Jump to content

Ummi Rahab

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ummi Rahab
Rayuwa
Cikakken suna Rahab Salim
Haihuwa Jahar Kaduna, 7 ga Afirilu, 2004 (20 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƴan uwa
Abokiyar zama Lilin Baba
Sana'a
Sana'a jarumi



Rahab Salim wacce aka fi sani da Ummi Rahab ko Ummi Takwara, (An haife ta a ranar 7 ga watan Afrilu, shekara ta 2004) a garin Kaduna.[1] Ƴar wasan kwaikwayo ce a masana'antar fim ta Kannywood[2] 'yar rawa kuma 'yar talla wacce ta auri Jarumi, Furodusa kuma mawakin Hausa, Lilin Baba.

Farkon Rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Ummi Rahab a ranar 7 ga watan Afrilu, shekara ta 2004 a cikin garin Kaduna dake arewa maso yammacin Najeriya.[3][4]

Ummi rahab tayi karatun firamare da sakandire a jihar Kaduna, kafin daga baya ta koma garin Kano domin ci gaba da rayuwar ta.[5]

Ummi Rahab na daga cikin jaruman Kannywood da suka fara taka rawa a wasan kwaikwayo tun suna ƙanana. Ummi Rahab ta fara fitowa a fim tun lokacin tana makarantar firmare, acikin fim din da tayi fice da shi wato "Takwara Ummi". A lokacin tana da shekaru goma a duniya inda ta fito a matsayin diyar Adam A Zango.[1] Ummi Rahab tayi fice a masana'antar fim na Kannywood kuma ta fito a bidiyon waƙoƙin Hausa da dama da suka hada da: Meleri - WUFF Dake.

Ranar 18 ga watan yuni,shekarata 2022 Ummi Rahab ta auri Lilin Baba.[6]

Mahadar shafukan waje

[gyara sashe | gyara masomin]
  1. 1.0 1.1 "Ummi Rahab Kannywood Biography, Age, Photos, Phone Number &Net Worth - ArewAngle". 18 January 2022. Retrieved 4 October 2022.
  2. ttps://www.northernwiki.com.ng/cikakken-tarihin-ummi-rahab/
  3. Hausaflix (18 March 2022). "Tarihin Rayuwar Ummi Rahab: Tarihi cikakke, rayuwar ta a Kannywood". Hausaflix. Retrieved 4 October 2022.
  4. Admin (13 March 2022). "CIKAKKEN TARIHIN UMMI RAHAB - Northernwiki Jaruman kannywood". Northernwiki. Retrieved 4 October 2022.
  5. Hausaflix (18 March 2022). "Tarihin Rayuwar Ummi Rahab: Tarihi cikakke, rayuwar ta a Kannywood". Hausaflix. Retrieved 4 October 2022.
  6. https://hausa.legit.ng/kannywood/1475147-aure-ya-kullu-bidiyo-da-hotunan-auren-lilin-baba-dakyakkyawar- amaryarsa-ummi-rahab/