Wikipedia:Wiki For Human Right 2021

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

WikiForHumanRights, Wani gangami ne da ake gudanarwa a duk shekara na wayar da kawunan mutane dangane da haƙƙoƙin ɗan adam. A ko wacce shekara bikin na zuwa da taken sa. Taken bikin na wannan shekarar shine Haƙƙin Samun Lafiyayyen Muhalli

Matashiya

Kowane Ɗan Adam ya kamata ya sami amintacce, tsaftatacce, da kuma lafiya mai ɗorewa da kyakkyawan muhalli don zaman rayuwa. Haƙƙin samun kyakkyawan yanayi na rayuwa, haƙƙi ne wanda sama da ƙasashe 159 suka amince da shi a duniya. Wannan babban abin alfahari ne.

Hausa Wikipedia za ta shiga gangamin #WikiForHumanRights domin bin sawun sauran ƴan uwanta na duniya domin yin rubuce-rubuce a shafin Wikipedia waɗanda suka danganci haƙƙin ɗan adam musamman na Mallakar muhalli.

Samun Ingantaccen ilmi game da haƙƙin ɗan adam da mahalli, zai taimaka wa al'umma ta farfaɗo daga COVID-19. Fahimtar ilimin da ke da alaƙa da waɗannan zai taimaka wa al'ummomin Hausawa fahimtar haƙƙin su.

Kasance tare da mu dan ƙirƙirar maƙaloli wanɗanda zasu haɗa da haƙƙin ɗan adam, lafiyar muhalli da kuma al'ummu daban-daban waɗanda al'amuran muhalli suka shafa a duniya.

Hausa Wikipedia ta shirya gudanar da babban gangami Na Musamman wanda zai guda akan kare hakkin dan Adam. Zamu saurari jawabi daga kwararru kan kare hakkin dan Adam. Bayan nan kuma zamu gudanar da gasa ta rubutu a kan shafin Hausa Wikipedia wanda za'a samu damar lashe kyautar wayoyi da sauran kyaututtuka. Muna tanaji maƙalolin da muke so ayi rubutu a game da su a wannan shafin.

SHIRI Hausa Wikipedia ta shirya gudanar da babban gangami Na Musamman wanda zai guda akan kare hakkin dan Adam. Zamu saurari jawabi daga kwararru kan kare hakkin dan Adam. Bayan nan kuma zamu gudanar da gasa ta rubutu a kan shafin Hausa Wikipedia wanda za'a samu damar lashe kyautar wayoyi da sauran kyaututtuka. Muna tanaji maƙalolin da muke so ayi rubutu a game da su a wannan shafin.

DOMIN SHIGA GASA Kowanne edita zai iya shiga gasar. Abinda ake buƙata shine mutum ya kasance yana da rijista da Wikipeda.

Sannan kuma sai kaje ma saka sunan ka a Nan

Maƙalolin da ake bukata

Ana bukatar a yi rubutu a game da waɗannan maƙalolin da suke a ƙasa ko kuma wasu maƙalolin da suka shafi Haƙƙin Ɗan Adam.

Ba iyaka wadannan maƙalolin kadai ake bukatar ayi ba, dukkan wata mukala da ta shafi kare hakkin dan adan ko cin zarafin dan adam ko masu kare rajin haƙƙin dan adam ana bukatar su. Domin samun kari na jerin maƙaloli waɗanda suka shafi hakkin dan adam ku shiga wannna shafin domin samun ƙari. Hakanan kuna iya ƙirƙirar wasu shafukan waɗanda basu a kowacce wikipedia.


Wannan jeri ne na mutane da suka shahara wajen yin Aiyuka na kare hakkin Dan Adam. Wasu ana bukatar a yi su yayin da wasu kuma ake bukatar a inganta su.

Sunaye
Adeola Austin Oyinlade
Aminu Kano
Ayo Fasanmi
Ayodele Awojobi
Bamidele Aturu
Beko Ransome-Kuti
Bisi Adeleye-Fayemi
Dele Giwa
Emmanuel N. Onwubiko
Fela Kuti
Festus Keyamo
Funmilayo Ransome-Kuti
Femi Falana
Gani Fawehinmi
Kenneth Uwadi
Kiki Mordi
Ola Oni
Olikoye Ransome-Kuti
Olisa Agbakoba
Omoyele Sowore
Sonny Okosun
Segun Awosanya
Abiola Akiyode-Afolabi
Priscilla Achapka

Wannan jerin dake a ƙasa kuma maƙaloli ne da suka shafi haƙƙin ɗan adam da ake bukatar ayi su.

Abin Kura mun riga mun shirya sunan da ya kamata ya zama a Hausa Wikipedia, daga gaba kuma ainahin sunan da maƙalar tazo dashi ne a Wikipedia ta Turanci. Abinda ake buƙata shine a fassara wannan maƙalar cikin Hausa da sunan da muka bata. Idan kuma kana da tambaya to kayi a shafin Tattaunawa na wannan shafin ko a kafar mu ta sada zumunta.

Wasu ƙungiyoyi na kare haƙƙin ɗan adam na ƙasa da ƙasa

Wannan aikin wani bangare ne na hadin gwiwa tsakanin Gidauniyar Wikimedia da Ofishin Babban Kwamishina na Kare Hakkin Dan-Adam na Majalisar Dinkin Duniya (UN Human Rights), wanda Wikimedia Argentina, Wikimedia Tunisia da sauran kungiyoyin Wikimedia da ke yankin suka tallafa.

Domin ƙarin bayani Shiga nan