Kisan gilla a Baga, 2013

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Infotaula d'esdevenimentKisan gilla a Baga, 2013
Map
 12°32′00″N 13°51′00″E / 12.5333°N 13.85°E / 12.5333; 13.85
Iri faɗa
Kwanan watan 16 –  17 ga Afirilu, 2013
Wuri Baga
Ƙasa Najeriya

Kisan kiyashi na Baga ya fara faruwa ne a ranar 16 ga watan Afrilu, a shekarar 2013 a kauyen Baga na Najeriya, a jihar Borno, inda aka kashe fararen hula akalla kusan guda 200, gami da jikkata daruruwa, tare da lalata gidaje da kasuwanni sama da 2,000 da salawantar da miliyoyin Nairori.[1][2] 'Yan gudun hijira, jami'an farar hula, da kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun zargi sojojin Najeriya da aikata kisan kiyashi; wasu jami'an soji sun dora laifin akan kungiyar Boko Haram, wacce tayi kaurin sune akan kai munanen hara-hare.[2]

Wai-wa-ye[gyara sashe | gyara masomin]

Dubban mutane ne suka mutu a fadace-fadace a Najeriya tun somawar rikicin Boko Haram a shekara ta 2009,[3] wanda ya faro ne daga yankin arewacin Najeriya. An kashe jagoran boren kungiyar Mohammed Yusuf a Maiduguri na jihar Borno a shekara ta 2009.

A cewar jaridar The New York Times, sojojin Najeriya sun yi amfani da tsarin "scorched-earth standard-(wata dabara ce ta soja da ke ruguza ko wargaza duk wani abu mai amfani dake a hannun makiya)" a yakin da suke yi da Boko Haram, tare da kashe fararen hula a lokacin da suke aiki a yankunan-(unguwanni) matalauta. Kafin kisan kiyashin na Baga, an saba amfani da tsarin-(scorched-earth standard) a matsayin matakan hukunta farar hula, ba tare da wani hukunci ba a Najeriya.[2]

Kwamandan rundunar hadin gwiwa ta Ƙasashen Duniya, Birgediya Janar Austin Edokpaye ya zargi mazauna garin na Baga da baiwa 'yan Boko Haram kariya kafin harin.[4]

Baga wani ƙaramin ƙauye ne wanda ake kamun kifi da ke gaban tafkin Chadi,[5] kusa da iyakar Chadi da Nijar.

Abubuwan da suka faru[gyara sashe | gyara masomin]

A yammacin ranar 16 ga watan Afrilu, yan Boko Haram sun yi artabu da sojojin gwamnati a wani sansanin soji da ke wajen Baga, inda suka kashe daya daga cikinsu.[2] A cewar mazauna garin, sojojin sun dawo ne da wasu dakaru da motocin yaki masu sulke.[2] Daga nan ne ake zargin sojoji sun kona gidaje a garin Baga ta hanayar watsa man fetur gami da kona kauyen, haka-zalika da harbin mutanen kauyen da suka yi yunkurin tserewa.[2][6] Wasu da suka yi yunkurin guduwa zuwa tafkin Chadi sun nutse a can (cikin tafkin), yayin da wasu suka samu damar tserewa cikin daji da ke kewaye yankin.[2] A cewar mazauna garin, sojojin sun ci gaba da kona gidaje a Baga a ranar 17 ga watan Afrilu.[7][6]

Birgediya Janar Austin Edokpaye ya bayyana cewa fararen hula shida ne kawai da soja daya aka kashe, yayin da sojojin suka kashe "yan ta'addar Boko Haram su 30."[7][4] Ya kara da cewa “Gidaji 30” ne kawai aka kona kuma makaman Boko Haram ne musababin tayar da gobarar.[7][4] Mazauna yankin da jami’an farar hula sun yi zargin cewa an kashe mutane kusan 200 tare da kona gidaje sama da 2,000.[7][6][2] An bayar da rahoton cewa an samu asarar rayuka musamman a tsakanin yara da tsofaffi.[2] A ranar 17 ga watan Afrilu, mutane 193 wadanda suka jikkata, an kwantar da su a asibitin kiwon lafiya na gida.[7] Rahoton hotunan tauraron dan adam na kungiyar Human Rights Watch da ta yi nazari akai, sun nuna cewa akalla gine-gine 2,275 ne suka ruguje sannan wasu gine-gine 125 suka lalace sosai.[6]

Martani[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan kisan kiyashin gwamnatin Najeriya ta fuskanci matsin lamba daga gwamnatocin kasashen duniya da kafafen yada labarai, lamarin da ya sa majalisar dokokin Najeriyar ta bukaci a gudanar da bincike.[2] Sojojin Najeriya sun tare gami da hana 'yan jaridun da ke yunkurin shiga kauyen, shiga kauyen.[2]

Inkarin sojojin Najeriya[gyara sashe | gyara masomin]

Birgediya Janar Chris Olukolade ya bayyana cewa duk wanda ya zargi sojojin Najeriya, to ya tausaya wa 'yan Boko Haram, kuma ya kara da cewar su-(yan boko haram), ne ke da alhakin kisan kiyashin, kuma sun harbe sojojin gwamnati daga kauyen.[2]

Gwamnatin Amurka tayi Allah wadai[gyara sashe | gyara masomin]

Mukaddashin mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka Patrick Ventrell, a ranar 22 ga watan Afrilu, na shekarar 2013, ya yi Allah wadai da rikicin da aka yi tsakanin jami’an tsaron Najeriya da mayakan Boko Haram a garin Baga, inda ya bukaci hukumomi da su mutunta hakkin dan Adam.[8]

Najeriya ta ba da umarnin bincike[gyara sashe | gyara masomin]

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, a ta bakin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Reuben Abati, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan fararen hula da aka kashe a yakin da aka yi tsakanin mayakan Boko Haram da sojojin Najeriya a karshen mako.[9]

Binciken Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam ta Kasa[gyara sashe | gyara masomin]

Hukumar kare hakkin dan Adam ta Najeriya, a ranar 29 ga watan Afrilun 2013 ta sanar da cewar; za ta gudanar da bincike a kan lamarin.[10] A watan Yunin 2013, hukumar ta fitar da rahoton wucin gadi. Rahoton ya bayyana cewa hukumar ta kasa kai ziyara garin Baga ne saboda gazawar jami’an tsaro wajen tabbatar da tsaron lafiyar jami’an hukumar a yankin. Rahoton, ya yi nuni da wani rahoton da ‘yan sanda suka yi, wanda ya nuna cewa sojoji a Baga “sun fara harbi ba kakkautawa ga duk wanda yake sun ganin (lamarin) ” kuma “sojoji sun kona unguwanni biyar a Baga gaba daya”.[11]

Duba kuma[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Baga Massacre: Crimes against humanity by JTF?". Nigeria Intel. Archived from the original on 12 May 2013. Retrieved 6 October 2014.
  2. 2.00 2.01 2.02 2.03 2.04 2.05 2.06 2.07 2.08 2.09 2.10 2.11 Nossiter, Adam (29 April 2013). "Massacre in Nigeria Spurs Outcry Over Military Tactics". The New York Times. Retrieved 29 April 2013.
  3. Dixon, Robyn (22 April 2013). "Dozens killed in gun battles in northern Nigeria". Los Angeles Times. Johannesburg. Retrieved 2 May 2013.
  4. 4.0 4.1 4.2 "37 Not 185 Died in Baga Clash, We Were Never Unprofessional – Army". Channels Television. 23 April 2013. Retrieved 13 July 2015.
  5. Akinlotan, Idowu (28 April 2013). "Baga massacre: Jonathan's words return to haunt him". The Nation (Nigeria). Archived from the original on 19 June 2013. Retrieved 29 April 2013.
  6. 6.0 6.1 6.2 6.3 "Nigeria: Massive Destruction, Deaths From Military Raid". Human Rights Watch. 1 May 2013. Retrieved 13 July 2015.
  7. 7.0 7.1 7.2 7.3 7.4 Ibrahim, Yahaya (27 April 2013). "Baga massacre: Survivors tell their stories". Daily Trust. Archived from the original on 23 September 2015. Retrieved 13 July 2015.
  8. "...UN, US, Others Condemn Killings". ThisDay. 24 April 2013. Archived from the original on 27 May 2013. Retrieved 13 July 2015.
  9. "Jonathan orders probe of Baga Massacre". PM News. 22 April 2013. Retrieved 13 July 2015.
  10. Ekott, Ini (30 April 2013). "Nigeria's Human Rights Body Launches Broad Inquiry into Baga Massacre". Premium Times. Retrieved 13 July 2015.
  11. The Baga Incident and the Situation in North-East Nigeria: An Interim Assessment and Report (PDF). The National Human Rights Commission. June 2013. pp. 14, 18–19. Retrieved 13 July 2015.

Hanyoyin haɗi na waje[gyara sashe | gyara masomin]