Jump to content

Kungiyar Kiristocin Najeriya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kungiyar Kiristocin Najeriya
Bayanai
Iri umbrella organization (en) Fassara da Christian organization (en) Fassara
Ƙasa Najeriya
Harshen amfani Turanci
Tarihi
Ƙirƙira 1976

christianassociationofnigeria.org

Ƙungiyar kiristoci ta Najeriya a taƙaice (CAN)[1], ƙungiya ce mai jagorantar ɗaukacin mabiya addinin Kirista a Najeriya.

Fayil:Christian Association of Nigeria logo.JPG
Alamar tambari na Ƙungiyar

An kafa ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya a shekarar 1976, kuma asalinta tana kunshe da Cocin Katolika da ƙungiyoyin Protestant ne, kawai. Koyaya, daga baya ta faɗaɗa ta haɗe da majami'un Pentecostal.[2]

A shekara ta 2000, ƙungiyar CAN ta nuna rashin amincewa da tsarin shari'a a jihohin arewa.[3] A cikin watan Fabrairun 2006, yayin da shugaban ƙungiyar, Akinola ya fitar da wata sanarwa da ke mayar da martani game da cin zarafin da Musulmi ke yi wa Kiristoci, inda ya shaida wa Musulmi cewa ba su da wani “abin da ke da alaƙa da tashin hankali”. Washegari Kiristoci sun yi tarzoma domin ramuwar gayya ga musulmi, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 70.[4][5] Daga baya Akinola, ya yi iƙirarin cewa an yi wa kalaman nasa mummunar fassara a ƙafafen yaɗa labarai na yammacin duniya. Har ma ya yi barazanar yin murabus idan har aka ci gaba da tada tarzoma.[6]

An kashi mutane 630

[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar 2 ga watan Mayu, 2004, an kashe Kiristoci fiye da 630 a Yelwa, Najeriya. Waɗanda suka mutun an bayyana mamatan a matsayin ‘yan ƙungiyar CAN ne.[7] Kisan kiyashin ana tuna shi a matsayin; Kisan kiyashi a Yelwa.

A watan Satumbar 2007, ƙungiyar ta amince da wani shiri na zaman lafiya da Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido ya gabatar.[8]

Ƙungiyar ta kunshi kungiyoyi biyar; su ne Majalisar Kirista ta Najeriya, da Sakatariyar Katolika ta Najeriya, Pentecostal Fellowship of Nigeria, Organization of African Instituted Churches, da kuma Evangelical Church Winning All/Fellowship of Churches of Christ in Nigeria.[9]

Ƙungiyar ta CAN tana da Mata da Matasa, Majalisar Zartarwa ta kasa mai kunshe da mambobi 105 (wanda sune ke zaɓen shugaban ƙungiyar), da manyan mambobi a babban zauren taron majalisar su 304 (waɗanda aka tabbatar a matsayin shugabannin gudanar da zaɓen shugaban ƙungiyar).[9]

A cikin shekara ta 2016, Supo Ayokunle, Shugaba (kuma Babban Jami'in Gudanarwa) na Ƙungiyar Baptist ta Najeriya, an zaɓi shi a matsayin shugaban ƙungiyar ta kiristoci da kuma matsayin Farfesa. Joseph Otubu, na Cocin Motailatu Cherubim and Seraphim Movement, mataimakin shugaban ƙungiyar.

An sake zaɓen Ayokunle a karo na biyu kuma an gabatar da shi a watan Yulin 2019 tare da mataimakinsa Rev Dr. Caleb Ahima.[10] A cikin watan Yuli 2022, an zaɓi Daniel Okoh a matsayin shugaban ƙungiyar na yanzu-(mai ci).[11]

Oda Wa'adin ofishi Mulki Suna Wurin haihuwa Mabiyin ɗarikar.. Bayani
1 November 1988 - November 1995 Zango 2, 1992 Anthony Cardinal Okogie Lagos, Najeriya Roman Catholic Archbishop of Lagos
2 November 1995 - November 2003 Zango 2 1999 Sunday C. Mbang Akwa Ibom, Najeriya Methodist Prelate of the Methodist Church of Nigeria
3 November 2003 - June 2007 Zango 1 Peter Akinola Ogun, Najeriya Anglican Prelate, Anglican Church of Nigeria
4 June 2007 - July 2010 Zango 1 Archbishop John Onaiyekan Kabba, Nigeria Roman Catholic Archbishop of Abuja
5 July 2010 - July 2016 Zango 2, 2013[12][13] Ayo Oritsejafor Warri, Najeriya Pentecostal Pastor, Word of Life Bible Church
6 July 2016 – July 2022 Zango 2 [14] Supo Ayokunle Oyo Najeriya Baptist Shugaban, Nigerian Baptist Convention
7 July 2022 - zuwa yau... Kan ƙaragar mulki[15] Daniel Okoh Kano, Najeriya Pentecostal General Supretendent, Christ Holy Church International
  1. ‘CAN’ na nufin, (Christian Association of Nigeria) a turance kenan
  2. "Pentecostalism in Nigeria". PewForum.org. Pew Forum on Religion & Public Life. Archived from the original on 6 March 2008. Retrieved 13 September 2007.
  3. Minchakpu, Obed (2000). "Nigerian Churches will Challenge Islamic Law". Compass. Compass Direct News Service. Archived from the original on 11 September 2007. Retrieved 13 September 2007.
  4. "Christians kill Muslims following warning by Nigerian Archbishop". Ekklesia.co.uk. Ekklesia. 23 February 2006. Retrieved 13 September 2007.
  5. "God's Country". The Atlantic. 1 March 2008. Archived from the original on 14 May 2008. Retrieved 19 September 2009.
  6. "Reactions to violence in Nigeria: Archbishop Peter Akinola explains, Christianity Today". Archived from the original on 2019-07-09. Retrieved 2023-01-30.
  7. Eyewitness: Nigeria's 'town of death'
  8. Olawale, Taiwo (9 September 2007). "Sultan, CAN Laud Govt Over Security Policy". This Day via allAfrica.com. Leaders & Company Limited. Retrieved 13 September 2007.
  9. 9.0 9.1 "Onaiyekan is new CAN president". CBCN.org. Catholic Bishops Conference of Nigeria. 19 June 2007. Archived from the original on 20 July 2007. Retrieved 19 June 2007.
  10. Adeniyi, Olakunle (2019-07-19). "CAN inaugurates Ayokunle for second term presidency". Nigeria news (in Turanci). Archived from the original on 2020-11-26. Retrieved 2019-07-19.
  11. "Daniel Okoh emerges CAN president". The Guardian (in Turanci). 2022-07-27. Archived from the original on 2022-07-27. Retrieved 2022-07-27.
  12. "'CAN Officers'". Retrieved 2017-03-18.
  13. "CAN re-elects Oritsejafor as president. On July 10, 2013. He was first elected into the position in May 2010'". Vanguard News. 2014-10-28. Retrieved 2016-02-04.
  14. Press, Fellow (2019-06-19). "Ayokunle retains seat as CAN president". Nigeria news (in Turanci). Archived from the original on 2019-07-19. Retrieved 2019-07-19.
  15. Press, Fellow (2022-07-26). "Most Rev Daniel Okoh emerges CAN President". National daily (in Turanci). Retrieved 2022-07-26.

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]