Ahmad Usman

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ahmad Usman
Gwamnan jahar oyo

22 ga Augusta, 1996 - ga Augusta, 1998
Chinyere Ike Nwosu - Amen Edore Oyakhire
Gwamnan jahar Ondo

Satumba 1994 - ga Augusta, 1996
Mike Torey - Anthony Onyearugbulem (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa 20 ga Augusta, 1951
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Mutuwa Jos, 14 ga Afirilu, 2021
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Aikin soja
Fannin soja Sojojin Ƙasa na Najeriya
Digiri colonel (en) Fassara

Kanal Ahmed Usman saurare (Agusta 20, 1951  – 14 Afrilu 2021) ya kasance mai kula da mulkin sojan Najeriya a jihar Ondo sannan kuma jihar Oyo a lokacin mulkin soja na Janar Sani Abacha.[1]

Farkon aiki[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Ahmed Usman a shekarar 1951 kuma ya girma a Okura-Lafia, ƙaramar hukumar Dekina, jihar Kogi . Bayan shiga aikin soja, muƙamai shi sun haɗa da zaman kwamanda na biyu a, Bataliya ta 192, Abak da Bataliya ta 141, Kano (1983-1985), Rundunar Majalisar Dinkin Duniya a Lebanon (1985-1986) da Bataliya Kwamanda G Amphibious, Elele Port Hartcourt (1990-1991).

Gwannan jihar ondo[gyara sashe | gyara masomin]

An naɗa Usman gwamnan jihar Ondo a watan Satumba 1994. Yayin da gwamnan jihar Ondo, Usman ya naɗa Oba Adeleye Orisagbemi a matsayin Attah na Ayede Ekiti. Yayin da ake nuna damuwa game da ƙungiyoyin asiri a jihar, a ranar 17 ga watan Yunin 1996, Usman ya yi barazanar korar duk wani alkalin jihar Ondo da ya bayar da belin wadanda ake zargi da kungiyar asiri. A shekarar 1998, Adeoluwa Oyerinde, tsohon Manajan Darakta na wani reshen Kamfanin Inbestment na Odu’a, anyi zargin cewa an bai wa Usman da wasu gwamnonin soji cin hanci yayin da Usman ke rike da mulki a Jihar Ondo.

Gwamnan jihar Oyo[gyara sashe | gyara masomin]

A watan Agustan 1996 ne aka tura Usman jihar Oyo domin ya zama gwamna a dai-dai lokacin da ake ƙara nuna rashin jin dadi game da mulkin soja karkashin jagorancin Sani Abacha. A ranar 12 ga Mayun 1997, wani bam da ya tashi a babban birnin jihar Ibadan ya raunata sojoji biyu da ɗan sanda guda.[2] Usman yace wadanda suka aikata wannan aika aika matsorata ne. An kashe mutane biyu tare da raunata kusan 20 a filin wasa na Salami da ke Ibadan a watan Afrilun 1998, lokacin da magoya bayan United Action for Democracy (UAD) suka tarwatsa wani gangamin goyon bayan Abacha da Kanar Usman ya yi jawabi a baya.

An kashe mutane bakwai a ranar Mayun 1998 a arangamar da aka yi tsakanin ƴan sanda da masu zanga-zangar neman dimokaraɗiyya. Usman ya zargi "makiya ƙasashen waje" da goyon bayan tashin hankalin. A cikin wannan watan ne Usman ya ce an sanya jami’an tsaro jajircewa domin daƙile duk wata zanga-zanga a babban birnin jihar Ibadan. Bayan ƴan kwanaki, an kama ƴan Najeriya 37, aka tuhume su da laifin yin zagon ƙasa, ciki har da malami kuma shugaban jam’iyyar Democratic Coalition na Jihar Oyo, Lam Adesina, wanda daga baya ya zama Gwamnan Jihar a shekarar 1999. Usman ya ce za a ɗauke su a matsayin fursunonin yaki. An tuhumi wasu mutane uku, daya fitaccen editan jarida ne da laifin zagon kasa. Sani Abacha ya rasu a watan Yuni 1998, kuma Usman ya samu mukamin gwamna a watan Agusta 1998.

Daga baya rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan dawowar mulkin dimokuradiyya a 1999 Usman ya shiga kasuwanci na zaman kansa kuma bai shiga harkar siyasa ba har sai a watan Agustan 2008, inda ya bayyana cewa yana da niyyar tsayawa takarar gwamnan jihar Kogi a 2011. Da yake takara a karkashin jam’iyyar PDP, ya sha kaye a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar. Daga baya ya nuna sha’awarsa ta tsayawa takara a zaɓen gwamnan jihar Kogi a 2019 shi ma a jam’iyyar All Progressives Congress, amma a ƙarshe bai shiga takarar ba.

Rasuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Usman ya rasu ne a ranar 14 ga Afrilu, 2021 yana da shekaru 69 a Jos, Jihar Filato, sakamakon rashin lafiya. An dawo da gawarsa garinsu na Okura-Lafia a jihar Kogi domin yin jana'izar Musulunci. [3] Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya mika ta'aziyyar rasuwar Usman.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]