Jump to content

Mariam Yalwaji Katagum

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mariam Yalwaji Katagum
Minister of State for Industry, Trade and Investment (en) Fassara

21 ga Augusta, 2019 - 2023
Aisha Abubakar
Rayuwa
Haihuwa Azare (en) Fassara, 1954 (69/70 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello Bachelor of Arts (en) Fassara : Turanci
Jami'ar jahar Lagos Master of Science (en) Fassara
Jami'ar Kwaleji ta Landon
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Mariam Yalwaji Katagum (An haife ta ranar 18 ga watan Nuwamba, shekara ta 1954) a Azare, jihar Bauchi[1] ta kasance Jakadiyar Najeriya a UNESCO[2] [3]kuma itace sakatariya ta dindindin, kuma itace Ministan masana'antu, cinikayya da zuba jari daga jihar Bauchi a Najeriya.[4][5]

A shekara ta 1976, Mariam Y. Katagum ta samu digiri na farko a fannin Turanci (BA. English) da kuma takardar shaidar kammala karatun digiri a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.[2] A shekara ta 1985, ta samu digiri a fannin Gudanar da Tsare-tsare a Jami’ar Legas. A cikin shekara ta alif 1999, Mariam Katagum ta sami Takaddar Shaida a (Social Development Policy, Planning and Practice) a Kwalejin Jami'ar, London. A wannan shekarar ne aka ba ta shaidar abota da UNESCO.[6]

Mariam ta fara aikin ta ne da bautan kasa (NYSC), a hukumar ruwa na jihar Jos.[1] A shekara ta alif 1977-1981, Mariam ta kasance Babban ma'aikaciyar Ilimi a Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Azare. Daga baya ta yi aiki a "Federal Scholarship Board," jihar Legas (1981-1984).

Bayan shekaru goma sha biyar da suka wuce aka tura ta zuwa hukumar Nigerian National Commission na UNESCO (1985-2000).[1] A tsakanin shekarun 2000-2001, Mariam ta kasance Darakta a kan Ayyuka na Musamman a Hukumar Ilimin Firamare ta Kasa (National Primary Education Commission) da ke Abuja.[1] Tun daga shekara ta 2001, Mariam tayi aiki a matsayin Babban Sakatariya na Hukumar Kula da Kasa ta Najeriya (wato, Nigerian National Commission) ta UNESCO.[6] A shekara ta 2004 ne, Mariam tayi jawabinta na karshe a taron UNU -UNESCO akan yake-yake a karni na 21 a Paris. Farawa daga 2006 Mariam ta koma kula da Ma'aikatar Ilimi ta Tarayya ta kasa da kasashen waje. A watan Yuni, shekara ta 2009, Katagum ta zama Ambasada, Wakiliya ta Dindindin na Nijeriya a UNESCO.[6]

Ta yi aiki a wasu kwamitocin kasa da na kasa da kasa da kuma bangarorin da suka hada da Kwamitin Amintattu na Asusun Tarihin Duniya na Afirka (2009-2011), Rukunin Afirka ta Yamma a UNESCO (2009-2012), E-9 Group a UNESCO (2010) -2012), da Kwamitin Babban Ofishin UNESCO (2011-2013), Hukumar PX ta Hukumar Zartarwa (2013) da sauransu.[6]

A shekara ta 2017, Katagum ta halarci taron "Gala Night" na Makon Afirka, a shekara ta 2017 wanda Kungiyar Afirka na UNESCO suka shirya a hedikwatan ta da ke Paris.[7]

A watan Yuli, shekara ta 2019, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zabi Katagum a matsayin karamar Ministan Masana'antu, Kasuwanci da Zuba jari na jihar Bauchi, Najeriya. [8]A matsayinta na Karamar Ministar Masana'antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Katagum ta karfafa a wajen kirkiro salon 'yancin kasuwanci na African Continental Free Trade Area (AfCFTA) mai matukar muhimmanci wajen cimma nasarorin da Najeriya za ta ci gajiyar su.[5]

  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 "EduCeleb (2019-07-24). "The profile of minister designate Mariam Katagum". EduCeleb. Retrieved 2019-11-03.
  2. 2.0 2.1 ""Minister solicits UNESCO's support for Nigerian women". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. 2019-09-17. Retrieved 2022-03-24". Archived from the original on 2020-11-16. Retrieved 2020-11-14.
  3. "Meet di women wey make Buhari list". BBC News Pidgin. Retrieved 2022-03-24.
  4. "President Buhari Swears In Ministers, Assign Portfolios (Full List)". Nigerian Voice. Retrieved 2022-03-24.
  5. 5.0 5.1 "FG committed to achieving seamless implementation of AfCFTA – Katagum". Daily Times Nigeria. 2019-09-28. Retrieved 2019-11-03.
  6. 6.0 6.1 6.2 6.3 "Chairperson | United Nations Educational, Scientific and Cultural Organization". www.unesco.org. Retrieved 2022-03-24.
  7. "Ambassador Mariam Katagum Commends Ogun State Cultural Troupe". www.nico.gov.ng. Retrieved 2019-11-03.
  8. "AfricaNews (2019-08-21). "Nigeria's new cabinet inaugurated, president remains Petroleum minister". Africanews. Retrieved 2019-11-03.

Hanyoyin haɗin waje

[gyara sashe | gyara masomin]