Kashim Ibrahim
Kashim Ibrahim | |||
---|---|---|---|
| |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Maiduguri, 10 ga Yuni, 1910 | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Mutuwa | 25 ga Yuli, 1990 | ||
Karatu | |||
Harsuna |
Hausa Turanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa da Malami | ||
Kyaututtuka | |||
Imani | |||
Addini | Musulunci | ||
Jam'iyar siyasa | Majalisar Jama'ar Arewa |
Kashim Ibrahim (Shettima) (an haife shi 10 ga watan Yuni a shekara ta 1910 zuwa 25 ga watan Yuli shekara ta 1990)[1] mutumin Kanuri ne kuma ɗan siyasa, ya riƙe shugabancin gargajiya a masarautar huhar Borno kuma minista ne na ayyukan jama'a a Nijeriya a shekarun 1950s. Yazama Waziri a Masarautar Borno bayan korar Wazirai biyu da akayi sakamakon zarginsu da akeyi akan yadda suke gudanar da ayyuka a masarautar ta jihar Borno. Yakasance na hannun daman Sardauna wato firimiya Ahmadu Bello.[2]
Rayuwarsa
[gyara sashe | gyara masomin]An haife Ibrahim a garin mazabar Gargar, Yerwa daga gidan Ibrahim Lakanmi.[3] Yafara karatun sa da koyon larabci da Quran kafin yaje Borno Provincial School a shekara ta 1922. A kuma shekarar 1925, Yasamu shiga Kwalejin Horo ta jihar Katsina inda ya kammala karatun sa da sakamakon malunta a shekara ta 1929. Ya fara aiki a matsayin Malami a shekarar 1929 a jihar Borno Middle School sannan daga shekara ta 1933, yazamanto Provincial Visiting Teacher. Inda daga bisani akai masa Karin girma yakaiga matsayin Senior Visiting Teacher and education officer for the province of Borno. An bashi sarautar Shettiman Borno a shekarar 1935 daga nan ne akasansa da Shettima Kashim. Ya shiga siyasa a shekarar 1951 zuwa 1952, sanda aka zabesa zuwa majilisar arewacin Najeriya (Northern Regional Assembly), An zabe shi daga Arewa a matsayin zababben majalisar ministoci. Daga nanne aka zabeshi a matsayin ministan tarayya na Ayyukan Jama'a bayan nan kukuma yazama ministan Ilimi.
A shekarar 1956, Shehun Borno yanada shi Wazirin Borno.[4] Waziri Ibrahim yazama Gwamnan yankin Arewacin Najeriya a shekarar 1962, yacigaba da mulkinsa har saida akayi juyin mulkin soji a ranar 16 ga watan Janairun shekara ta 1966, wanda takawo mulkin Manjo General Johnson Aguiyi-Ironsi.[5] An nadashi CBE a shekarar 1960 kuma wanda yanadashi shine KCMG a shekarar 1962.[6]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Ibrahim, Sir Kashim", in Christopher Osadiaye Orumwese Ugowe, Eminent Nigerians of the twentieth century, Hugo Books, 2000, p. 155.
- ↑ Ahmadu Bello, My Life, Cambridge University Press, 1962, p. 31.
- ↑ "The Settlement of 1960: Who was Who" (PDF). Sati Fwatshak and Philip Ostien. Retrieved 2015-08-28.
- ↑ Rosalynde Ainslie, Catherine Hoskyns, Ronald Segal. Political Africa: A Who's Who of Personalities and Parties, New York: Frederick A. Praeger, 1961, p. 128.
- ↑ "Provinces and Regions of Nigeria". WorldStatesmen. Retrieved 2010-05-28.
- ↑ Oxford Dictionary of National Biography