Jump to content

Mustafa Ibn Umar El-Kanemi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mustafa Ibn Umar El-Kanemi
Rayuwa
Haihuwa Dikwa, 1924
ƙasa Najeriya
Mutuwa Kairo, 2009
Ƴan uwa
Mahaifi Umar Ibn Muhammad na Borno
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
Sana'a
Imani
Addini Musulunci

Shehu Mustafa Ibn Umar El-Kanemi (ɗan Shehu Umar Ibn Muhammad na Borno ) shi ne Shehun Borno daga shekarar alif 1974 zuwa 2009.[1][2]

An haifi Mustapha El-Kanemi a shekarar 1924, ɗa na hudu ga Shehun Borno na 17, Sir Umar ibn Mohammed El-Kanemi, kuma ya girma a Dikwa, jihar Borno. Ya zama sakataren Walin Borno a shekarar 1945, sannan ya yi aiki a sassa daban-daban na hukumar ta ƙasa a matsayin wakilin Shehu.[2] A shekarar alif 1952 ya halarci Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria inda ya karanci harkokin gwamnati.[3]

An zaɓi El-Kanemi a matsayin ɗan majalisar dokokin yankin Arewa a shekarar 1956, mai wakiltar mazaɓar Damaturu/Busari, sannan aka sake zaɓen sa a shekarar 1959. Ya kasance sakataren majalisa a yankin Arewa a lokacin jamhuriya ta farko ta Najeriya. Ya koma Maiduguri a shekarar 1966 kuma a shekarar 1970 ya zama hakimin gundumar. An naɗa shi Shehun Borno a shekarar 1974. A wani lokaci ya kasance mataimakin shugaban majalisar ƙoli ta harkokin addinin musulunci.[2] Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi na Borno daga dangin masarautar Dikwa ne ya gaje shi.[4]

  1. "Short biography of Mustafa Ibn Umar El-Kanemi of Borno". Archived from the original on 2012-04-25. Retrieved 2023-09-02.
  2. 2.0 2.1 2.2 "Mustapha Amin El-Kanemi (1924–2009)". ThisDay. 5 March 2009. Retrieved 8 September 2010.
  3. HOPE AFOKE ORIVRI (22 February 2009). "Shehu of Borno dies at 83". Nigerian Compass. Retrieved 8 September 2010.
  4. Naija Pundit (6 March 2009). "The intrigues, power play behind the emergence of new Shehu of Borno". The Guardian. UK. Archived from the original on 12 March 2011. Retrieved 8 September 2010.

Littafi Mai Tsarki

[gyara sashe | gyara masomin]
Mustafa Ibn Umar El-Kanemi
Regnal titles
Magabata
Umar Ibn Abubakar Garbai of Borno
13th Shehu of Borno
1974-2009
Magaji
Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi of Borno

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]