Sa'adu Abubakar

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Simpleicons Interface user-outline.svg Sa'adu Abubakar
Sa'adu Abubakar at meeting with John Kerry (29176258455).jpg
Rayuwa
Haihuwa Sokoto, ga Augusta, 24, 1956 (64 shekaru)
ƙasa Najeriya
Yan'uwa
Mahaifi Siddiq Abubakar III
Karatu
Sana'a
Sana'a soja
Digiri general officer (en) Fassara
Imani
Addini Musulunci


An haifi mai martaba Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'adu Abubakar III a 24 ga watan Augusta na shekara ta 1956 A sananniyar masarautar nan ta gidan sarkin musulmi dake Sakkwato a Arewacin Najeriya).

Shine kuma ke rike da mukamin shugaban kungiyar Musulmi ta Najeriya wato (Jama'atu Nasril Islam, (JNI)). Bayan sarautar kasar Sakkwato kuma shine shugaban sama da mutane miliyan saba'in na musulman Najeriya wadanda sune suke sama da rabin mutanen Najeriya. Mai martaba Sa'adu Abubakar ya hau karagar mulki ne bayan rasuwar yayan sa wanda shine ke kan karagar kafin rasuwar sa wato Muhammadu Maccido, wanda ya rasu sakamakon hadarin jirgin sama da ya rutsa dasu.