Kisan gilla a Konduga, Fabrairu 2014

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Infotaula d'esdevenimentKisan gilla a Konduga, Fabrairu 2014
Map
 11°39′06″N 13°25′10″E / 11.6517°N 13.4194°E / 11.6517; 13.4194
Iri aukuwa
Bangare na Rikicin Boko Haram
Kwanan watan 14 ga Faburairu, 2014
Wuri Konduga
Adadin waɗanda suka rasu 62

An yi kisan kiyashi a Konduga, Jihar Borno, Najeriya a ranar 11 ga Fabrairu 2014.[1][2] Kisan gillar da mayaƙan Boko Haram suka yi wa mazauna ƙauyukan Kirista ne.[3] Aƙalla mutane 62 ne suka mutu.[2]

Kisa[gyara sashe | gyara masomin]

Kisan kiyashin ya faru ne ranar 11 ga watan Fabrairun 2014 a Konduga, jihar Borno, arewa maso gabashin Najeriya.[1] Ƙauyen da harin ya faru yawancin mazaunan sa mabiya addinin kirista ne. Maharan da dama, kuma sanye da kayan sojoji ne, suka kai farmaki a ƙauyen. An harbe wasu daga cikin waɗanda aka kashe; wasu kuma an tsaga makogwaronsu. Ya zuwa 15 ga watan Fabrairu, 2014, an kashe mutane 121. Rahotanni sun ce mayakan sun yi furta kalmar Allahu Akbar ne a lokacin da suke kai hari ƙauyen, wadda kuma kalma ce da mabiya addinin Islama ke amfani da ita. Daga nan ne mayaƙan suka ci gaba da lalata gidaje da wuraren kasuwanci a garin.[4]

Abubuwan da suka biyo baya[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar 15 ga watan Fabrairun 2014, Boko Haram ta kai hari irin wannan a Izghe, Borno. Sama da mutane 121 aka kashe a harin. Dubban mutanen ƙauyen ne suka tsere daga garin zuwa iyakar ƙasar da Kamaru domin gujewa tashin hankalin. Waɗanda suka tsira da ransu sun ce ƴan bindigar sun yi harbi kan mai uwa da wabi a kan hanyarsu, ba gaira ba dalili, tare da ƙona coci-coci, gami da wawashe kayan abinci baki ɗaya.[4]

Daga nan ne ƴan ta'adan mayakan Boko Haram suka kai farmaki kan sojojin Najeriya inda suka kashe sojoji 9 sannan suka tilastawa sojojin ja da baya daga yankin.[5] Daga nan ne sojojin su ka yunƙuro da ci gaba da kai hare-hare ta sama da ta ƙasa kan ƴan Boko Haram, lamarin da ya tilasta wa ƴan ta'addan ɓoyewa a cikin dazuzzukan yankin.

A ranar 6 ga Mayu, 2014, kusan mutane 200 ne suka mutu a lokacin da ƴan tada ƙaya baya sanye da kakin soji suka kai hari a Gamboru, wani gari a jihar Borno da ke kan iyakar Najeriya da Kamaru. Maharan sun kutsa cikin garin ne a lokacin da wasu daga cikin mazauna garin ke tsaka da barci, sun ƙona gidaje tare da harbin mutanen da suka yi ƙoƙarin tserewa daga harin.[6]

Boko Haram[gyara sashe | gyara masomin]

Ƙungiyar Boko Haram ƙungiya ce ta ƴan ta'adda mai jihadi a Najeriya wacce ke neman kafa tsarin shari'a a ƙasar baki ɗaya. Mohammed Yousuf ne ya kafa ƙungiyar, kungiyar ta saba jefa bama-bamai a gine-ginen gwamnati da majami'u a hare-haren ta na ƴann bindiga. Kungiyar ta fi kai hare-hare a tsohon yankin daular Bornu, yanzu jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya. Kungiyar Boko Haram ta kaddamar da harin ta'addanci na farko a shekarar 2009, kuma tun daga nan take ta fama da rikici mai tsanani da gwamnatin Najeriya, da sojoji da kuma mazauna garin. Kungiyar Boko Haram ta yi kisan kiyashi a ƙauyuka kafin kisan kiyashin Konduga. Rikicin ya zama ruwan dare inda a ranar 14 ga watan Mayun 2013 shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kafa dokar ta ɓaci a arewacin Najeriya tare da haɗa sojoji domin fatattakar mayaƙan.[7]

Sauran ayyukan Boko Haram sun haɗa da harbe-harbe a shekarar 2013, kisan kiyashi a watan Janairun 2014, fadace-fadacen 2014 da 2015, da kuma harin ƙuna baƙin wake a 2018 da 2019.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 "Statement on recent murders and abductions in Borno State, Nigeria". United States Diplomatic Mission to Nigeria. February 14, 2014. Archived from the original on March 2, 2014. Retrieved February 26, 2014.
  2. 2.0 2.1 "Konduga Attack: Death Toll Rises to 62, as Military Bombards Possible Boko Haram Hideouts, Articles - THISDAY LIVE". Archived from the original on 2014-03-03.
  3. Cook, David (2018-07-01), Kassim, Abdulbasit; Nwankpa, Michael (eds.), "BBC Hausa Service Interview with Muhammad Yusuf", The Boko Haram Reader, Oxford University Press, pp. 71–76, doi:10.1093/oso/9780190908300.003.0010, ISBN 978-0-19-090830-0
  4. 4.0 4.1 "Boko Haram Islamists Massacre Christian Villagers in Borno State, Nigeria".
  5. "BBC - Homepage". www.bbc.com. Retrieved 2020-05-16.
  6. "Over 200 killed in Boko Haram Led Attack in Nigerian Town". IANS. news.biharprabha.com. Retrieved 7 May 2014.
  7. Greg Botelho, CNN (14 May 2013). "Nigerian president declares emergency in 3 states during 'rebellion' - CNN.com". CNN.