Za a iya gano tarihin Nijeriya daga mazauna na farko wadanda suka wanzu tun daga aƙalla alif 13,000 BC da kuma wayewar farko irin su al'adun Nok wanda yasoma kusan daga alif 1500 BC. Yawancin tsoffin al'ummomin Afirka sun zauna a wannan yankin da aka fi sani da Najeriya a yau, irinsu Masarautar Nri,[1]Daular Benin,[2] da Daular Oyo.[3]Musulunci ya iso Najeriya ne ta daular Bornu tsakanin (1068 AD) da kasashen Hausa wajen (1385 AD) a ƙarni na 11,[4][5][6][7] yayin da addinin Kiristanci ya shigo Najeriya a ƙarni na 15 ta hanyar Augustawa da Capuchin sufaye daga Kasar Portugal.[ana buƙatar hujja]Daular Songhai ta mamaye wani sashe na yankin.[8]Son Ali ne ya kafa garin Gao a matsayin babban birnin daular, duk da cewa akwai jihar Songhai a yankin Gao tun daga karni ta 11. Wasu muhimman birane a jihar sun hada da Timbuktu da Djenné wadanda aka kame a shekarun 1468 da 1475 bi da bi, inda suka zamo cibyar kasuwanci sannan daga kudu akwai arewacin jihar Akan wato Bonoman. Daga ƙarni na 15, ƴan kasuwar bayi Turawa sun isa yankin don siyan ’yan Afirka bayi a matsayin wani ɓangare na cinikin bayi na Atlantic, wanda ya fara a yankin Najeriya na zamani; tashar jiragen ruwa ta Najeriya ta farko da ’yan kasuwar bayi da Turawa ke amfani da ita ita ce Badagry, tashar ruwa ta bakin teku.[9][10] ƴan kasuwan yankin sun ba su bayi, tare da haifar da rikice-rikice tsakanin ƙabilun yankin da kuma kawo cikas ga tsofaffin tsarin kasuwanci ta hanyar Trans-Sahara.[11]