Ken Saro-Wiwa
Ken Saro-Wiwa | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Bori da Niger Delta, 10 Oktoba 1941 |
ƙasa | Najeriya |
Harshen uwa |
Khana (en) Harshen, Ibo Khana |
Mutuwa | Port Harcourt, 10 Nuwamba, 1995 |
Makwanci | Port Harcourt Cemetery |
Yanayin mutuwa | hukuncin kisa (rataya) |
Ƴan uwa | |
Mahaifi | Jim Wiwa |
Yara |
view
|
Karatu | |
Makaranta |
Jami'ar Ibadan Kwalejin Gwamnati Umuahia |
Harsuna |
Turanci Khana (en) Pidgin na Najeriya Harshen, Ibo |
Sana'a | |
Sana'a | marubuci, maiwaƙe, marubin wasannin kwaykwayo, gwagwarmaya, environmentalist (en) da mai tsare-tsaren gidan talabijin |
Employers | Jami'ar jahar Lagos |
Muhimman ayyuka |
Basi and Company (en) A Bride For Mr B (en) |
Kyaututtuka | |
Mamba | Movement for the Survival of the Ogoni People (en) |
Fafutuka | environmentalism (en) |
IMDb | nm3167978 |
Kenule Beeson "Ken" Saro-Wiwa (an haife shshi a ranar 10 ga watan Oktoba 1941 - 10 Nuwamba 1995)[1] ya kasance marubuci ɗan Nijeriya, mai gabatar da shirye-shiryen talabijin, mai rajin kare muhalli, kuma ya ci kyautar ''Kyauta ta Rayuwa'' jajirtacce kuma abin misali wajen yin gwagwarmaya ba ta tashin hankali ba don farar hula, tattalin arziƙi da muhalli haƙƙoƙi da kuma Kyautar Muhalli ta Goldman.[2] Saro-Wiwa ya kasance memba ne na mutanen Ogoni, kabilu marasa rinjaye a Najeriya wadanda asalin garinsu, Ogoniland, a yankin Neja Delta an yi niyyar hako danyen mai tun daga shekarun 1950 wanda ya gamu da mummunar illa ta muhalli daga shekaru da dama na zubar da dattin man fetur ba tare da ƙa'ida ba.[3]Tun da farko a matsayin kakakin ƙungiya sannan kuma a matsayin shugaba na Movement for the Survival of the Ogoni People (MOSOP), Saro-Wiwa ya jagoranci kamfen ne na nuna adawa da lalata muhalli na kasa da ruwan Ogoni da ayyukan kamfanonin mai na kasa da kasa, musamman ma kamfanin Royal Dutch Shell.[4] Ya kuma kasance mai sukar lamirin gwamnatin Nijeriya, wanda ya ke kallo a matsayin mara son aiwatar da dokokin muhalli a kan kamfanonin man fetur na kasashen waje da ke aiki a yankin.[5]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Ken Saro-Wiwa | Nigerian author and activist | Britannica" . www.britannica.com . Retrieved 28 February 2022.
- ↑ "Ken Saro-Wiwa" . Encyclopedia Britannica. 6 November 2020. Archived from the original on 1 June 2021. Retrieved 19 July 2021.
- ↑ Refugees, United Nations High Commissioner for. "Refworld | Nigeria: Information on the Ogoni people including where they live, names of towns and villages, languages spoken and a detailed map of Ogoni areas" . Refworld . Retrieved 27 April 2023.
- ↑ "Ogoni 9 execution anniversary: Who be Ken Saro-Wiwa" . BBC News Pidgin (in Nigerian Pidgin). 11 November 2019. Retrieved 27 May 2020.
- ↑ "Ken Saro-Wiwa" . FantasticFiction . Archived from the original on 3 August 2020. Retrieved 27 May 2020.