Zaynab Alkali
![]() | |
---|---|
![]() | |
Rayuwa | |
Haihuwa | jihar Borno, 1950 (70/71 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Bayero |
Harsuna | Turanci |
Sana'a | |
Sana'a |
author (en) ![]() |
Zaynab Alƙali An haife ta ne a shekarar 1950 ta kasan ce farfesa ce a harshen Turanci. kuma tafito ne daga gidan Turah- Mazila dake jahar Borno da Adamawa, tayi Makarantar sakandarin tane a Queen Elizabeth, Illorin. sannan ta tafi zuwa Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria inda ta samu digirin ta na farko dana biyu, Sai daga baya ta koma Jami'ar Bayero dake Kano takaranta English har takaiga tasamu digiri na uku wato matakin Dakta. Zainab Alkali ta shahara a rubuce-rubucen takaitattun kagaggun labarai, littafinta na farko data wallafa ya shahara shi ne littafinta 'The Stillborn' a shekara ta 1984 sannan sai littafinta na biyu 'Virtuous woman' wadda Longman suka wallafa a shekara ta 1987, Zainab Alkali dai ta kasance marubuciya kuma ta wallafa littafai da dama, kuma littafan ta sun kasance an fassara su zuwa yaruka daban-daban kamar Jamusanci, larabci, Faransanci da Safaniyanci.
Tana daga cikin mata marubuta na farko a Arewacin Najeriya.
Rayuwarta[gyara sashe | Gyara masomin]

An haifi Zainab Alkali ne a garin Tura-Wazila a jahar Borno dake Arewacin kasar Najeriya a shekarar 1950. Ta yi karatu a jami'ar Bayaro dake Kano da digirin BA a 1973 Ta yi karatun digirin digirgir a jami'ar sannan ta zama shugabar makarantar mata ta kwana ta Sakere Girls Boarding School. Ta koyar da darasin turanci a jami'o'in Najeriya da dama. Ta zama shugabar sashe a Jami'ar Jahar Nasarawa dake Keffi.
Ayyukanta[gyara sashe | Gyara masomin]
Littattafanta[gyara sashe | Gyara masomin]
- The Stillborn, Lagos: Longman (Drumbeats), 1984, ISBN 978-0-582-78600-4
- The Virtuous Woman, Longman Nigeria, 1987, ISBN 978-978-139-589-5
- Cobwebs & Other Stories, Lagos: Malthouse Press, 1997, ISBN 978-978-0230296.
- The Descendants, Tamaza, 2005, ISBN 978-978-2104-73-1
- The Initiates, 2007, ISBN 978-978-029-767-1.
Wanda ta gyara[gyara sashe | Gyara masomin]
- Zaynab Alkali, Al Imfeld (eds), Vultures in the Air: Voices from Northern Nigeria, Ibadan-Kaduna-Lagos: Spectrum Books, 1995, ISBN 978-978-2462-60-2