Category:Muhammad

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Manzo Muhammad Al-Habib ɗan ʿAbdullahi (Sallallahu ʿAlaihi wa Sallam).

Muhammad Larabci محمد‎; Annabi ne kuma Manzo ne wato ma'aikin Allah Madaukakin Sarki. Allah Ya aiko shi domin ya tabbatar da addinin da Annabawan da suka gabace shi suka koyar, Kamar Annabi Ibrahim da Annabi Musa da Annabi Annabi Isah da dukkannin sauran Annabawan Allah (tsira da amincin Allah ya kara tabbata a gare su) Annabi Muhammad (s.a.w) shine cikamakon Annabawa, wato Annabin karshe wanda daga kansa babu wani annabin Allah. Dukkan wanda yayi ikirarin annabta bayan zuwan Annabi Muhammad (s.a.w) to karya yake. Shine kuma ya hada kan dukkan larabawa suka dunkule waje daya, tare da daidaita yan adam ta hanyar koyarwar sa da Alkue'anin da yazo da shi.

Nasabar Sa[gyara sashe | gyara masomin]

Muhammad ɗan Abdullahi ɗan Abdul-Muɗɗalibi ɗan Hashimi ɗan Abdu-Manafi ɗan Ƙusayyi ɗan Kilabi, Sallallahu alaihi wa aalihi wa sallam, (Harshen Larabci: Abūl-Qāsim Muḥammad ibn ʿAbd Allāh ibn ʿAbd al-Muṭṭalib ibn Hāshim ibn ˁAbd Manāf ibn Qusayy ibn Kilāb) nasabarsa maɗaukakiya tana tuqewa zuwa ga Annabi Ibrahim, alaihi salatu wassalam. Manzon Allah ne. Khataman-Nabiyyin da addinin Musulunci.

Iyayen Sa[gyara sashe | gyara masomin]

Mahaifiyarsa: Ita ce Aminatu (Āminah) 'yar Wahbi ɗan Abdu-Manaf ɗan Zuhrata ɗan Kilabi (Radhi Allahu anha). Alkunyarsa: Abu-Qasim, Abu Ibrahim.

Mahaifinsa: Shi ne Abdullahi dan Abdullahi dan Abdulmutallabi dan Hashimu dan Abdumunaf dan Qusay dan Kilab (Allah ya kara yarda a gareshi)

Laƙabinsa: Al-Musɗafa (zababben Allah) yana da sunaye da suka zo a cikin Ƙur'ani Mai Girma kamar, Khataman-Nabiyyin, da Al-Ummi da Al-Muzzammil da Al-Muddassir da An-Nazir da Al-Mubin da Al-Karim da An-Nur da An-Niˁima da Ar-Rahma da Al-ˁAbdu da Ar-Ra'uf da Ar-Rahim da Ash-Shahid da Al-Mubasshir da An-Nazir da Ad-Da'i da sauransu.

Haihuwar Sa[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Annabi Muhammad (s.a.w) a wajen shekara ta 570M. Mahaifinsa shine Abdullahi ya rasu kafin haihuwar Sa. Mahaifiyar sa Amina itama ta rasu lokacin da yake dan shekara shida a [[duniya]. Haka yasa kakan sa Abdul-Mudallib ya rike shi har zuwa lokacin daya rasu, lokacin Annabi Muhammad (s.a.w) yana dan shekara takwas a duniya. Daga nan sai kawun sa Abu-Talib yaci gaba da rikon sa. Abu-Talib ya taimaka ma Manzon Allah (s.a.w) sosai a rayuwar sa.

Aiko Shi[gyara sashe | gyara masomin]

Kogon Hira, wajen da aka fara wa Annabi Wahayi

Aikoshi: An aiko shi a Makkah 27 Rajab yana ɗan shekara arba'in.

Koyarwarsa Ya zo da daidaito tsakanin dukkan halitta da 'yan-uwantaka da rangwame na gaba ɗaya ga wanda ya shiga musulunci, sa'annan ya kafa shari'a maɗaukakiya da dokoki na adalci da ya karɓo daga wajan Allah su kuma musulmi suka karɓa daga gare shi.

Mu'ujizozinsa Mu'ujizarsa madauwamiya ita ce Ƙur'ani amma waɗanda suka faru a farkon Musulunci suna da yawa ba sa kuma kirguwa.

Kiransa Ya kira mutane zuwa ga Tauhidi a Makkah a ɓoye shekara uku ya kuma kira su a bayyane shekara goma.

Hijirar Sa zuwa Madina[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan Tsanani da takurawar Kafuran Makkah akan Annabi Muhammad (s.a.w) da wadanda sukayi inami da shi yayi yawa, sai Allah Yayi ma Manzon Sa da sauran Wadan da sukayi imani da shi izinin akan suyi kaura daga garinsu na haihuwa wato birnin Makka zuwa wani garin daban na wati Madina. Mutanen birnin Madina kuwa sunyi matukar murna da zuwan sa garin su kuma sun bashi kyakkyawan masauki. Sanna kuma sukayi imani dashi suka shiga AddiMusulunci. A farkon Hijira dai Shi Annabi da kansa dakuma babban aminin sa kuma na farko wajen imani dashi wato Sayyadina Abubakar Sukayi tasu hijirar tare. Sannan sauran musulmai sukayi ta bin bayansu daya bayan daya. Kaurar Annabi (s.a.w) daga Makka zuwa Madina shine ake kira Hijira kuma shine farkon kalandar Musulunci.

Matan Sa[gyara sashe | gyara masomin]

Annabin Musulunci Muhammad Ya auri mata goma sha daya, ga Jerin sunayen su.

Ammomin sa[gyara sashe | gyara masomin]

Ammominsa: Tara ne, su 'ya'yan ˁAbdul-Muɗɗalib ne: Al-Haris da Zubair da Abu Ɗalib da Hamza da Al-Ghaidaq da Dirar Al-Muqawwam da Abu Lahab da ˁAbbass.

Ammominsa mata: Su shida ne daga iyaye mata daban-daban su ne: Aminah da Ummu Hakima da Barra da Atiqa da Safiyya da Arwa. Wasiyyansa goma sha biyu ne, su ne: Amirul-Mu'minina Ali ɗan Abi Ɗalib (a.s) da Hasan ɗan ˁAli da Hussain ɗan ˁAli da ˁAliyyu ɗan Husaini da Muhammad ɗan ˁAli da Jaˁfar ɗan Muhammad da Musa ɗan Jaˁfar da ˁAli ɗan Musa da Muhammad ɗan ˁAli da ˁAli ɗan Muhammad da Alhassan ɗan ˁAli da Muhammad ɗan Hassan Mahadi (a.s).


'Ya'yayen sa


  • Qasim ibn Muhammad, (598 – 600 ko 601 M)
  • Zainab bint Muhammad, (599 – 630 M)
  • Ruqayyah bint Muhammad, (601 – 624 M)
  • Umm Kulthum bint Muhammad, (603 – 630 M)
  • Abd-Allah ibn Muhammad, (d. 615 M)
  • Fatimah bint Muhammad, (c. 615 – 632 M)
  • Ibrahim ibn Muhammad, (630 – 631 M)

Masu yi masa hidima na musamman[gyara sashe | gyara masomin]

Mai tsaron ƙofarsa: Anas ɗan Malik.

Mawaƙinsa: Hassan ɗan Sabit, da ˁAbdullahi ɗan Rawahata, da Ka'abu ɗan Malik.

Mai kiran sallarsa: Bilal Al-Habashi da ˁAbdullahi ɗan Ummu Maktum da Saˁad Al-Kirdi.

Tambarin zobensa: Muhammadur Rasulullah!

Tsawon rayuwarsa: shekaru 63.

Tsawon lokacin Annabtarsa: shekaru 23.

Tarihin wafatinsa: 28 Safar 11 H.

Wajan da ya yi wafati: Madinah.

Inda aka binne shi: Madinah a Masallaci Maɗaukaki Mai Alfarma. Ka sani cewa Muhammad (S.A.W) shi ne ƙarshen annabawa kuma addininsa shi ne musulunci mai shafe duk wani addini kuma shari'arsa zata wanzu har zuwa qiyama kuma ita kaɗai ce shari'ar da zata arzuta mutum da tabbatar masa da burinsa da amincinsa har zuwa ƙarshen rayuwar duniya da lahira. Kamar yadda shi kaɗai ne mutum abin koyi ga dukkan duniya baki ɗaya, dukkan mutanen duniya idan suna son alheri ga kawukansu to dole ne su bi tarfarkinsa su yi koyi da kyawawan halyensa (S.A.W) da kuma sanin sashen tarihinsa da ba makawa mu kawo wasu daga siffofinsa (S.A.W): Shi ne Muhammad ɗan ˁAbdullah (S.A.W) kuma babarsa ita ce Aminatu 'yar Wahab. An haife shi a Makkah ranar juma'a goma sha bakwai ga watan Rabi'ul awwal bayan ɓollolwar alfijir a shekarar giwa, a zamanin sarki mai adalci Kisra . (wato idan an kwatanta shi da ire-irensa).

Aiko Annabi Mai Daraja (S.A.W)

An aiko Annabi Muhammad (S.A.W) da saqo a 27 ga Rajab bayan yana ɗan shekara 40 yayin da Jibrilu (A.S) ya sauka gareshi daga wurin Allah (S.W.T) yana kogon Hira wanda yake dutse ne a Makkah ya ce masa ka karanta kuma ya saukar masa da ayoyi biyar na surar Alaƙi . Sai ya zo ya tsaya a kan dutsen Safa a masallaci mai alfarma na Makkah a lokcin akwai jama'a masu yawa a wurin da ake taruwa ya isar da saƙon Allah na shiryar da mutane zuwa ga imani da shi yana cewa da su: "Ku ce babu abin bauta sai Allah kwa rabauta" .

A lokacin tunda mutanen Makkah mushrikai ne, kuma suna ganin maslaharsu ita ce shirka kuma suna tsoron maslaharsu sai suka riƙa yi masa isgili suna yi masa dariya suna cutar da shi. Kuma duk sa'adda ya dage wajen shiryar da su sai su dage wajen cutar da shi har ya ce: "Ba a cutar da wani Annabi ba kamar yadda aka cutar da ni" . Ba wanda suka yi imani da shi sai mutane ƙalilan, na farkonsu Imam ˁAli sannan sai matarsa Khadijah (A.S) sannan sai wasu mutane. Farkon wanda ya yi imani da shi daga maza Imam Ali sannan daga mata sai Hadiza (A.S).

Yayin da takurawar mushrikai ta yi yawa sai ya yi hijira zuwa Madinah wannan kuwa ita ce hijirar farko a tarihin Musulmi, yayin da suka yi yawa sai qarfinsu ya daɗu kuma suka samu koyarwa daga Manzon Allah da shari'arsa Mai Sauƙi Mai Hikima, da kuma misali na kyawawan halaye da mutumtaka da wayewa da cigaba a Madinah har suka fi dukkan duniya da addini na sama da waɗanda ba na sama ba. Kuma an samu yaƙoƙi masu yawa a Madinah kuma dukkanninsu sun zama domin kare kai ne daga maƙiya mushrikai da yahudawa da kiristoci da suke kai hari kan musulmi, kuma Annabi a kowne lokaci yana zaɓar ɓangaren sulhu da zaman lafiya ne da rangwame, don haka ne ma adadin waɗanda ake kashewa daga ɓangarorin biyu ba su da yawa a dukkan yaƙoƙinsa tamanin da wani abu, wato; waɗanda aka kashe na musulmi da kafirai duka ba su kai sama da dubu ɗaya da ɗari huɗu ba.

Mutuwa Mai Zafin Gaske Tun lokacin da aka aiko Annabi da saƙo har ya tafi daga duniya wahayi yana sauka gareshi kuma Jibrilu (A.S) shi ne ake aiko masa daga wajen Ubangiji (S.W.T) a hankali a hankali har littafin Ƙur'ani ya ciki a cikin shekaru ishirin da uku, sai Manzo (S.A.W) ya yi umarni da a haɗa shi kamar yadda yake a yau ɗin nan. Manzo (S.A.W) ya kasance yana tsara wa musulmi duniyarsu da addininsu, yana sanar da su littafi da hikima kuma yana yi musu bayanin dokokin ibada da biyayya da mu'amala da zamantakewa da siyasa da tattalin arziki da sauransu.[1]

  1. Hooker, Richard (July 14, 1999). "arkan ad-din the five pillars of religion". United States: Washington State University. Archived from the original on 2010-12-03. Retrieved 2010-11-17. Unknown parameter |deadurl= ignored (|url-status= suggested) (help)

Ƙananan rukunoni

Wannan rukuni ya ƙumshi 8 wanɗannan ƙananan rukunoni, daga cikin jimlar 8.

A

K

S

Z

Shafuna na cikin rukunin "Muhammad"

9 shafuna na gaba suna cikin wannan rukuni, daga cikin jimlar 9.