Jump to content

Harris Eghagha

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Harris Eghagha
Gwamnan jahar ogun

ga Yuli, 1978 - Oktoba 1979
Saidu Ayodele Balogun - Olabisi Onabanjo
Rayuwa
Haihuwa Okpe, 8 ga Maris, 1934
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Urhobo (en) Fassara
Mutuwa 19 ga Maris, 2009
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da hafsa
Digiri Janar

Birgediya Janar Harris Otadafevwerha Deodemise Eghagha (An haife shi a ranar 8 ga Maris, 1934). An nada shi gwamnan soja a jihar Ogun, Najeriya daga watan Yuli a shekarar 1978 zuwa watan Oktoban 1979 a lokacin mulkin soja na Janar Olusegun Obasanjo, inda ya mika mulki ga zababben gwamna Olabisi Onabanjo a farkon watan Oktoba. Jamhuriyar Najeriya ta Biyu.[1]

An haifi Eghagha a ranar 8 ga Maris, 1934 a Mereje, karamar hukumar Okpe, Urhoboland, jihar Delta .

Eghagha ya taka rawa kadan a juyin mulkin watan Janairun 1966 wanda aka hambarar da jamhuriya ta farko a Najeriya kuma ya Haifar da mulkin soja na Manjo-Janar Johnson Aguiyi-Ironsi [2] a matsayin Lieutenant na biyu mai kula da shinkan gen hanya a Kaduna.

Gwamana Jihar Ogun

[gyara sashe | gyara masomin]

An nada shi gwamnan soja a jihar Ogun, Najeriya a Ranar Yuli, 1978 zuwa Oktoban 1979. Yasamu Nasarorin da ya samu a lokacin dayake gwamnan jihar Ogunsun hada da gina rukunin majalisa da hanyoyin sadarwa a Abeokuta, babban birnin jihar. Ya gina tare da kaddamar da Otal din Jihar Ogun, Abeokuta, ya kafa masana’antu a fadin jihar sannan ya kafa Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Ogun (yanzu Moshood Abiola Polytechnic ) a Abeokuta. Ya kuma rike mukaddashin Gwamnan Jahohin Sokoto da Kwara, kuma ya kasance Babban Kwamishinan Najeriya a Ghana.

Birgediya Janar Har[3]ris Eghagha ya rasu a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Legas a ranar 19 ga Maris, 2009 yana da shekaru 75.

  1. https://military-history.fandom.com/wiki/Harris_Eghagha
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-06-15. Retrieved 2022-06-15.
  3. https://archive.ogunstate.gov.ng/public/ogun-state/governors/harris-eghagha[permanent dead link]