Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
.
Leonardo da Vinci, an haife shi a Vinci (yanzu Italiya) a shekara ta alif 1452, ya mutu a Amboise (Faransa) a shekara ta alif 1519. Ya rayu a lokacin Renaissance. Ya kasance shahararren mai zane, injiniya, masanin kimiyya. Duk da cewa anfi sanin shi a matsayin mai zane, har ila yau ya shahara da ayyukansa na littafi, inda yake zane da rubuce rubuce akan abubuwa daban daban d suka shafi nazarin halittar dan Adam, taswira, labarin kasa da makamantansu.