan sanda zuwa mataimakin kwamishinan ƴan sanda.[6]
Daura ya jagoranci tawagar PSC masu sa ido a zaɓen watan Fabrairun shekara ta 2010 a jihar Anambra. Rahoton nasa ya ce ƴan sandan sun nuna hali mai kyau, amma an cire akwatunan zaɓe a wasu rumfunan zaɓe a lokacin.[7]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://web.archive.org/web/20110724143253/http://www.bayelsa.gov.ng/new/index.php?option=com_content&view=article&id=109:bayelsa-state&catid=47:the-state&Itemid=111#
- ↑ https://www.worldstatesmen.org/Nigeria_federal_states.htm
- ↑ 3.0 3.1 https://web.archive.org/web/20100419071249/http://www.noprin.org/policenews.html#
- ↑ https://web.archive.org/web/20100824075407/http://www.psc.gov.ng/node/133
- ↑ https://odili.net/news/source/2008/oct/30/800.html[permanent dead link]
- ↑ https://allafrica.com/stories/200810300953.html
- ↑ https://allafrica.com/stories/201002080616.html