Moses Fasanya
Moses Fasanya | |||||
---|---|---|---|---|---|
ga Augusta, 1998 - Mayu 1999 ← Anthony Onyearugbulem (en) - Adebayo Adefarati (en) →
22 ga Augusta, 1996 - ga Augusta, 1998 ← Temi Ejoor - Anthony Obi → | |||||
Rayuwa | |||||
Cikakken suna | Moses Fasanya | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Ƙabila | Yaren Yarbawa | ||||
Harshen uwa | Yarbanci | ||||
Karatu | |||||
Harsuna |
Turanci Yarbanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa |
Moses Fasanya wani Kanal ne ɗan Najeriya ne daga garin Ibadan na jihar Oyo wanda ya taɓa riƙe muƙamin shugaban mulkin soja na jihar Abia (Agusta 1996 – Agusta 1998) a lokacin mulkin soja na Janar Sani Abacha.[1] Daga nan ya zama shugaban mulkin soja na jihar Ondo a cikin watan Agustan 1998, inda ya miƙa mulki ga gwamna Adebayo Adefarati a cikin watan Mayun 1999.[2]
Ya jawo wahalhalu a jihar Ondo ta hanyar yin katsalandan wajen gudanar da zaɓen shugaban gargajiya na Owo, lamarin da ya janyo hargitsi da kashe-kashe da ɓarnata dukiya.[3] A cikin watan Oktoban shekarar 1998, an kashe ɗaruruwan mutane a rikicin da ya ɓarke tsakanin ƴan ƙabilar Ijaw na yankin Akpata da ƴan ƙabilar Ilaje da ke neman aiki a wani sabon rijiyoyin mai da aka gano. Fasanya ya sha wahala wajen samun yarjejeniya da shugabannin Ijaw kan hanyoyin daidaita lamarin.[4] Ya tura sojoji da ƴan sanda yankin a wani yunƙuri na maido da zaman lafiya.[5] A cikin watan Fabrairun 1999, mataimakan Fasanya sun zalunce su tare da tsare ƴan jarida goma sha biyar da ke bayar da rahotannin taron shugabannin Jihar Odu’a Investment Company a Akure.[6]
A cikin watan Maris ɗin 2009, wata tankar mai ta kama wuta a Obadore kusa da Jami'ar Jihar Legas. Tsohon gwamna Fasanya ya yi asarar kayayyakin bugu da sauran kayayyaki na sama da Naira miliyan 3 da ya ajiye a shaguna goma na garin da gobarar ta tashi.[7]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ http://abiaexecutiveinformant.com/storylinks.html[permanent dead link]
- ↑ https://www.worldstatesmen.org/Nigeria_federal_states.htm
- ↑ https://web.archive.org/web/20050912023350/http://www.thisdayonline.com/archive/2001/04/20/20010420pol05.html
- ↑ https://www.nytimes.com/1998/10/05/world/ethnic-clashes-kill-hundreds-of-nigerians.html
- ↑ https://www.unhcr.org/refworld/country,,HRW,,NGA,,3ae6a82e0,0.html
- ↑ "Kwafin ajiya" (PDF). Archived from the original (PDF) on 2021-05-13. Retrieved 2023-03-28.
- ↑ http://thepmnews.com/2009/03/16/after-the-fire-ex-governor-traders-count-losses?version=print