Zinedine Yazid Zidane

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Zinedine Yazid Zidane
Zinedine Zidane by Tasnim 03.jpg
ɗan Adam
jinsinamiji Gyara
ƙasar asaliFaransa Gyara
country for sportFaransa Gyara
sunan asaliZinedine Zidane Gyara
sunan haihuwaZinedine Yazid Zidane Gyara
sunaZinedine Gyara
sunan dangiZidane Gyara
pseudonymZizou Gyara
lokacin haihuwa23 ga Yuni, 1972 Gyara
wurin haihuwaMarseille Gyara
yarinya/yaroEnzo Fernández, Luca Zidane Gyara
harsunaSpanish, Italiyanci, Faransanci Gyara
sana'aassociation football player, association football manager Gyara
muƙamin da ya riƙeUNICEF Goodwill Ambassador Gyara
matsayin daya buga/kware a ƙungiyamidfielder Gyara
laƙabiZizou Gyara
makarantaUniversity of Limoges Gyara
addiniMusulunci Gyara
wasaƙwallon ƙafa Gyara
coach of sports teamReal Madrid CF, Real Madrid CF Gyara
Zinédine Zidane

Cikakken sunan Zinedine dai shine, Zinedine Yazid Zidane'. Kuma an haife shine a ranar 23 ga watan junin shekarar 1972. Wato yanzu yana da shekaru 37 a duniya. Sunayen Iyayen Zidane dai sune Ismail da Malika kuma dukkanin su musulmai ne larabawa da suka fito daga ƙasar Algeriya. kuma sunyi hijirah ne zuwa faransan a 1953, inda kuma suka zauna a garin Marseille, anan ne kuma aka haifi Zidane.

Zidane dai ya fara buga wasan ƙwallon ƙafa ne da ƙungiyar Club ɗin nan mai suna La Castellane dake garin na Marseille a lokacin yana da shekaru 14 da haihuwa. A lokacin ne kuma wani mai horas da yan wasa na ƙungiyar AS Cannes Jean Varraud ya ganshi tare da ɗaukan sa haya. Kuma a club ɗin ne ya shafe shekaru 4.

A ranar 8 ga watan Fabairun 1991 ne kuma Zidane ya fara cin ƙwallon sa na farko a gasar wasan ƙwarrarru ta Professional abinda ya burge shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafan na AS Cannes kuma harya bashi kyautar sabuwar mota. Bayan da Zidane yabar ƙungiyar AS Cannes ya kuma koma ƙungiyar Girondins de Bordeaux akan kuɗi Euro miliyan 7 a shekarar 1992-93.

A shekarar 1996 Zidane ya koma ƙungiyar wasan ƙwallon ƙafan Juventus akan kuɗi Fan miliyan 3.2. A shekarar 2001 kuwa, Zidane ya koma ƙungiyar Real Madrid akan kuɗi Euro miliyan 78 bayan daya sanya hannu a kwangilar wasa na shekaru 4. kuma a wannan lokaci kuɗin da Zidane ya sanya hannu shine mafi yawa da wani ɗan wasa ya samu a wajen kwangilar buga wasan ƙwallon ƙafa a duniya.

Daga cikin nasarorin da Zidane ya samu a lokacin wasannin sa sun haɗa da cin kofin Zakarun wasannin ƙungiyoyin wasan ƙwallon ƙafan Spain da kuma kasancewa zakarar wasan ƙwallon ƙafan ƙungiyar FIFA har sau uku. kuma Zidane ya shiga jerin sunayen mutane 100 na kundin FIFA. Zidane ya kuma shiga tarihin Hukumar ta FIFA na jerin sunayen yan wasan ƙwallon kafa na duniya irin su Pele da Vava da Geoff Hurst A ranar 7 ga watan mayun 2006 ne Zidane ya buga wasan sa na ƙarshe a ƙungiyar sa ta Real Madrid. Zidane ya taimaka wajen samun nasarar cin kofin duniya da Faransa ta samu a shekarar 1998. A watan Junin bana ne dai aka naɗa shi mai bada shawar na musanman ga shugaban ƙungiyar wasan ƙwallon ƙafa ta Real Madrid Florentino Perez. A shekarar 2004 kuwa, Mujallar Forbes ta 'yan jari hujja da ake bugawa a Amirka ta baiyana Zidane a matsayin na 42 wajen 'yan wasan da suka fi kowane ɗan wasa samun kuɗi a duniya, inda tace yana samun dalar Amurka miliyan 15.8 a duk shekara.

Zidane yana da aure da yara kuma sunan matar sa Veronique suna da 'ya'ya huɗu; Enzo da luca da theo da Elyaz. Yanzu haka kuma 'ya'yan sa biyu Luca da Theo suna buga wasa a ƙaramar ƙungiyar wasan ƙwallon ƙafan Real Madrid.

Kuma yanzu haka yana rike da takardar zama ɗan ƙasar Algeriya, mahaifar iyayen sa duk da cewar shi ɗan ƙasar Faransa ne wato inda aka haife shi.