Jump to content

TY Shaban

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
TY Shaban
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Larabci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a mawaƙi da mai tsara fim
Imani
Addini Musulunci

Tanim Yahuza Sha'aban wanda aka fi sani da TY Shaban ko Shaba, ya kasance mawaƙin Najeriya, ɗan wasan kwaikwayo, mai rawa, mai gabatar da shirin talabijin kuma mai shirya fim a masana'antar shirya fina-finai ta Arewacin Najeriya wanda aka fi sani da Kannywood.[1][2][3].

Farkon Rayuwa da Ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Shaba a yankin Nassarawa da ke ƙaramar hukumar Nasarawa a jihar Kano, Najeriya.Ya halarci makarantar firamare ta Brigade, karamar makarantar sakandare a kwalejin malamai ta Kano da kuma babbar makarantar sakandare a filin wasa na makarantar sakandaren gwamnati da ke Duka a Kano. Yayi karatun aikin gona a Kwalejin Ilimi ta Tarayya (Fasaha) Bichi.Ya kuma karanci Public Administration a Kano Polytechnic. Ya kuma yi difloma a harkar Fina-finai a Jami’ar Yusuf Maitama Sule, Kano,duk a Jihar Kano.TY Shaban mawaƙi ne kuma mai shirya fim kuma furodusa a Fina- Finan Arewacin Najeriya.TY Shaban shi ne mahaifin Sani TY Shaban (Freiiboi) wani mawaƙin HIP-HOP na Hausa mai shekaru 16 daga Arewacin Najeriya.[4][5]Shaban ya ce ya sanya ɗan nasa ne a cikin filin nishadi saboda ya gano cewa hazakar yaron ta hanyar waka ne.[6]

Masana'antar Kiɗa

[gyara sashe | gyara masomin]

An fara sanin Shaban a fagen Mawakan Hausa. Wakokinsa "Uwargida Ran Gida" da "Shaba zo Taho" sanannu ne saboda sun kai kowane yanki na kasar Hausa.

Masana'antar Fim

[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan aikin waƙa,Shaban ya shiga harkar fim,yana fitowa a fina-finai kuma ya zama furodusa.A shekarar 2019,BBC Hausa ta sanya fim din Shaban a cikin Goma cikin fina-finan Hausa.

  1. "Shaban Ty". multichoicetalentfactory.com (in Turanci). Retrieved 2021-02-13.
  2. . "TY Shaban da [[Samira Ahmad]] na murnar zagayowar ranar haihuwar diyarsu, A'isha". HausaFilms.TV Blog. Retrieved 2021-02-13. URL–wikilink conflict (help)
  3. "Yan kannywood sun nuna bacin ran su kan rashin tsawatarwa game da hoton diyar gwamnan kano da angonta". Pulse Nigeria (in Turanci). 2018-03-09. Retrieved 2021-02-13.
  4. "...Daga Bakin Mai Ita tare da Sani TY Shaban 'Free Boy'". BBC News Hausa. 2020-12-03. Retrieved 2021-02-13.
  5. Hiphop, Hausa. "FREIIBOI SHABA-NUMBER 1" (in Turanci). Archived from the original on 2021-06-14. Retrieved 2021-02-13.
  6. https://www.bbc.com/hausa/articles/c294wx89wygo