Ayo Rosiji
Ayo Rosiji | |||
---|---|---|---|
| |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Abeokuta, 24 ga Faburairu, 1917 | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Harshen uwa | Yarbanci | ||
Mutuwa | 31 ga Yuli, 2000 | ||
Karatu | |||
Makaranta | University of London (en) | ||
Harsuna |
Turanci Yarbanci Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | Egbe Omo Oduduwa |
Cif Ayotunde Rosiji (24 Fabrairu 1917 - 31 Yuli 2000) ɗan siyasan Najeriya ne, wanda ya yi ministan lafiya da kuma ministan yaɗa labarai.[1]
An haife shi a Abeokuta, Jihar Ogun, a ranar 24 ga watan Fabrairu 1917 ɗa ne ga dangin wani ɗan sanda Egba. Rosiji ya halarci makarantar firamare ta Christ Church, Abeokuta, sannan ya halarci makarantar Grammar ta Ibadan da Kwalejin Gwamnati da ke Ibadan, inda ya yi karatun sakandare. Ya kuma yi karatu a babbar kwalejin Yaba, inda ya samu takardar shedar aikin injiniya. Daga nan sai ya tafi kasar waje don yin karatun digiri na biyu a fannin shari'a a Jami'ar London da ke Landan, Ingila bayan ya yi aiki a Shell Nigeria a matsayin injiniya. Ya koma Najeriya, ya zama ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa kungiyar Action Group.
Oloye Rosiji ya mutu a ranar 31 ga watan Yuli 2000.