Kofa:Addini

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Masallacin Musulmai masu addinin musulunci
Bukukuwan addinin kirista

Addinai.

Addinai na nufin tsari mai kyau dan inganta rayuwar 'yan Adam ta hanyar tsara musu yanda zasu rayu a sigar ruhinsu da kuma gangar jikinsu, ana sanya musu tsare-tsare da kuma dokokin da zasu bi,domin bin hanyar da zai sa su samu salama a ruhinsu da gangar jikinsu a duniya da lahira. Rashin bin hanyar zai iya haifar musu da koma baya da cikas a rayuwarsu bayan mutuwarsu. Sannan su zamo masu bauta ga abinda suke bautamawa.Suna samar ma kansu wuraren bauta.Dukkan addinai na duniya an gina sune akan aikata aikin kwarai.Kada kayi cuta, kada ka zalunce wani,kada ka aikata aikin da zai bata wa tsarin tinanin dan adam ko aikin shi. Sai dai wasu tsarin addininsu yana sabama wani addini harma ya cutar dashi.Wanda hakan na kawo fada da fitana.Akwai lissafin addinai a Duniya sama da dubu goma 10,000.kashi 90% na Mutanen Duniya suna da Addini.Sannan kashi 84% na yawa mutanen duniya sunayin addini ne a daya daga cikicin addinai guda biyar ( 5) manya na Duniya sune kamar haka:-

Addinai suna da fannonin ilimi daban-daban a cikinsu tahanyar samar da da’a da Akidu]].Suna samar da bayanai akan yanda Addininsu yake gudana.Kuma suna kira zuwa ga a shigo Addininsu.

Abin-bauta[gyara sashe | Gyara masomin]

A kowanne Addini akwai abinda suke bautamawa kamar haka:-

Christianity Kiristanci[gyara sashe | Gyara masomin]

coci wajen bautar kiristoti

Alloli uku a jinsi daya(wato trinity)

Islam Musulunci[gyara sashe | Gyara masomin]

masallacin abuja kenan daya daga cikin wajen bautar Allah da musulmai keyi

Ubangiji daya

Raba-raben Addinan Muslulunci[gyara sashe | Gyara masomin]

Addinin musulunci ya kasu zuwa ga uku,kowanne Akidar daban, salan bautarsu daban, da hukunce-hukunce dadai sauransu, sune kamar haka, akwai

  1. Sunni (Yan sunnah) misalinsu Ahlussunna da Darika
  2. Shi'ite (Yan shi'a) misalinsu Fatimiyyah da imamiyyah sha-biyu
  3. Ahmadiyyah.
  4. salafiyya. da dai sauransu

Hinduism Addinin hindu[gyara sashe | Gyara masomin]

Alloli da yawa.


Buddhism Addinin buda[gyara sashe | Gyara masomin]

Ubangiji dayafolk religion Addinin gargajiya[gyara sashe | Gyara masomin]

Jigo ko kuma Jagora[gyara sashe | Gyara masomin]

A kowanne Addini ana samun jigo wanda ya kawo Addinin kamar haka:-

Ma’anar Addini[gyara sashe | Gyara masomin]

See also: Duba and Tarihin Addinai

Addini na nufin mika wiya ga abunda akayi Imani adashi a matsayin abin bauta,cikakkiyar bin tsari da kuma dokar da abin bautan ya gindaya (Abin-bauta).Sannan da’a ga wakilan addinin, Sanin ya kamata da kuma sadaukarwa.